2027: Bayan Hukuncin Kotu, PDP Ta Dauki Matsaya kan Takarar Sheikh Pantami a Jihar Gombe
- PDP ta ce za ta sake gudanar da zaɓen fitar da gwani na gwamnan Gombe bayan kotu ta soke takarar Farfesa Isa Pantami
- Kotun Tarayya ta umarci jam’iyyar ta gudanar da sabon zaɓen fitar da gwani cikin kwanaki 30 masu zuwa
- Jam’iyyar adawa ta PDP ta ce za ta bi umarnin kotu tare da tabbatar da bin tsarin dimokuraɗiyya da dokokinta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Gombe, Nigeria - Jam’iyyar PDP ta ce za ta gudanar da sabon zaɓen fitar da gwani na neman kujerar gwamnan Jihar Gombe a zaben 2027.
Hakan ya biyo bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya na soke zaben da ya samar da tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Isa Ali Pantami, a matsayin ɗan takarar PDP a Gombe.

Source: Facebook
Sakataren Yaɗa Labarai na PDP ta kasa, Haruna Mohammed Jungudo, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Alhamis, kamar yadda Punchi ta ruwaito.
Wane hukunci kotu ta yanke?
Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Gombe ta soke fitowar Pantami a matsayin ɗan takarar gwamna na PDP, sannan ta umarci jam’iyyar ta gudanar da sabon zaɓen fidda gwani cikin kwanaki 30.
Mai shari’a Amina Aliyu Mohammed ce ta yanke hukuncin, bayan wata ƙara da mai neman tikitin gwamna na PDP, Usman Aliyu Garry, ya shigar inda ya ƙalubalanci tsarin da ya samar da Pantami a matsayin ɗan takarar jam’iyyar..
Pantami ya samu tikitin PDP ne ta hanyar amincewar murya a wani zaɓen fidda gwani da aka gudanar a watan Mayu 2026, bayan ya fice daga jam’iyyar APC.
PDP za ta bi umarnin kotu
Da yake martani kan hukuncin, Jungudo ya ce PDP na nan kan matsayinta na tabbatar da dimokuraɗiyyar cikin gida, bin matakan da suka dace da kuma kiyaye kundin tsarin mulkinta da ƙa’idojin zaɓe.
Sanarwar ta ce:
"PDP ta lura da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Gombe, wanda ya soke zaɓen fidda gwani na jam’iyyar na farko na neman kujerar gwamnan Jihar Gombe tare da umartar gudanar da sabon zaɓe.
“PDP, a matsayinta na jam’iyya mai biyayya ga doka, tana mutunta tsarin doka da ikon bangaren shari’a. Saboda haka, jam’iyyar za ta nazarci hukuncin a hankali tare da ɗaukar matakan gaggawa domin tabbatar da bin umarnin kotun.
“Saboda haka, jam’iyyar za ta fara matakan da suka dace domin gudanar da sabon zaɓen fidda gwani na neman kujerar gwamnan Jihar Gombe bisa hukuncin kotun.”

Source: Twitter
Wani dan PDP, Rabiu Muhammd Shitu ya ce hukuncin da kotu ta yi ya sa sun fara zargin akwai wata makarkashiya da aka kulla don hana Pantami shiga zaben 2027.
Da yake hira da Legit Hausa, dan siyasar ya ce:
"Duk a mako daya, babbar kotun tarayya ta soke takarar Malam kuma aka ce kotun koli ta hana dan takara shiga zaben fitar da gwani fiye da daya, ni ina zargin duk hakan na da alaka da siyasar Gombe.

Kara karanta wannan
Kotun musulunci ta ɗauki matakin farko kan wadanda ake zargi da kisan Dan Shagamu a Kano
"Kuma in sha Allahu ko suna so ko ba su so, da yardar Allah Malam ne gwamnan jihar Gombe na gobe," in ji shi.
Pantami da Gwamna za su kece raini
Kun ji cewa ɗan takarar gwamnan jihar Gombe na jam'iyyar APC, Dr Jamil Isyaku Gwamna, ya ce a shirye yake ya yi muhawara da sauran 'yan takara.
Ɗan takarar gwamnan jihar na PDP, Farfesa Isa Ali Pantami, shi ma ya ce a shirye yake ya halarci muhawarar domin tattauna tsare-tsare, nasarori da makomar Gombe.
Asali: Legit.ng

