NELFUND: Gwamna Abba Ya Ware Bangaren da Yake Ganin Tinubu Ya Kawo Sauyi a Najeriya
- Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya yaba wa Shugaba Tinubu kan kafa Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND)
- Ya ce NELFUND yana matukar taimaka wa ɗalibai da iyayensu wajen samun kuɗin karatu a manyan makarantu
- Dalibai 1,101 ne suka kammala karatu a Jami’ar Al-Istiqama ta Sumaila, wanda Gwamna Abba ya halarci bikin yaye su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan ƙirƙirar Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND).
Gwamna Abba ya bayyana cewa shirin wani muhimmin mataki ne da zai iya faɗaɗa damar samun ilimin manyan makarantu a Najeriya.

Source: Twitter
Tribune Nigeria ta rahoto cewa Abba ya bayyana hakan ne a bikin yaye ɗalibai na haɗaka karo na biyu da na uku na Jami’ar Al-Istiqama da ke Sumaila, inda ɗalibai 1,101 suka kammala karatu.
Abba ya yaba wa Tinubu kan NELFUND
Gwamnan ya ce NELFUND zai samar wa ɗalibai da iyayensu ƙarin damar biyan kuɗin manyan makarantu tare da rage matsalolin kuɗi da ke hana wasu samun ilimi a matakin gaba da sakandare.
A cewarsa, zuba jari a fannin ilimi zuba jari ne ga makomar Jihar Kano da Najeriya, yana mai jaddada cewa samun al’umma mai ilimi da ƙwarewa na da muhimmanci wajen samun ci gaba mai ɗorewa.
Ya nuna godiyarsa ga Gwamnatin Tarayya kan tallafin da take bai wa ɓangaren ilimi, musamman kafa NELFUND.
A cewarsa, shirin muhimmin mataki ne wajen faɗaɗa damar samun ilimin manyan makarantu, ta hanyar bai wa ɗalibai damar samun lamuninnkuɗi don karatunsu a manyan makarantu daban-daban.
Gwamna Abba Kabir ya shawarci ɗalibai
Gwamnan ya buƙaci ɗaliban da suka kammala karatun su yi amfani da ilimi da ƙwarewar da suka samu wajen ayyukan da za su amfani jama’a, tare da bayar da gudunmawa mai ma’ana Jihar Kano da Najeriya.

Kara karanta wannan
Gwamna ya ɗauki zafi da 'yan bindiga suka shiga gari, suka kashe basarake a Najeriya
Ya kuma yaba wa shugabanci da ma’aikatan Jami’ar Al-Istiqama bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen bunƙasa ilimin manyan makarantu a Kano da samar wa matasan Najeriya damar yin karatu.

Source: Facebook
Ya taya ɗaliban murnar kammala karatunsu cikin nasara, tare da ƙarfafa musu gwiwa su ci gaba da bin tsarin ladabtarwa, gaskiya da sauran kyawawan ɗabi’un da suka koya a lokacin karatunsu.
Abba ya kuma ƙarfafa musu gwiwa su rungumi ƙirƙire-ƙirƙire, kasuwanci da kuma ci gaba da neman ilimi, yana mai cewa ƙwarewar da ta dace za ta taimaka musu wajen tunkarar ƙalubalen zamani da bayar da gudunmawa ga ci gaban al’ummominsu.
Gwamna Abba ya gargadi yan siyasar Kano
Kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya gargadi yan siyasa, magoya baya da jam'iyyu yayin da ake shirye-shiryen zaben 2027.
Abba ya bukaci jam’iyyun siyasa da magoya bayansu kan gujewa kalaman kiyayya, tsokana, barazana da tashin hankali yayin da yakin neman zabe.
Asali: Legit.ng
