Babbar Magana: Shugaba Tinubu da Kashim Shettima Sun Karya Dokar Najeriya a Lokaci 1

Babbar Magana: Shugaba Tinubu da Kashim Shettima Sun Karya Dokar Najeriya a Lokaci 1

  • Lauyan kare haƙƙin bil’adama, Inibehe Effiong, ya ce rashin Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima a Najeriya lokaci guda ya saɓa wa doka
  • Effiong ya ce Sashe na 145 na Kundin Tsarin Mulki ya tanadi yadda za a miƙa ikon shugaban ƙasa idan shugaban ya tafi hutu ko ya kasa gudanar da aikinsa
  • Ya buƙaci Majalisar Ƙasa ta shiga tsakani kan rashin shugaban ƙasa da mataimakinsa a ƙasar lokaci guda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Lauya mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama, Inibehe Effiong, ya bayyana rashin Shugaba Bola Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima a Najeriya lokaci guda a matsayin “saɓa wa kundin tsarin mulki."

Kalaman lauyan sun zo ne yayin da ake ci gaba da muhawara a tsakanin jama’a kan rashin shugaban kasa da mataimakinsa a Najeriya lokaci guda.

Kara karanta wannan

Bayan kusan shekaru 10, kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da kuskuren da Buhari ya yi

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a ofishinsa da ke fadar gwamnatin tarayya a Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Effiong ya bayyana hakan ne a shirin The Morning Brief na Channels tv ranar Talata, yayin da yake magana kan tasirin kundin tsarin mulki na tsawaita zaman Tinubu a ƙasashen waje da kuma tafiyar Shettima zuwa Amurka.

Tinubu ya tsawaita hutun aiki

Shugaba Tinubu ya tafi kasashen waje tun ranar 30 ga Agusta, lokacin da ya tafi Landan domin fara hutun aiki.

Fadar Shugaban Ƙasa ta sanar ranar Litinin cewa Tinubu ya ƙara tsawaita zamansa a ƙasashen waje da wasu kwanaki, kuma zai dawo Najeriya a ƙarshen mako.

Shi kuwa Shettima ya bar Abuja ranar 20 ga Satumba domin wakiltar Tinubu da jagorantar tawagar Najeriya zuwa taron Majalisar Ɗinkin Duniya da ake gudanarwa a New York.

Tinubu da Shettima sun karya doka

Effiong ya ce Sashe na 145 na Kundin Tsarin Mulki ya buƙaci a miƙa ikon shugaban ƙasa a hukumance idan ya tafi hutu ko kuma ya kasa gudanar da ayyukan ofishinsa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tsawaita hutun da yake yi a ƙasar waje, ya canza ranar dawowa Najeriya

Ya ƙara da cewa akwai wasu ayyukan kundin tsarin mulki waɗanda shugaban ƙasa ko mukaddashin shugaban ƙasa ne kawai zai iya aiwatarwa.

Lauyan ya ce:

“Wannan shi ne dalilin da ya sa Sashe na 145 ya tanadi cewa a kowane lokaci dole ne a samu shugaban ƙasa na zahiri ko kuma mukaddashin shugaban ƙasa,” in ji Effiong.
“Ƙaramin Sashe na 145(1) ya tanadi cewa idan shugaban ƙasa ya tafi hutu ko kuma ya kasa gudanar da ayyukan ofishinsa, dole ne ya aika da rubutacciyar sanarwa ga Shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Wakilai.
“Sashen ya ƙara tanadar da cewa idan shugaban ƙasa ya gaza aika da sanarwar cikin kwanaki 21, Majalisar Ƙasa za ta iya umartar mataimakin shugaban ƙasa ya gudanar da ayyukan shugaban ƙasa a matsayin mukaddashi.”
Shettima.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima a fadar Aso Rock Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Ya buƙaci Majalisa ta shiga tsakani

Effiong ya ce sama da kwanaki 21 sun wuce tun bayan barin Tinubu Najeriya, ba tare da an nuna wa jama’a wata sanarwa a hukumance da ke miƙa ikon shugaban ƙasa ga Shettima ba.

Ya bayyana lamarin a matsayin “yin watsi” da nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora wa shugaban ƙasa, sannan ya buƙaci Majalisar Ƙasa ta shiga tsakani.

Kara karanta wannan

Kabir Masari: Yadda wani dan Arewa ya zama dan gaban goshin Tinubu

“Abin da Shugaba Tinubu ya yi ba wai kawai yin watsi da nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora masa ba ne; saɓa wa doka ne kai tsaye kuma ya kamata a tilasta masa,” in ji shi.

Tinubu ya tura Shettima taron UNGA

Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya tura Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya wakilce shi a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81.

Shettima zai jagoranci tawagar Najeriya da ta ƙunshi gwamnoni, ministoci da wasu manyan jami’an gwamnati zuwa birnin New York.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262