'Ya Danganta da Tinubu': Atiku kan Yiwuwar Halartar Muhawarar Shugaban Kasa

'Ya Danganta da Tinubu': Atiku kan Yiwuwar Halartar Muhawarar Shugaban Kasa

  • Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya yi magana game da halartar muhawarar shugaban ƙasa ta 2027
  • Mai magana da yawun Atiku, Kenneth Okonkwo, ya ce muhawarar da ake shirya wa tsakanin jam’iyyun adawa kaɗai dabara ce ta APC
  • ADC ta ƙalubalanci Bola Tinubu kan cire tallafin man fetur, tana mai cewa gwamnati ta gaza bayyana wa ’yan Najeriya amfanin matakin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana abin da zai saka ya halarci muhawarar ’yan takarar shugaban ƙasa gabanin zaɓen 2027.

Atiku ya tabbatar da cewa zai halarci muhawarar ne kawai idan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC suka halarta.

Atiku ya magantu kan muhawarar shugaban kasa a 2027
Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar da na APC, Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Atiku Abubakar, Sunday Dare.
Source: Getty Images

A wata sanarwa da kakakinsa na musamman, Kenneth Okonkwo, ya wallafa a shafinsa na X, ya bayyana yadda ake shirya muhawara tsakanin jam’iyyun adawa kaɗai a matsayin abin da ba zai ci gaba da kasancewa ba.

Kara karanta wannan

Atiku ya fito ya yi bidiyo kan dawo da tallafin mai da aka fara yada jita jita

Atiku ya gindaya sharadin halartar muhawarar shugaban kasa

Okonkwo ya ce Atiku, wanda ke jagorantar Ƙungiyar Jam’iyyun Adawa da Shugabanninsu, zai sanya halartar Tinubu da APC a matsayin sharadin halartarsa a kowace muhawarar shugaban ƙasa.

Ya ce babu inda APC za ta ɓuya a shekarar 2027, yana mai cewa Atiku a shirye yake ya tattauna da ’yan Najeriya ta wasu hanyoyi.

“Mai girma Atiku Abubakar a matsayinsa na jagoran Ƙungiyar Jam’iyyun Adawa da Shugabanninsu, ba shi da wani zaɓi face sanya halartar Shugaba Bola Tinubu da APC a matsayin sharadin halartarsa a kowace muhawarar shugaban ƙasa. Babu inda APC za ta ɓuya a 2027."

Okonkwo ya ƙara da cewa Atiku a shirye yake ya tattauna da ’yan Najeriya ta hanyar hira da manema labarai, tarukan jama’a, taron manema labarai da sauran dandamali.

Sanarwar ta ce Atiku ba zai shiga duk wata muhawara da za ta mayar da jam’iyyun adawa suna fafatawa tsakaninsu, tare da bai wa APC wata dama ta musamman ba.

Kara karanta wannan

'Kotu za ta hana Atiku takarar 2027,' Nafiu Bala bayan batun tallafin mai

Atiku ya soki salon mulkin Tinubu
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar yayin taron siyasa. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: UGC

Kalubalaen da Atiku ya jefa ga Tinubu

Atiku, ta bakin kakakinsa, ya kuma ƙalubalanci Tinubu da ya halarci muhawarar shugaban ƙasa ta ƙasa, domin jam’iyya mai mulki da jam’iyyun adawa su gabatar da manufofinsu ga ’yan Najeriya.

Okonkwo ya ce hakan zai bai wa ’yan Najeriya damar fahimtar manufofin ɓangarorin biyu da hanyoyin da suke shirin amfani da su wajen aiwatar da manufofin, domin su yanke shawara mai inganci a zaɓen 2027.

A ranar 18 ga Agusta 2026, kwana guda kafin fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya a hukumance, Atiku bai halarci taron sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta farko kan yaƙin neman zaɓe mai ma’ana ba a Abuja.

Atiku ya sake magana kan dawo da tallafi

A wani labarin, an ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce matsayarsa ba ta sauya ba kan shirin mayar da tallafin man fetur idan ya lashe zaben 2027.

Kara karanta wannan

APM ta hutar da 'yan adawa, ta gano dan takarar da zai lallasa Tinubu a zaben 2027

Atiku ya nesanta kansa da wasu kalaman mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, yana mai cewa bai yi magana da umarninsa ba.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce zai samar da tsarin tallafi da zai taimaka wajen rage tsadar makamashi da dawo da walwalar 'yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.