2027: An Samu Matsala a Taron Hadakar Jam’iyun Adawa domin Kifar da Tinubu

2027: An Samu Matsala a Taron Hadakar Jam’iyun Adawa domin Kifar da Tinubu

  • Taron gamayyar jam’iyyun adawa da aka shirya domin 2027 ya gamu da cikas, bayan Atiku, Obi, Kwankwaso da Amaechi sun kasa halarta
  • Jam’iyyun adawa da suka halarta sun amince da kafa tsarin haɗin gwiwa domin samar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda a zaɓen 2027
  • Masu shirya taron sun yi gargaɗin cewa rarrabuwar kawuna tsakanin ‘yan adawa na iya bai wa APC damar samun nasara a zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - An samu cikas a babban taron farko na ƙasa na jam’iyyun adawa, wanda aka shirya domin samar da haɗin kai gabanin babban zaɓen 2027.

Ƙungiyar G100 ce ta shirya taron tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar ‘Yan Majalisar Wakilai ta Ƙananan Jam’iyyun Adawa, a Cibiyar Shehu Musa Yar’Adua.

An samu matsala a taron hadakar jam'iyun adawa
Sanata Rabiu Kwankwaso, Atiku Abubakar da Peter Obi. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso, Atiku Abubakar, Mr Peter Obi.
Source: Twitter

An yi taron hadakar yan adawa

Kara karanta wannan

'Yan adawa sun fitar da tsarin kafa gwamnati a 2027 da kifar da Tinubu

Manufar taron ita ce samar da tsarin da zai taimaka wajen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda, tare da kafa gwamnatin riƙon kwarya ta shekaru huɗu, cewar The Nation.

Sai dai rashin halartar tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar na ADC, tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na NDC da tsohon ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya jefa taron cikin rashin tabbas.

Ba a bayar da wani bayani a hukumance daga jam’iyyun kan dalilin da ya sa waɗannan manyan ‘yan siyasar adawa suka kasa halartar taron ba.

Duk da haka, wasu jam’iyyun adawa sun halarci taron, ciki har da SDP, PRP, DLA da APM.

Wadanda suka halarta sun haɗa da ɗan takarar shugaban ƙasa na SDP, Prince Adewole Adebayo, da abokin takararsa, Dr Usman Bugaje; ɗan takarar PRP, Donald Duke; ɗan takarar DLA, Ambasada Moses Olusola; da abokin takarar mataimakin shugaban ƙasa na APM, Lawal Daura.

A jawabin buɗe taron, Darakta-Janar na G100, Salihu Mohd Lukman, ya yi gargaɗin cewa ci gaba da rarrabuwar jam’iyyun adawa na iya bai wa APC damar samun rinjaye a 2027.

Kara karanta wannan

'Yan adawa za su yi babban taro a yau domin shirin kifar da Tinubu a 2027

Lukman ya ce jam’iyyun adawa sun sha shiga zaɓen shugaban ƙasa daban-daban, lamarin da ya bai wa jam’iyya mai mulki damar cin gajiyar rabuwar ƙuri’un masu zaɓe.

Ya bukaci jam’iyyun su fara mayar da hankali kan samar da dokokin haɗin gwiwa kafin su fara tattauna batun ɗan takara.

Ya kuma gabatar da tsarin kafa Babbar Kwamitin Jagoranci, ƙungiyoyin aiki guda biyar da kuma yarjejeniyar ƙasa ta shekaru huɗu mai suna “National Covenant for Democratic Renewal”.

Ana shiri kan kifar da Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya yayin taken kasar. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: UGC

An ba yan siyasa shawara a Najeriya

Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Majalisar Wakilai ta Ƙananan Jam’iyyun Adawa, Frederick Agbedi, shi ma ya yi kira ga haɗin kai, yana cewa ya kamata shugabannin siyasa su fifita halin ƙuncin da ‘yan Najeriya ke ciki fiye da burinsu na kashin kansu.

Mataimakin Shugaban ADC na Ƙasa mai kula da Kudu maso Kudu, Usani Uguru Usani, wanda ya jagoranci tawagar jam’iyyarsa, ya bukaci mahalarta su yi aiki domin kayar da APC a 2027.

Shugaban PRP na ƙasa, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya ce babu wata jam’iyyar adawa guda da za ta iya kayar da APC ita kaɗai, yana bayyana shirin haɗin gwiwar a matsayin “genuine sign of hope for Nigerians”.

Kara karanta wannan

Atiku ya ragargaji Tinubu kan tafiya hutu Turai 'Najeriya na ci da wuta'

Tsohon gwamnan Niger, Babangida Aliyu, ya bukaci mahalarta su ci gaba da wannan tsari, yana nuna damuwa kan yadda bukatun kai da na kuɗi suka mamaye muradun ƙasa, cewar Punch.

Aliyu ya kuma shawarci masu shirya taron su faɗaɗa tattaunawar zuwa matakin jihohi da ƙananan hukumomi, domin tabbatar da cewa an haɗa ‘yan jam’iyya na ƙasa da ƙasa.

Ana shirin hadaka domin kifar da Tinubu

Mun ba ku labarin cewa kungiyar G-100 za ta gudanar da taron hadin kan jam’iyyun adawa a Abuja ranar 18 ga watan Agusta, 2026, gabanin zaben 2027.

Kungiyar ta gana da shugabannin jam’iyyun adawa shida domin tattauna yadda za a samar da hadin kai.

'Yan G-100 sun ce hadin kan adawa zai bukaci sadaukarwa da sassauci daga shugabannin jam’iyyun na adawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.