‘Ka Hakura da Neman Takara a 2027’: Atiku Ya Sake Shawartar Shugaba Tinubu

‘Ka Hakura da Neman Takara a 2027’: Atiku Ya Sake Shawartar Shugaba Tinubu

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar ya sake ba Shugaba Bola Tinubu shawara game da zaben 2027
  • Atiku ya ce rikicin shugabancin Hukumar BCDA da makamancinsa a NIPOST sun nuna gazawar gwamnati wajen aiwatar da doka
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce ya kamata Tinubu ya mayar da hankali kan magance matsalolin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ba shugaban kasa, Bola Tinubu shawara kan tsayawa takara a 2027.

Atiku ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya janye daga takarar shugaban ƙasa ta shekarar 2027 da ke tafe.

Atiku ya shawarci Tinubu kan tsayawa takara a 2027
Atiku Abubakar da Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Getty Images

'Kura-kuran da gwamnatin Tinubu ta tafka'

Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC a zaɓen 2027, ya ce gwamnatin Tinubu ta yi kura-kurai masu yawa wajen tafiyar da mulki, cewar The Sun.

Kara karanta wannan

Bauchi: Tsohon kwamishina ya zama mataimakin dan takarar gwamna a APC

Ya bayyana cewa rikicin shugabanci da ya kunno kai a Hukumar Raya Ƙauyukan Kan Iyaka (BCDA) ya nuna cewa ana saba umarnin gwamnatin tarayya ke bayarwa.

A cewarsa, duk da shugaban ƙasa ya naɗa sabon Babban Sakatare na hukumar, tsohon mai riƙe da muƙamin bai bar ofis ba kuma har yanzu yana gudanar da ayyukansa.

Atiku ya ce wannan ba shi ne karo na farko ba, domin irin wannan ruɗani ya taɓa faruwa a Hukumar NIPOST, lamarin da ya jefa jama'a cikin ruɗani.

Ya tambayi yadda za a ci gaba da tallata Najeriya a matsayin ƙasa mai jan hankalin masu zuba jari alhali gwamnati ba ta iya fayyace wanda ke jagorantar wata hukuma.

Har ila yau, ya ce dokar da ta kafa BCDA ta tanadi muƙamin Babban Sakatare a matsayin shugaban gudanarwa, ba Darakta Janar ba kamar yadda aka sanar.

A cewarsa, wannan kuskure ya nuna cewa ba a yi cikakken nazarin doka kafin sanar da naɗin ba, abin da ke nuna gazawar tsarin gwamnati.

Atiku ya taso Tinubu a gaba kan takara
Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: UGC

Zargin da Atiku ya yi wa gwamnatin Tinubu

Atiku ya ƙara da cewa yawan rikice-rikicen da ake samu a hukumomin gwamnati na nuna matsalolin rashin daidaito, rashin tuntuba da kuma gazawar bin ƙa'idojin doka.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Mataimakin shugaban APC da wasu manyan ƙusoshi sun fice daga jam'iyyar

Ya kuma yi nuni da sauya manufofi akai-akai da kuma kashe kuɗaɗen gwamnati a ayyukan da ba su dace da wasu hukumomi ba, lamarin da ya rage amincewar jama'a, cewar Vanguard.

A ƙarshe, Atiku ya buƙaci Fadar Shugaban Ƙasa ta fayyace matsayin shugabancin BCDA tare da tabbatar da cewa duk wasu naɗe-naɗe na gaba sun bi tanadin doka.

Ya kuma shawarci Shugaba Tinubu ya dakatar da shirinsa na sake neman zaɓe a 2027, ya mayar da hankali wajen magance matsalolin tattalin arziƙi, tsaro da sauran ƙalubalen da ke fuskantar Najeriya.

Gbajabiamila: Atiku ya bukaci kyakkyawan bincike

An ji cewa Atiku Abubakar ya bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa kan sabbin zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake yi wa Femi Gbajabiamila.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce duk jami'an gwamnati dole ne su fuskanci bincike ba tare da la'akari da mukaminsu ba.

Femi Gbajabiamila dai bai fito fili ya mayar da martani kan zarge-zargen ba, kuma ba a tabbatar da ikirarin ta hanyar bincike mai zaman kansa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.