An Hada Mata Musulmai da Allah SWT kan Sake Zaben Tinubu da Shettima a 2027
- Bello Matawalle ya buƙaci mata Musulmi a faɗin Najeriya su mara wa Bola Tinubu da Kashim Shettima baya a zaɓen 2027
- Karaminin ministan na tsaro ya ce goyon bayan tikitin Musulmi-Musulmi ya samo asali ne daga kishin addini, ba don kuɗi ko siyasa ba
- Aminu Masari ya ce a kusan shekaru 40 da ya yi a siyasa, bai ga shugaban ƙasa mai kyakkyawan shiri ga Najeriya kamar Tinubu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna, Nigeria - Karamin Ministan Tsaron Najeriya, Bello Matawalle, ya buƙaci mata Musulmi a faɗin Najeriya su mara wa tikitin Musulmi-Musulmi na APC baya a zaben 2027.
Tsohon gwamnan na jihar Zamfara ya roki matan tare da hada su da Allah da su zabi Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima a zaben shekara mai zuwa.

Kara karanta wannan
"Zan iya rantsewa," Tsohon gwamna ya ce bai taba ganin shugaba kai tsari kamar Tinubu ba

Source: Facebook
Matawalle ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da ya yaɗu, wanda HM Arewa, wata kafar yaɗa labarai da ke watsa labarai da Hausa, ta wallafa a Facebook ranar Talata.
A cikin bidiyon, an ga Matawalle yana jawabi ga wasu mata a wani taron jama'a da aka ce an gudanar a Kaduna, inda tsohon kakakin Majalisar Wakilai, Aminu Masari, shi ma ya halarta.
“Wannan taron siyasa ne da ya shafi siyasar Bola Ahmed Tinubu, kuma duk wanda ke nan yana aiki ne domin ganin an tabbatar da tikitin Musulmi-Musulmi,” in ji Matawalle da Hausa.
Matawalle ya bayyana dalilinsa
Ya ce Musulmi da ya goyi bayan tikitin Musulmi-Musulmi kuma aka samu nasarar tabbatar da shi, zuciyarsa za ta kasance cikin kwanciyar hankali saboda ya san dalilin da ya sa yake yin hakan.
“Kun yi hakan ne saboda addininku da kuma neman yardar Allah, domin Allah yana umartar Musulmi su so ’yan uwansu Musulmi,” in ji shi.
Ya ce bai kamata su bari sukar da ake yi wa goyon bayansu ga tikitin ta hana su ci gaba da matsayinsu ba, domin a cewarsa, ba kuɗi ko siyasa ne suka sa suke yin hakan ba, illa imanin addininsu.
Minista ya ja hankalin mata musulmi
Ya ƙara da cewa:
“Saboda haka, kuna kan hanyar zaɓen Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima, tikitin Musulmi-Musulmi, a matsayinku na Musulmi, ’ya’yan Musulmi kuma jikokin Musulmi.
“Babu wanda zai iya cewa abin da kuke yi ba daidai ba ne, ko kuma ya ce kun yi kuskure saboda kuna bin koyarwar addininku, kawai don ƙasa Najeriya ce. Dole ku tsaya kan imaninku.”

Source: Facebook
Matawalle ya buƙaci matan su ci gaba da tsayawa kan abin da suka yi imani da shi, yana mai cewa za su iya kasancewa da kyakkyawan fata ko da Allah ya karɓi rayukansu a lokacin da suke aiki domin tabbatar da tikitin Tinubu da Shettima.
Matawalle ya yi alkawarin kuri'u miliyan 20
Kun ji cewa Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya kaddamar da kungiyar ‘Tinubu Again’, wadda ke shirin tallata shugaban kass, Bola Tinubu.
Matawalle ya yi alkawarin samar da kuri’u sama da miliyan 20 ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran ’yan takarar APC a babban zaben 2027.
Asali: Legit.ng
