Kotu Ta Saki Fasfon Tsohon Ministan da Ake Tuhuma da Takardun Bogi Ya Tafi Asibitin Waje
- Alkali ta ba da umarnin a saki takardun fasfon Uche Nnaji domin ya iya balaguro bayan lauyansa ya shigar da bukatar hakan
- Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta karbi rokon lauyan wanda ake kara, Ogwu Onoja SAN, yanzu zai iya yin tafiya zuwa kasar waje
- An dage ci gaba da sauraron shari'ar da lauyoyin hukumar ICPC suka shigar har sau zuwa ranar 26 ga watan Oktoban nan mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Babbar kotun tarayya mai zama a garin Abuja ta bada izini a saki fasfon Uche Nnaji domin ya iya zuwa kasashen waje.
Uche Nnaji wanda ya rike Ministan kirkira, kimiyya da fasaha yana neman kotu ta ba shi dama ne ya je ketare domin ganin likita.

Source: Facebook
Tsohon ministan kimiyya zai iya fita waje
Jaridar Leadership ta rahoto cewa tsohon ministan ya samu hanyar fita kasar waje da nufin a duba shi a asibiti kamar yadda ya roka.
Alkali Joyce Abdulmalik ta bada wannan izini a ranar Litinin 21 ga watan Satumba 2026.
Hakan ya biyo bayan rokon da lauyan tsohon ministan tarayyar, Cif Ogwu Onoja SAN ya gabatar a babban kotun da ke birnin Abuja.
Zargin da su ke wuyan tsohon ministan
Hukumar ICPC tana tuhumar Uche Nnaji a kotun da laifuffuka shida da suka shafi amfani da takardun bogi da bada bayanan karya.
An san cewa sauran laifuffukan da ake zargin ya aikata a shari’ar mai lamba FHC/ABJ/CR/391/2026 sun hada da rashin gaskiya a aiki.
Lauyoyin ICPC sun ce N29,578,466.67 da Nnaji ya karba a matsayin albashi da alawus lokacin yana minista a gwamnati haramtattu ne.
Fasfon Nnaji ya dawo hannunsa
Kafin a bada belin shi a kan N20m kwanaki, sai da alkali ta sa sharadin ya damka wa kotu takardun fasfonsa na fita kasashen ketare.
Kafin ya samu beli lokacin sai da aka bukaci 'dan takaran gwamnan Enugu a 2027 ya kawo wanda zai tsaya masa a kotun tarayyar.

Kara karanta wannan
Hakar ma’adanai: Atiku ya tausaya wa yaro, ya dauki dawainiyar karatunsa a makaranta
Dole wanda za a kawo ya zama babban ma’aikacin gwamnati wanda ya kuma shafe akalla shekaru hudu bai canza wurin zama ba.
An sa shi ya kawo takardar daukarsa aiki da takardar albashinsa na watanni uku baya.
Tunda ya roki a kyale fita kasar waje wanan karo da sunan zuwa asibiti, alkalin ta yi umarni a maido masa fasfona tsawon lokacin.
Alkali ta dage shari'ar Nnaji da ICPC
Bayan nan, Premium Times ta ce a karshe an daga shari’ar sai 26 ga watan Oktoba 2026.
Legit Hausa ba ta da masaniya game da rashin lafiyar da ta ke damun tsohon ministan ko kuma asibiti ko kasar da zai je ganin likita.
Ko da za a samu wata matsala nan gaba a gagara ganin Mista Nnaji a kotu, doka za ta bada dama a cafko jami’in da ya samo belin shi.

Source: Facebook
Wike ya ambaci abokan fadansa a gwamnonin APC
Rahoto ya zo cewa Nyesom Wike, ya ambaci sunayen gwamnonin jam’iyyar APC da ke adawa da kungiyarsa ta Rainbow Coalition Movement.

Kara karanta wannan
Gwamna ya ɗauki zafi da 'yan bindiga suka shiga gari, suka kashe basarake a Najeriya
Ministan Babban Birnin Tarayya (Abuja) bai ga maciji da wasu gwamnoni, daga ciki har da shugaban kungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan Imo.
Wike ya yi zargin cewa gwamnonin suna adawa da ƙungiyar shi ne saboda muradun kansu na siyasa da harin shugabancin majalisa a 2027.
Asali: Legit.ng
