APC Ta Fito da Sabon Gargadi game da Zaben Atiku a 2027
- Jam’iyyar APC ta yi kira ga ‘yan Najeriya da kada su zaɓi tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin shugaban ƙasa a zaɓen 2027
- Jam’iyyar ta zargi Atiku da kasancewa cikin wasu tsofaffin badakalar cin hanci da rashawa, tana mai cewa bai kamata a sake ba shi babban matsayi ba
- Wannan na zuwa ne yayin da wasu rahotanni ke cewa wasu gwamnonin APC da ba su gamsu da wasu harkokin cikin jam’iyyar ba na tattaunawa da Atiku ta bayan fage
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugabancin jam’iyyar APC ya gargadi ‘yan Najeriya kan zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, a zaɓen 2027.
Kwamitin Aiki na Ƙasa na APC ya yi wannan kira ne cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na jam’iyyar, Felix Morka, ya fitar.

Kara karanta wannan
Kungiyar kare hakkin Musulmi a Najeriya ta yi magana kan kama Atiku gabanin zaben 2027

Source: Facebook
The Sun ta wallafa cewa jam’iyyar ta yi zargin cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar yana da tarihin da ya shafi wasu badakalar cin hanci da rashawa da kuma fifita wasu mutane a harkokin gwamnati.
APC ta zargi Atiku da badakala
APC ta ce rahotannin da ake yaɗawa a kafafen yaɗa labarai da sauran wurare sun haɗa da zarge-zargen da suka shafi cin hanci da rashawa a cikin gida da ƙasashen waje.
Jam’iyyar ta lissafa batutuwan da suka shafi aikin samar da wutar lantarki ta Mambilla, badakalar Siemens, shari’ar William Jefferson, rikicin kuɗaɗen PTDF da kuma binciken Majalisar Dattawan Amurka kan wasu mu’amalolin kuɗi.
APC ta ce waɗannan batutuwa sun bayyana a wasu bayanan hukuma, shari’o’i, binciken gwamnati da rahotannin majalisun dokoki na cikin gida da ƙasashen waje.
Magana kan batun Mambilla
Punch ta wallafa cewa APC ta ce sabon rikicin da ya shafi aikin samar da wutar lantarki na Mambilla ya ƙara tayar da hankalinta.
Jam’iyyar ta yi nuni da wani bincike da Kotun Sasantawa ta Ƙungiyar Kasuwanci ta Duniya a Paris ta gudanar kan biyan dala 500,000 da aka yi a watan Janairun 2003.
A cewar APC, an biya kuɗin ne daga Leno Adesanya, mai tallata Sunrise Power, ga Jennifer Douglas, wadda a lokacin matar Atiku ce, ta hannun wani kamfani da ke ƙasashen waje.

Source: Facebook
Sai dai zarge-zargen da APC ta yi wa Atiku an bayyana su ne a matsayin matsayar jam’iyyar, ba hukuncin da ya tabbatar da laifin Atiku ba.
Haduwar Atiku da 'yan APC
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu gwamnonin APC da ba su gamsu da wasu harkokin cikin jam’iyyar ba na binciken yiwuwar kulla alaka da Atiku Abubakar gabanin zaɓen 2027.
Rahotanni sun ce damuwar wasu daga cikin gwamnonin ta samo asali ne daga tasirin ƙawancen Rainbow Coalition da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ke jagoranta a siyasar 2027.
Wani mai tallata Tinubu a Arewacin Najeriya ya ce wasu gwamnonin APC da ba su gamsu da al’amura ba sun fara tattaunawa kan yiwuwar ƙawance da Atiku.
Asali: Legit.ng
