Dattawa Za Su Caɓa, Dan Takarar Gwamnan ADC Ya Masu Alƙawarin Albashi duk Wata

Dattawa Za Su Caɓa, Dan Takarar Gwamnan ADC Ya Masu Alƙawarin Albashi duk Wata

  • Dan takarar gwamna a ADC, Olooye Adegboyega Taofeek Adegoke ya yi alkawarin biyan dattawa alawus duk wata
  • Adegoke ya kuma yi alkawarin aiwatar da cikakken ikon kananan hukumomi, da samar da ilimi kyauta daga firamare har zuwa sakandare a Oyo
  • Ɗan takarar ADC ya ce zai gina layin dogo daga Moniya a Ibadan zuwa Oke-Ogun, domin taimaka wa manoma jigilar amfanin gonarsu zuwa kasuwanni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ibadan, Oyo - Ɗan takarar gwamnan jam'iyyar ADC a Oyo, Olooye Adegboyega Taofeek Adegoke, ya yi alkawura ga dattawa.

Adegoke ya yi alkawarin biyan mazauna jihar ’yan shekara 75 zuwa sama alawus kowane wata.

Dan takarar gwamnan ADC ya yi alkawari ga dattawa

Source: Instagram

Adegoke ya yi alkawarin ba dattawa albashi

Ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar godiya da ya kai mazabar tarayya ta Irepo, Oorelope da Olorunsogo, inda ya kuma yi alkawarin samar da ilimi kyauta, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Kamfanin Opay ya nemi agajin DSS, ƴan sanda kan jita jitar zai gudu a Najeriya

Ya ce zai fara biyan alawus ɗin ne cikin kwanaki 100 na farko bayan kama aiki, idan aka zaɓe shi a matsayin gwamnan jihar a 2027.

Adegoke, ɗan kasuwa kuma mai taimakon jama’a, ya kuma sake jaddada aniyarsa ta tabbatar da cikakken ikon kananan hukumomi idan ya zama gwamna.

Ya ce ilimin kyauta zai shafi matakin firamare da sakandare a fadin Oyo, domin rage nauyin da iyaye ke fuskanta wajen ilimantar da ’ya’yansu.

Dan takarar ADC zai ba dattawa albashi
Taswirar jihar Oyo da ke Kudu maso Yammacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Alkawuran da Adegoke ya yi

Dan takarar ADC ɗin ya kuma yi alkawarin gina layin dogo da zai haɗa Moniya a Ibadan da yankin Oke-Ogun, cewar Daily Post.

Ya ce hakan zai sauƙaƙa safarar amfanin gonakin manoma zuwa Ibadan da sauran manyan kasuwannin birane.

Adegoke ya gode wa mazauna kananan hukumomin Irepo, Oorelope da Olorunsogo bisa goyon bayan da suka ba shi da kuma jam'iyyar ADC.

Ya ce zai sake dawowa yankin domin neman kuri’u idan lokacin yakin neman zaɓe ya buɗe a ranar 9 ga Satumba 2026.

Ya bayyana cewa duk da shirin ziyartar mazabun tarayya 14 da ke jihar domin gode wa al’umma, ya fara da Irepo, Oorelope da Olorunsogo ne saboda girmama shugaban ADC na Oyo, Afees Jimoh.

Kara karanta wannan

An samu ɓaraka, Ministan Tinubu ya fara takun saƙa da gwamnonin APC 2 a Najeriya

Godiya da dan takarar gwamna ya yi

Adegoke ya nuna godiyarsa ga mutanen Kishi, Igbeti da Igboho, inda ya yi alkawarin bai wa ci gaban yankunan fifiko idan aka zaɓe shi.

Ya ce tun kafin samun tikitin takarar gwamna na ADC, ya riga ya nuna jajircewarsa wajen ci gaban yankunan.

Ya kuma yi alkawarin samar da karin ababen more rayuwa a Oke-Ogun da sauran sassan Oyo.

A cewarsa, Oke-Ogun shi ne cibiyar samar da abinci a Oyo, kuma iliminsa kan tattalin arzikin noma ya ba shi fahimtar matsalolin manoma.

Dan takarar ADC ya raba masara

Kun ji cewa dan takarar gwamnan ADC a Oyo, Taofeek Adegoke ya tayar da kura a kafofin sadarwa yayin taron siyasa wanda al'umma suka cika.

Lamarin ya ja hankali ne bayan bidiyonsa yana rabon dafaffiyar masara ga magoya baya ya bazu a kafafen sada zumunta.

Magoya bayansa sun yi ta kiransa "Gwamna", suna karbar masarar kai tsaye daga hannunsa, yayin da wasu suka ce hakan alama ce ta tawali'u.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.