Farashin Fetur Zai Iya Kara Sama da Gangar Mai Ta Tashi saboda Yaki a Iran

Farashin Fetur Zai Iya Kara Sama da Gangar Mai Ta Tashi saboda Yaki a Iran

  • Gangar kowace danyen mai na Brent ta kara kudi kadan a cikin farkon makon nan a kasuwar duniya
  • Man ya tashi da akalla 4.6%, hakan yana nufin kowace ganga na neman kai $95 saboda rikici da ake ta yi
  • Muddin danyen mai ya kara kudi, matatar Dangote za ta canza farashi, haka zalika masu kawo kaya daga ketare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

America - Farashin gangar mai ta tashi da fiye da 2% a farkon makon nan a sakamakon rikicin Amurka da kasar Iran da ake ta yi.

Wannan canjin farashi da aka samu a kan kudin kowace ganga zai iya canza lissafa, har ya kawo bambanci a kasuwannin duniya.

Gidan mai
Gidan mai da ake saida fetur da dizal a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Farashin gangar mai a kasuwar duniya

Reuters ta rahoto cewa mai yana kara kudi a sanadiyyar kai wa juna hari da aka koma yi tsakanin sojojin Amurka da na kasar Iran.

Kara karanta wannan

Kalaman Putin sun faranta wa kasar Iran rai yayin da take yaki da Amurka

Man Brent ya tashi da $4.16 a kasuwa a ranar Litinin. Hakan yana nufin gangar danyen ma ya kara tsada da kashi 4.6 cikin 100.

Yayin da gangar Brent ya kai $94.65, shi kuma danyen man Amurka na US West Texas ya karu da $4.46, ya koma $90.22 a kasuwa.

Kafin nan sai da aka sai da man Brent a $91.52, wannan shi ne mafi darajar da gangar ta yi tun karshen Agustan 2025 in ji Oilprice.com.

Yakin Amurka da Iran ya tashi kudin fetur

Gaza cin ma matsayar sulhu tsakanin mahukunta a Washington da Tehran ya jawo dakarun sojojin Amurka suka kai wa Iran hari.

Sojojin Amurka sun farmaki tsibirin Larak da ke yankin mashigar Hormuz. Harin kasar na farko a Iran a cikin kusan wata guda kenan.

A halin yanzu litar man fetur ta zarce N1300 bayan karin da matatar Dangote ta yi a makon nan.

Kara karanta wannan

Jita jitar Opay da shahararrun labaran bogi da suka rika yawo makon jiya a Najeriya

Mashigar Hormuz da farashin mai a duniya

Kokarin dawo da yakin danye zai jawo dar-dar a Hormuz, mashigar da ake wuce wa da daya bisa biyar na man da ake sha a duniya.

An zura ido domin ganin ko za a iya bude mashigar da karfin bindiga, ko kuwa dole Amurka da Iran za su koma kan teburin yin sasanci.

Saboda wannan rigima, alkaluma sun nuna jirage kusan biyar kurum ake gani suna wuce wa ta Hormuz, lamarin da ya dagula kasuwa.

Jirgin mai
Wani jirgin mai da ya dauko kaya yana wucewa ta Landan Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Amurka na ikirarin yi wa kasuwar Iran lahani

Rahoton ya ce Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi ikirarin yi wa Iran barna, sun kona yankin tsibirin Kharg da ake da makamashi.

Bayanai sun ce babu tabbacin wannan magana kuma har Iran International ta ce Trump ya dogara ne da wani kirkirarren bidiyon bogi.

Idan farashi suka cigaba da tafiya haka, babu mamaki a ga sauyi a gidajen mai saboda canjin da za a samu daga matatu ko ‘yan kasuwa.

Kara karanta wannan

Ba sauki: Matatar Dangote ta sake kara farashin man fetur

Dangote ya yi karin kufin man fetur

An rahoto matatar man fetur ta Dangote ta sake kara farashin fetur da N65, wanda ya sa farashin lita daya ya koma N1,265 daga N1,200.

Wannan shi ne karo na uku da matatar ke kara farashin fetur a tsawon kwanaki takwas, inda aka samu jimillar karin N100 wato 8.6%.

Masana da 'yan kasuwa na hasashen cewa wannan karin zai jawo tashin farashin fetur a gidajen mai da kuma kudin sufuri a fadin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng