2027: Yadda Ta Kaya tsakanin Bala Lau da Abdulaziz Yari wajen Tallata Tazarcen Tinubu
- Abdulaziz Yari da wsu jagorori a APC sun ziyarci shugabannin kungiyar JIBWIS na tsagin Kaduna
- Abdullahi Bala Lau ya yi magana a matsayinsa na Shugaban Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah
- Malamin ya bada shawarwari, kuma ya yi kira ga ‘yan APC da su rika duba halin da talaka yake ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Darekta Janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a APC, Sanata Abdulaziz Yari ya ziyarci shugabannin Izala.
Tawagar Abdulaziz Yari tana ta zama da shugabannin kungiyoyin addinin Musulunci a kasar irinsu Tijanniyya, Qadriyya da JIBWIS.

Source: Twitter
Tawagar Abdulaziz Yari a gaban yan Izala
A ranar Litinin ne jaridar Tribune ta rahoto cewa Abdulaziz Yari ya hadu da Abdullahi Bala Lau da sauran kungiyar Izala.
Sheikh Abdullahi Bala Lau shi ne yake jagorantar kungiyar Izala ta bangaren Kaduna.
An yi magana a kan al’amuran da suka shafi kasa, rashin tsaro a yankin Arewa, matsin tattalin arziki da kuma hadin-kan kabilu.
Tawagar yakin zaben APC da ta ziyarci Izala
‘Yan tawagar APC sun hada da Dr. Abdullahi Umar Ganduje, Sanata Adamu Aliero, Ali Modu Sheriff da sakataren APC, Ajibola Bashiru.
Daily Trust ta ce an ga Rt. Hon. Aminu Masari, Nasiru Sani Zangon Daura, Rt. Hon. Ahmed Idris Wase da Hon. James Abiodun Faleke.
Shugaban Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah, Bala Lau ya yi kira ga shugabanni a kowane matakai su kula da talakawa.
Malamin ya fada wa Yari yadda suke kokarin ganin an samu zaman lafiya kamar yadda aka ji daga wani bidiyon Nuhu Sada a X.
Abin da Bala Lau ya fada wa Yari
Bala Lau ya ce duk yadda alaka ta ke tsakanin Izala da shugabannin na APC, ya kamata su bude kofar da za a rika yi masu wa’azi.
Ya ce:
“Muna fatan taimakon da mu ke yi da ku, ya zama ta yadda idan mun ga abin da ba daidai ba, mu ce a gyara kaza, a gyara kaza…
Wallahi idan ku ka yi wannan ba ku bukatar zuwa kamfe cikin al’ummarmu, kuna yawo al’umma za su rika cewa madalla, ana addu’a Allah ya fishe ka jin kunyar wanan kujera.
A matsayinsu na kungiyar addini kuwa, ya ce duk abin da aka bijiro masu da shi, dole sai sun yi nazarin shi kafin su dauki wani mataki.
Tare da Bala Lau akwai irinsu Sheikh Kabir Haruna Gombe da sauran manyan malamai.
Qadiriyya ta bi Shugaba Bola Tinubu
An ji jagoran ƙungiyar Qadiriyya a Afirka, Sheikh Qaribullah Sheikh Nasiru Kabara, ya bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Nadin Sanata Abdul’aziz Yari a matsayin Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen APC ya ƙara ƙarfafa alaƙar ƙungiyar da jam'iyyar APC.
'Yan Qadiriyya za su fara gudanar da addu'o'i na musamman don dorewar zaman lafiya, farfaɗo da tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma tsaro.
Asali: Legit.ng

