'Yan Boko Haram Sun Yi Wa Motocin Dan Takarar Gwamnan APC Kwanton Bauna a Borno

'Yan Boko Haram Sun Yi Wa Motocin Dan Takarar Gwamnan APC Kwanton Bauna a Borno

  • Ayarin motocin ɗan takarar gwamnan Borno na APC, Mustapha Gubio, ya taka bam da aka dasa a hanyar Gubio-Kareto-Damasak
  • Fashewar ta lalata motar sulke ta ’yan sanda da ke jagorantar ayarin, yayin da jami’an tsaro suka dakile yunƙurin ’yan ta’addan na kai hari
  • Hanyar Gubio-Kareto-Damasak na daga cikin wuraren da ke da matuƙar haɗari saboda yawan hare-haren Boko Haram da barazanar IED

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Ayarin motocin ɗan takarar gwamnan jihar Borno na jam’iyyar APC, Injiniya Mustapha Gubio, ya faɗa cikin kwanton baunar da ake zargin ’yan Boko Haram ne suka shirya.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis, 3 ga watan Satumban 2026 lokacin da Gubio da tawagarsa ke dawowa Maiduguri bayan ziyarar godiya da suka kai garin Damasak.

Boko Haram sun kai hari a Borno
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Motar ’yan sanda ta taka bam

Kara karanta wannan

Kamfanin Opay ya nemi agajin DSS, ƴan sanda kan jita jitar zai gudu a Najeriya

Wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ’yan ta’addan sun dasa nakiyoyi a kan babbar hanyar Gubio-Kareto-Damasak, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Jami’in ya ce motar sulke ta ’yan sanda da ke jagorantar ayarin ta taka ɗaya daga cikin nakiyoyin, lamarin da ya haddasa fashewa mai ƙarfi.

“Mun shiga Damasak lafiya kuma muka shafe kusan mintuna 40 a wurin. A hanyar dawowa, ’yan ta’addan sun dasa nakiyoyi a kan hanya, motar sulke da ke jagorantar ayarin ta taka ɗaya daga cikinsu kuma ta fashe.” In ji shi.

Jami’an tsaro sun dakile harin

Bayan fashewar bam ɗin, ’yan ta’addan sun yi yunƙurin kai wa ayarin motocin harin kwanton bauna.

Sai dai haɗin gwiwar jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji, ’yan sanda da ’yan kungiyar Civilian Joint Task Force (CJTF) sun mayar da martani cikin gaggawa.

Jami’an sun shiga musayar wuta da maharan, lamarin da ya taimaka wajen dakile harin tare da kare sauran motocin ayarin.

Ba a samu asarar rayuka ba

Jami’an tsaron sun yi nasarar fatattakar maharan tare da hana su sake kai wani hari ko jawo asarar rayuka a cikin babban ayarin.

Kara karanta wannan

Yadda wasu ƴan Najeriya ke tsallake garuruwansu zuwa Benin saboda hare hare

Sai dai motar sulke ta ’yan sanda da ta taka nakiyar ta samu mummunar lalacewa sakamakon fashewar.

Ba a samu rahoton cewa Mustapha Gubio ko wani babban jami’in da ke cikin ayarin ya samu rauni ba.

Hanyar na cikin wuraren da ke da haɗari

Hanyar Gubio-Kareto-Damasak ta shahara da kasancewa ɗaya daga cikin hanyoyin da ke da matuƙar haɗari a jihar Borno.

Ana amfani da hanyar wajen zirga-zirgar ’yan Boko Haram daga sansanoninsu da ke yankin Tafkin Chadi zuwa Alagarno, dajin Sambisa da wasu sassan jihar Yobe.

A lokacin da ake ƙoƙarin samun ƙarin bayani, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Borno, DSP Nahum Kenneth Daso, bai amsa kiran waya ba, kuma bai mayar da martani ga saƙonnin da aka tura masa ba.

Saboda haka, ba a samu bayanin hukuma daga rundunar ’yan sanda kan harin na ranar Alhamis ba.

An farmaki tawagar Mustapha Gubio
Gwamna Babagana Umara Zulum tare da Mustapha Gubio Hoto: @GovZulum
Source: Facebook

Sojoji sun fafata da 'yan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji su yi arangama da 'yan ta'adda bayan da suka kai hari a jihar Borno.

‘Yan ta’addan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 10:50 na dare kan sojojin Bataliya ta 101 Special Forces da aka jibge a Kukawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng