'Dan Takaran Gwamna a ADC Ya Aiko wa Mutanen Katsina Sako daga Gadon Asibiti

'Dan Takaran Gwamna a ADC Ya Aiko wa Mutanen Katsina Sako daga Gadon Asibiti

  • Sanata Ahmad Babba Kaita ya yi wa magoya baya da masoya magana daga inda yake kwance a asibiti
  • An yi wa ‘dan takaran gwamnan na Katsina aikin kashi a wani asibiti a waje, yanzu yana samun sauki
  • Kakakin kwamitin kamfen Babba Kaita, Abubakar Ahmed ya fitar da sanarwa yana yi wa jama’a godiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Katsina - Ahmad Babba Kaita mai neman takarar gwamnan jihar Katsina yana samun sauki a asibiti bayan aiki da aka yi masa.

‘Dan takarar jam’iyyar ADC a zaben gwamnan Katsina a 2027, Sanata Ahmad Babba Kaita ya je kasar waje inda aka yi masa aiki.

Sanata Ahmad Babba Kaita
Sanata Ahmad Babba Kaita a asibitin da aka yi masa aiki Hoto: Yasir Sani Dikko
Source: Facebook

Ahmad Babba Kaita ya yi magana daga asibiti

Da yake magana daga ketare, jaridar Leadership ta rahoto Ahmad Babba Kaita yana gode wa jama’a da addu’o’in da suka yi masa.

Kara karanta wannan

ADC ta shiga shirye shiryen dinke barakar da ta bijiro wa jam’iyyar a jihohi

‘Dan siyasar ya ga sakonni kuma ya ji adduo’in jama’a, yana mai sanar da su an yi masa aikin kashi lafiya domin an yi nasara.

Mai neman takarar gwamnan ya ce yana sa ran nan ba da dadewa ba zai dawo ya cigaba da harkokinsa kamar yadda ya saba.

Sanata Ahmad Babba Kaita ya ce ya ji dadin sakonnin da ya gani daga jama’a, inda ake ta yi masa fatansa samun cikakkiyar lafiya.

Jawabin 'dan takaran ADC, Sanata Babba Kaita

'Dan siyasar yake cewa:

“Ina so in tabbatar maku da cewa an yi aikin kashin lafiya kalau, kuma yanzu haka ina samun sauki
"In sha Allahu, nan ba da dadewa ba zan mike."

Tsohon ‘dan majalisar tarayyan ya kuma mika godiya ga jam’iyyar ADC da ta ba shi damar tsaya wa takarar gwamnan Katsina a 2027.

Babba Kaita ya kuma jinjina wa ‘yan takaran ADC na Katsina ganin kokarin da suke yi na kawo wa al’umma saukin rayuwa a jihar.

Kara karanta wannan

Kwamishina ya yi amai ya lashe kan barazana ga masu adawa da APC

'Dan takaran gwamnan yana sa ganin nasarar ADC

Jaridar nan ta Independent ta ce Sanata Kaita ya kuma yabi ‘yan ofishin yakin neman zabensa saboda yadda abubuwa suke ta gudana.

Duk da yana gadon asibiti, ya ce harkokin ADC sun cigaba da tafiya a fadin Katsina.

Ganin an tunkari yakin aben gwamnoni da ‘yan majalisar dokoki, Sanata Kaita ya ce suna sa ran za su ga bayan APC a jihar Katsina.

Sanarwar ta fito ne daga ofishin Kakakin kwamitin yakin zaben ABK, Abubakar Ahmed.

Hoton 'dan siyasar a kwance kamar yadda wani matashin 'dan ADC ya wallafa a Facebook.

Jam'iyyar ADC za ta sasanta rigimar cikin gida

Ganin zabe ya gabato, ana da labari ADC ta soma yin sulhu domin a tsallake takarar 2027 cikin nasara ta hanyar sasanta 'yan jam'iyya.

Kwamitin sulhun ADC zai yi aikin hada kan mambobin jam'iyyar a fadin kasar nan da nufin guje wa sakon kasa da makarkashiya a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Kashim ya fada wa abokai da masoya abin da yake bukata wajensu da ya cika 60

Shugaban jam'iyyar na kasa, Sanata David Mark ya dage zai kawar da duk abin da zai hana doke Bola Tinubu da jam'iyyarsa ta APC a badi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng