Atiku Ya Dauki Zafi da Ya Ga Rahoton Yadda Aka Raba Tallafin N25,000 ga Yan Najeriya

Atiku Ya Dauki Zafi da Ya Ga Rahoton Yadda Aka Raba Tallafin N25,000 ga Yan Najeriya

  • Atiku Abubakar ya yi martani kan rahoton shirin tallafin radadi da ofishin Audita Janar na tarayya ya fitar da yadda aka raba wa talakawa kudi
  • Tsohon mataimakin shugaban kasa ya ce rahoton ya nuna akwai shakku kan yadda aka raba biliyoyin Naira ga yan Najeriya masu rauni
  • Ya sha alwashin kafa kwamitin kwararru da za su binciki yadda shirin tallafin ya gudana a karkashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya dauko tallafin shirin tallafin rage radadi na N25,000 da gwamnatin tarayya ta ce ta rabawa talakawa.

Atiku yi alkawarin kafa tawagar kwararru a fannin kudi, bincike, fasaha da lissafin kudaden gwamnati domin nazari kan Naira biliyan 33.75 da gwamnatin Bola Tinubu ta ce ta rabawa talakawa miliyan 3.29 karkashin shirin tallafin rage radadi.

Kara karanta wannan

2027: An samu gwamna na farko da ya goyi bayan tsarin Atiku na rage tsadar fetur a Najeriya

Atiku Abubakar.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Atiku ya bayyana hakan ne ranar Asabar ta bakin babban mataimakinsa na musamman kan hulda da jama'a, Phrank Shaibu, kamar yadda Tribune Nigeria ta rahoto.

Atiku ya yi martani kan shirin tallafi

Dan takarar shugaban kasa na ADC ya ce alkaluman sun haifar da muhimman tambayoyi kan yadda shirin ya kai ga wadanda aka tanada watau talakawa da ke fama da tsadar rayuwa.

Bisa ga alkaluman, idan aka raba Naira biliyan 33.75 tsakanin gidaje miliyan 3.29, kowane gida zai samu kusan Naira 10,258.

Atiku ya ce a daidai lokacin da farashin sufuri, wutar lantarki da abinci ke kara tsada, ya kamata 'yan Najeriya su samu cikakken bayani kan yadda aka raba tallafin da kuma ko ya kai ga wadanda aka yi niyya.

Atiku hango lam'a a shirin tallafi

Ya ce:

“Wannan ba batun lissafin kudi kawai ba ne. Idan ba za a iya yin cikakken bayani kan kudaden da aka ware domin tallafa wa 'yan Najeriya, to hakan zai raunana amincewar jama'a da shirin.”

Kara karanta wannan

Atiku ya nuna yadda kalaman IPMAN suka 'kunyata' Tinubu kan dawo da tallafin fetur a Najeriya

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yaba wa Babban Audita Janar mai binciken kudaden gwamnatin tarayya, Shaakaa Chira, kan sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora masa.

Daily Trust ta ce rahoton ofishin Audita Janar ya nuna cewa babu wata shaida da ke nuna Naira biliyan 33.75 da aka ce an rabawa marasa karfi sun kai ga wadanda ya kamata.

Atiku ya kuma ce akwai sabani a bayanan da gwamnati ta fitar game da shirin, inda ya yi nuni da ikirarin cewa an raba sama da Naira biliyan 600 ga gidaje sama da miliyan 10, bayan da a baya aka ambaci gidaje miliyan 15.

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wurin taron kasa da kasa Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Matakin da Atiku ya shirya dauka

Domin tabbatar da gaskiya, Atiku ya ce zai kafa tawagar kwararru masu zaman kansu domin nazarin rahoton da Audita Janar ya fitar kan biyan tallafin.

Ya ce:

“Za mu binciki bayanan wadanda suka amfana, hanyoyin biyan kudaden, bayanan daidaita lissafi da tambayoyin binciken kudi, gwargwadon bayanan da jama'a da hukumomi suka samar. Bayan kammala binciken, za mu bayyana sakamakon ga 'yan Najeriya."

Atiku ya nuna damuwa kan matasa

Kara karanta wannan

2027: Shirin Atiku na dawo da tallafin man fetur ya samu gagarumar goyon baya

A wani labarin, kun ji cewa Atiku Abubakar ya nuna damuwa kan abin da ya bayyana a matsayin ƙaruwa da ake samu na matasan Najeriya da ke sayar da ƙodojinsu domin samun tsira.

Atiku ya danganta wannan yanayi da ƙarin tsadar rayuwa da ya ce manufofin tattalin arzikin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu suka haifar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262