Zaben 2027: ADC Ta Fitar da Jerin Sunayen 'Yan Takararta na Gwamna a Jihohi 28
- ADC ta fitar da sunayen ’yan takarar gwamna da mataimakansu a jihohi 28 domin wakiltar jam’iyyar a zaɓen 2027
- Daga cikin fitattun ’yan takarar akwai Halliru Dauda Jika a Bauchi, Herman Hembe a Benue da Zakari Mohammed a Kwara
- A Kaduna, Isa Mohammed Ashiru zai tsaya takarar gwamna, yayin da Gbadebo Rhodes-Vivour zai fafata a Lagos ƙarƙashin tutar ADC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta fitar da sunayen ’yan takararta na gwamna da mataimakansu da za su fafata a zaɓen 2027.
Mai magana da yawun jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, 4 ga watan Satumban 2026.

Source: Facebook
Bolaji Abdullahi ya fitar da sanarwar ne a shafinsa na X dauke da sunayen 'yan takarar gwamnan na ADC.
Ya ce jerin sunayen ya ƙunshi ’yan takarar gwamna da za su ɗauki tutar ADC a jihohi 28 na Najeriya.
Bolaji ya ce mutanen da aka zaɓa sun haɗa da maza da mata da za su wakilci manufofin jam’iyyar da kuma ƙudurinta na samar wa ’yan Najeriya shugabanci nagari da kuma wata sahihiyar mafita ta siyasa.
Fitattun ’yan takarar ADC
Daga cikin fitattun ’yan takarar da jam’iyyar ta bayyana akwai Sanata Halliru Dauda Jika a jihar Bauchi.
Haka kuma, tsohon ɗan Majalisar Wakilai, Herman Iorwase Hembe, zai tsaya takarar gwamna a Benue, yayin da tsohon ɗan Majalisar Wakilai Zakari Mohammed zai fafata a jihar Kwara.
A Plateau kuma, tsohon jami’in Sojojin Najeriya mai muƙamin Birgediya Janar, John Sunday Sura, ne zai tsaya takarar gwamna ƙarƙashin tutar ADC.
Jam’iyyar ta kuma gabatar da ’yan takara a Adamawa, Akwa Ibom, Borno, Cross River, Delta, Ebonyi, Enugu, Gombe, Jigawa, Kano, Katsina, Kebbi, Nasarawa, Niger, Ogun, Oyo, Rivers, Sokoto, Taraba, Yobe da Zamfara.
A jihar Lagos, Gbadebo Rhodes-Vivour zai tsaya takarar gwamna, yayin da Gbadamosi Babatunde Olalere zai kasance mataimakinsa.
A Kaduna kuwa, Isa Mohammed Ashiru zai yi takarar gwamna, tare da Kantiok Irmiya Ishaku a matsayin mataimakinsa, yayin da Ahmad Babba Kaita zai yi takara a Katsina.
Jerin ’yan takarar ADC da mataimakansu
1. Abia
Gwamna: Kalu Kalu Agu; Mataimaki: Alozie Ogadinma Darlington
2. Adamawa
Gwamna: Modibbo Hammantukur Ribadu; Mataimaki: Aguwa Kevin Iliya
3. Akwa Ibom
Gwamna: Akpanudoedehe John James; Mataimaki: Nsien Mkpombuk Tommy
4. Bauchi
Gwamna: Halliru Dauda Jika; Mataimaki: Sama’ila Mohammed Kabir
5. Benue
Gwamna: Herman Iorwase Hembe; Mataimaki: Abba John Abba
6. Borno
Gwamna: Babagana Buhari; Mataimaki: Mamman Dauda
7. Cross River
Gwamna: Nkoyo Toyo; Mataimaki: Okwocho Andrew Adagbor
8. Delta
Gwamna: Great Ogboru; Mataimaki: Afiari Gloria
9. Ebonyi
Gwamna: Ukpai Mba Udeh; Mataimaki: Onwe Daniel Ede
10. Enugu
Gwamna: Ocho Obodo Eze Chukwuma; Mataimaki: Eze Arinze Christopher
11. Gombe
Gwamna: Bala Bello; Mataimaki: Bala Sani Isa
12. Jigawa
Gwamna: Sabo Mohammed Nakudu; Mataimaki: Musa Ya’u Balarabe
13. Kaduna
Gwamna: Isa Mohammed Ashiru; Mataimaki: Kantiok Irmiya Ishaku
14. Kano
Gwamna: Ibrahim Ali Amin; Mataimaki: Shehu Abdulkadir Bari
15. Katsina
Gwamna: Ahmad Babba Kaita; Mataimaki: Aminu Yar’Adua Ahmed
16. Kebbi
Gwamna: Abubakar Malami; Mataimaki: Zagi Musa Mohammed
17. Kwara
Gwamna: Zakari Mohammed; Mataimaki: Olawuyi Julius Olayide
18. Legas
Gwamna: Gbadebo Rhodes-Vivour; Mataimaki: Gbadamosi Babatunde Olalere
19. Nasarawa
Gwamna: Nuhu Angbazo; Mataimaki: Ahmed Yusuf
20. Niger
Gwamna: Mohammed Kpautagi; Mataimaki: Musa Mamman
21. Ogun
Gwamna: Biodun Collins Ogundipe; Mataimaki: Muraina Oluwaranti Oluyemi
22. Oyo
Gwamna: Taofeek Adegboyega Adegoke Adegóke; Mataimaki: Wahab Adeniyi
23. Plateau
Gwamna: John Sunday Sura; Mataimaki: Pwa Jok-Kele Chundung Bitrus
24. Rivers
Gwamna: Gabriel Pidomson; Mataimaki: Okungba David Amapakaye
25. Sokoto
Gwamna: Manir Mohammad Daniya; Mataimaki: Isah Bello Ambarura
26. Taraba
Gwamna: Abubakar Umar Tutare; Mataimaki: Kwetishe Haruna Kwenyan
27. Yobe
Gwamna: Kassim G. Gaidam; Mataimaki: Kori Lawan Mohammed
28. Zamfara
Gwamna: Shinkafi Bilyaminu Yusuf; Mataimaki: Muhammad Abdulmuddalib Auwal

Source: Facebook
Dan takarar ADC zai ba dattawa alawus
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar gwamnan jam'iyyar ADC a Oyo, Olooye Adegboyega Taofeek Adegoke, ya yi alkawura ga dattawa.
Adegoke ya yi alkawarin biyan mazauna jihar ’yan shekara 75 zuwa sama alawus kowane wata.
Asali: Legit.ng



