Mata Ta Kalli Tawagar APC Ido da Ido, Ta Ce ko Kuri’a 1 ba Za Su Samu ba

Mata Ta Kalli Tawagar APC Ido da Ido, Ta Ce ko Kuri’a 1 ba Za Su Samu ba

  • Wata mata a Arewacin Najeriya ta yi watsi da APC da Bola Tinubu, tana cewa jam’iyyar ba za ta samu kuri’a ko damar yaƙin neman zaɓe ba
  • Matar ta bayyana hakan ne yayin da ta fuskanci tawagar APC da ke gudanar da gangamin wayar da kan jama’a
  • Lamarin ya faru ne yayin da ayyukan siyasa ke ƙara ƙamari gabanin zaɓen 2027 lokacin da korafe-korafen jama’a ya yi yawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Wata mata daga Arewacin Najeriya ta kunyata tawagar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya yayin da ae shirin zaben shekarar 2027.

Matar ta yi watsi da jam'iyyar Shugaba Bola Tinubu gabanin babban zaɓen 2027, inda ta fada wa tawagar wayar da kan jama’ar APC gaskiya.

Mata ta kunyata tawagar APC a Arewa
Shugaban APC, Nentawe Yilwatda da mambobin jam'iyyar. Hoto: Prof. Nentawe Yilwatda.
Source: Twitter

Matar ta bayyana hakan ne a wani bidiyo da ke yaɗuwa a kafafen sada zumunta wanda muka samu daga shafin Vanguard.

Kara karanta wannan

Nafiu Bala ya kawo sabon rikici a ADC kan yadda Atiku ke sukar Tinubu

Yadda mata ta fadawa tawagar APC gaskiya

Dattijuwar ta bayyana cewa jam’iyyar da ɗan takararta ba za su samu kuri’a daga al’ummarta ba.

An gano matar tana fuskantar wasu mambobin tawagar APC da ke gudanar da gangamin wayar da kan jama’a a wani taron jama’a.

A cikin bidiyon, ta bayyana cewa jam'iyyar APC ba za ta samu “ko kuri’a guda” daga yankin ba, tare da ƙara cewa ba za a ma bari jam’iyyar ta gudanar da yaƙin neman zaɓe a yankin ba.

Ta ce:

“APC ba za ta samu ko kuri’a guda ba, ballantana ta yi kamfe. Idan kuna so, ku yi abin da ya wuce kamfe, ba za mu zaɓi APC ba.”
An caccaki salon mulkin Tinubu da APC
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Yadda mulkin APC ya kai mutane wuya

Maganganun matar sun nuna irin rashin karɓuwar da tawagar jam’iyyar mai mulki ta fuskanta a yankin, yayin da kalamanta suka nuna ƙudirin kin amincewa da kasancewar jam’iyyar a yankin, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

'Yan adawa za su yi babban taro a yau domin shirin kifar da Tinubu a 2027

An yaɗa bidiyon ne a kafafen sada zumunta ranar Litinin, 31 ga Agusta, 2026, a daidai lokacin da ayyukan siyasa ke ƙara ƙamari gabanin babban zaɓen 2027, yayin da jam’iyyun siyasa ke ƙoƙarin ƙarfafa goyon bayansu a matakin ƙasa.

Kalaman matar sun kuma zo ne a daidai lokacin da ake samun yawaitar koke-koken jama’a kan matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, batutuwan da ake sa ran za su mamaye muhawarar siyasa gabanin zaɓen.

Lamarin ya jawo martani daga masu amfani da kafafen sada zumunta, inda wasu ’yan Najeriya suka nuna goyon bayansu gare ta, yayin da wasu suka ce ya kamata masu zaɓe su tantance jam’iyyu da ’yan takara bisa ayyukansu da kuma hanyoyin da suke ba da shawarar magance matsalolin ƙasar.

Kwamishina ya yi barazana ga masu sukar APC

An ji cewa Kwamishinan Borno Sainna Buba ya yi barazanar cutar da masu sukar APC, yana cewa za a 'karya yatsunsu' idan suka nuna adawa.

Buba ya ce masu goyon bayan gwamnati za su more amfanin gwamnati, yayin da waɗanda suka ƙi bi su za su fuskanci hukunci.

Kalamansa sun janyo suka kan dimokuraɗiyya, ’yancin faɗar albarkacin baki da kuma yadda jami’an gwamnati ke mu’amala da masu adawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.