Ana Wata Ga Wata: Shugaban Amurka, Donald Trump Ya Canza Sunan Fasahar AI
- Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce daga yanzu za a riƙa kiran fsahar AI da “Super Intelligence” watau SI a gwamnatins
- Trump ya bayyana hakan ne yayin jawabin da ya gabatar a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 a birnin New York na kasar Amurka
- Ya ce kalmar “artificial” na sa fasahar ta yi kama da abin ƙirƙira na karya ne, alhali fasahar tana da matuƙar ƙarfi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
New York, US - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da cewa daga yanzu za a riƙa kiran fasahar Artificial Intelligence (AI) da “Super Intelligence” (SI), yana mai cewa sabon sunan ya fi bayyana ainihin fasahar.
Trump ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin jawabin buɗe taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 da aka gudanar a brinin New York na kasar Amurka.

Source: Getty Images
Ya ce Amurka ta ƙi amincewa da duk wani yunƙuri na samar da tsarin duniya da zai sanya dokoki kan amfani da AI, yana mai cewa daga yanzu za a riƙa amfani da sunan “Super Intelligence”, kamar yadda Punch ta rahoto.
“Amurka ba ta amince da duk wani yunƙuri na ƙirƙirar tsarin duniya na sarrafa AI da ake yawan magana a kai yanzu, wanda daga yanzu za a riƙa kiran sa a hukumance da Super Intelligence, wato na sauya sunan,” in ji Trump.
Dalilin Trump ya sauya sunan AI
Ya bayyana cewa kalmar “artificial” tana sa fasahar ta yi kama da abin ƙarya, duk da irin ƙarfin da take da shi.
“Amfani da kalmar artificial yana sa intelligence ya zama kamar ƙarya. Yana sa ya yi kama da abin ƙarya, alhali ba ƙarya ba ne. A zahiri, abin mamaki ne, amma dole ne mu yi taka-tsantsan,” in ji shi.
Trump ya ce za a sauya takardun gwamnatin Amurka domin amfani da kalmar “Super Intelligence” maimakon “Artificial Intelligence”, yana mai fatan sauran ƙasashe za su rungumi sabon sunan.
“Daga wannan lokaci, za a sauya dukkan takardun Amurka, kuma ina fatan na duniya ma, domin amfani da kalmar da ta fi dacewa, wato Super maimakon artificial. Don haka, Super Intelligence ce,” in ji shi.
Yadda matskin canza sunan AI ya fara
Sanarwar Trump ta zo ne kwanaki kaɗan bayan da ya nemi mabiyansa a kafar sada zumunta su zaɓi sabon suna ga fasahar AI, kamar yadda ABC News ta ruwaito.
A lokacin, ya gabatar da “Superior Intelligence”, “Extreme Intelligence” da “Supreme Intelligence” a matsayin wasu daga cikin sunayen da za a iya amfani da su.
A jawabin na Majalisar Ɗinkin Duniya, Trump ya kuma bayyana cewa Amurka za ta ci gaba da jagorantar ƙoƙarin bunƙasa wannan fasaha, tare da cewa ba zai hana ci gabanta ba.
Trump ya gargadi magoya bayansa
Kun ji cewa Donald Trump ya gargadi magoya bayansa na jam’iyyar Republican cewa za su “je wutar jahannama” idan ba su fito sun yi zaɓe a watan Nuwamba ba.
Trump ya gargadi magoya bayansa cewa nasarar ’yan Democrat a zaɓen Nuwamba za ta sauya abin da ya bayyana a matsayin nasarorin da gwamnatinsa ta samu.
Asali: Legit.ng

