Ana Batun Zaben 2027, Kwankwaso Ya Aika Sako kan Makomar Najeriya
- Tsohon Gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa Najeriya za ta shawo kan ƙalubalen da take fuskanta
- Kwankwaso da Peter Obi sun tattauna dabarun faɗaɗa shirin NDC zuwa karkara da matakin al’umma domin isar da saƙon “ceto ƙasa”
- Ya ce haɗin gwiwarsu na da nufin rage talauci, yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, inganta tsaro da sauya Najeriya daga dogaro da amfani zuwa samar da kaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Abuja, Najeriya – Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan makomar Najeriya.
Sanata Kwankwaso ya bayyana kyakkyawan fata cewa Najeriya za ta shawo kan ƙalubalen da take fuskanta.

Source: Facebook
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, bayan ganawar da shi da wasu ’yan takarar NDC suka yi da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Peter Obi, a hedikwatar Obidient da ke Abuja.
Tawagar ta ƙunshi ’yan takarar gwamna, sanatoci da sauran masu neman mukamai na jam’iyyar.
NDC na son faɗaɗa tasirinta zuwa karkara
Kwankwaso ya ce tattaunawar ta mayar da hankali ne kan dabarun faɗaɗa da ƙarfafa tasirin NDC, musamman ta hanyar kai saƙon jam’iyyar na “ceto ƙasa” zuwa yankunan karkara da matakin al’umma.
Ya ce jam’iyyar za ta ci gaba da ƙarfafa tsarin shugabancinta da magoya bayanta a ƙananan hukumomi da garuruwa domin samun damar isar da manufofinta ga jama’a.
A cewarsa, wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin jam’iyyar na ƙara samun karɓuwa a tsakanin al’ummar Najeriya, musamman waɗanda ke zaune a yankunan karkara.
Abin da ya haɗa Kwankwaso da Peter Obi
Kwankwaso ya ce haɗin gwiwarsa da Peter Obi ya samo asali ne daga matsayar da suke da ita ta neman inganta rayuwar ’yan Najeriya masu fama da matsaloli.
Ya ce burinsu ya haɗa da fitar da marasa galihu daga talauci da kuma rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
Baya ga haka, ya ce haɗin gwiwar na neman tallafa wa ƙananan masana’antu da ’yan kasuwa, inganta tsaron ƙasa da haɗa kan al’umma.
Haka kuma, Kwankwaso ya ce suna son sauya tattalin arzikin Najeriya daga wanda ya fi karkata ga amfani da kaya zuwa tattalin arzikin da ya fi mayar da hankali kan samar da kaya da ayyuka.
“Najeriya za ta gyaru”
Da yake bayyana manufofin haɗin gwiwar, Kwankwaso ya ce:
“Haɗin gwiwarmu mai ƙarfi da Mai Girma Peter Obi ya samo asali ne daga ƙudurinmu na fitar da ’yan Najeriya masu rauni daga talauci, rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, tallafa wa ƙanana da matsakaitan ’yan kasuwa, tabbatar da tsaron ƙasa, haɗa kan jama’a da kuma sauya Najeriya daga amfani zuwa samarwa.”
Kwankwaso ya kuma bayyana cewa NDC za ta ci gaba da ƙarfafa tsarin jam’iyyar a matakin ƙasa tare da kai tsaye zuwa al’ummomin karkara.
A ƙarshe, tsohon gwamnan ya bayyana kyakkyawan fata kan makomar Najeriya, inda ya taƙaita saƙonsa da cewa:
“Najeriya za ta gyaru"

Source: Facebook
Abin da ya raba Kwankwaso da Sanata Hanga

Kara karanta wannan
"Gwamnatinmu ce"; Kwamishina ya yi barazanar guntile 'yan yatsun masu adawa da APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Rufai Hanga da ke wakiltar Kano ta Tsakiya a majalisar dattawa ya yi magana kan dalilinsa na raba gari da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Sanata Hanga ya bayyana cewa rashin jituwarsa da Kwankwaso, ta samo asali ne daga sabani kan ayyukan tallafa wa jama’a da harkokin siyasa.
Asali: Legit.ng

