Yadda Wike da Wasu Gwamnoni Suka yi wa Atiku da Peter Obi Gadar Zare
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana yadda gwamnonin G-5 suka tsara dabarar da ta taimaka wa Peter Obi samun ƙuri'u a wasu jihohin Kudu
- Wike ya ce sun yi la'akari da ƙarfin jam'iyyar PDP a Edo da Cross River tare da ganin Atiku Abubakar zai iya amfana da ƙuri'un yankin
- Ya bayyana cewa G-5 ta hana Obi samun nasara a Rivers saboda damuwar cewa hakan na iya aika wani saƙo na siyasa da ba sa so
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana yadda gwamnonin G-5 suka yi amfani da wata dabara wajen hana Atiku Abubakar samun ƙuri'u a wasu jihohin Kudu maso Kudu a zaɓen 2023.
Wike ya ce gwamnonin sun yi hakan ne domin jam'iyyar PDP kada ta samu damar cin zaɓe a wasu jihohin da take da ƙarfi, inda suka bar ɗan takarar LP, Peter Obi, ya samu nasara.

Kara karanta wannan
Dickson: Jagoran NDC na kasa ya fadi dalilin kin shiga APC, ya aika sako ga Kwankwaso da Obi

Source: Twitter
TVC ta ruwaito cewa Wike ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Journalists’ Hangout na tashar.
Yadda G-5 ta taimaka wa Obi
Wike ya ce gwamnonin G-5 sun zauna tare suka tsara dabarar da za ta hana Atiku amfana da ƙarfin PDP a wasu jihohin Kudu maso Kudu.
Ya ce a Edo sun san PDP tana da ƙarfi, don haka suka yanke shawarar barin Obi ya karɓi ƙuri'un maimakon Atiku.
“Ta yaya ya ci? Lokacin da mu G-5 muka zauna, mun tsara dabararmu. Mun ce a Edo, PDP ta fi ƙarfi a Kudu maso Kudu. Matsalarmu za ta kasance Atiku. Saboda haka, maimakon Atiku ya karɓi ƙuri'un, bari su tafi LP. Wannan ita ce dabararmu,”
In ji shi.
Punch ta wallafa cewa Wike ya ce an yi amfani da irin wannan dabarar a Cross River domin rage damar Atiku na samun ƙuri'u daga jihar.
Me yasa Obi ya fadi a Rivers?
Ministan ya ce Rivers ce kaɗai aka ɗauki mataki na musamman a kanta, inda suka hana Obi samun nasara saboda abin da suka ɗauka a matsayin illar siyasa.
“Rivers ce kaɗai muka ce muna da matsala a nan. Obi ba zai ci a nan ba, domin idan ya ci, hakan zai aika wani saƙo a wani wuri da mutane ba za su fahimta ba. Kuma muka hana shi,”
In ji Wike.
Ya ce dabarar ta samo asali ne daga tunanin cewa idan PDP ba ta yi nasara a Kudu maso Kudu ba, hakan zai zama hasara ga Atiku, yayin da nasarar Obi ba za ta taimaka masa sosai wajen neman kujerar shugaban ƙasa ba.
G-5 sun yaki Atiku
G-5 ya ƙunshi gwamnonin PDP biyar da suka nuna adawa da takarar Atiku Abubakar a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Ƙungiyar ta ƙunshi Seyi Makinde na Oyo, Samuel Ortom na Benue, Okezie Ikpeazu na Abia, Nyesom Wike na Rivers da Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu.
Gwamnonin sun yi adawa da takarar Atiku ne bisa hujjar cewa ya kamata a mayar da tikitin shugaban ƙasa zuwa Kudu bayan shekara takwas da shugaban ƙasa daga Arewa, Muhammadu Buhari, ya yi kan mulki.

Source: Facebook
Wike ya ce ya kamata Obi ya fara tunanin zaɓen 2031 maimakon 2027, yana mai cewa yanayin siyasar da ya taimaka masa a 2023 ya canza.
Maganar goyon Obi da NDC
A wani labarin, kun ji cewa Isaac Fayose ya yi ikirarin cewa wasu gwamnoni biyar da aka zaɓa a ƙarƙashin jam'iyyar APC suna ba da goyon baya a ɓoye ga jam'iyyar NDC a 2027.
Fayose ya yi wannan ikirarin ne a daidai lokacin da ake magana kan zaben 2027, inda ya ce gwamnonin sun yi alkawarin tallafa wa yaƙin neman zaɓen NDC da kuɗi.
Ya ce gwamnonin ba za su fito fili su yi wa NDC kamfen ko su yi kalaman da za su amfani jam'iyyar ba, saboda kasancewarsu 'yan APC, amma sun yi alkawarin tallafa mata a ɓoye.
Asali: Legit.ng

