Atiku zai Rattaba Hannu kan Dawo da Tallafin Man Fetur da 'Yan Najeriya

Atiku zai Rattaba Hannu kan Dawo da Tallafin Man Fetur da 'Yan Najeriya

  • Jigon jam’iyyar ADC, Ralph Nwosu, ya ce Atiku Abubakar zai rattaba yarjejeniya da ’yan Najeriya kan farashin man fetur idan ya lashe zaɓen 2027
  • Mr. Nwosu ya ce yarjejeniyar za ta bayyana farashin man fetur da sauran manufofin tattalin arzikin Atiku Abubakar da ya shirya kawo wa jama'a
  • Ya ce tawagar kamfen ɗin Atiku na tsara shirin kwanaki 100 na farko na gwamnatin sa domin tabbatar da cewa alkawuran sun tabbata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Tsohon shugaban ADC, Ralph Nwosu, ya ce ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, zai kulla yarjejeniya ta musamman da ’yan Najeriya kan farashin man fetur idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a 2027.

Kara karanta wannan

Ba irin na baya ba ne"; Amaechi ya fayyace shirin Atiku na dawo da tallafin fetur

Atiku ya sha nanata cewa zai dawo da tallafin man fetur, yana mai cewa cire tallafin ya ƙara tsananta matsin tattalin arziki tare da jefa ƙarin ’yan Najeriya cikin talauci.

Atiku Abubakar zai kulla yarjejeniya da yan kasar nan
Alamar jam'iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta kawo labarin cewa Nwosu, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis 27 ga waran Agusta, inda yake magana kan shirin Atiku na dawo da tallafin man fetur.

Atiku Abubakar zai yi magana kan man fetur

Politics Nigeria ta wallfa cewa Nwosu ya ce a lokacin kamfen ɗin Atiku za a bayyana wa ’yan Najeriya dalla-dallan yadda za a aiwatar da manufar, ciki har da farashin man fetur da ake sa ran za a samar.

A cewar Nwosu, Atiku zai yi wa ’yan Najeriya cikakken alkawari tun kafin ya hau kujerar shugaban ƙasa, sannan zai tabbatar da cewa ya cika alkawarin.

Ralph Nwosu ya ce za a samar da yarjejeniya kan man fetur
David Mark tare da Ralph Nwosu Hoto: ADC Coalition 2027
Source: Facebook

A kalamansa:

“Atiku zai rattaba yarjejeniya. Nan ba da jimawa ba za mu ƙaddamar da ainihin kamfen ɗinmu. Yanzu dai mun fara kunna wutar kamfen ne kawai."

Ya ƙara da cewa yarjejeniyar za ta ƙunshi takamaiman alkawura kan farashin man fetur da sauran manufofin tattalin arzikin Atiku.

Kara karanta wannan

Kamar Atiku, an samu 'dan takarar shugaban kasa da zai dawo da tallafin man fetur

Atiku ya fitar da tsarin mulkin Najeriya

Ya bayyana cewa tawagar kamfen ɗin tana tsara shirin kwanaki 100 na farko na gwamnatin Atiku idan ta samu mulki, domin tabbatar da cewa alkawuran da ɗan takarar ya yi suna da tsare-tsare masu kyau.

Ya ce:

“Kamfen ɗin Atiku ya riga ya fara zama yana tsara abin da zai yi a kwanaki 100 na farko na mulkinsa, domin kada mu riƙa yin maganganun da ba su da tushe.

Atiku ya sha bayyana cewa Najeriya, kasancewar tana da dimbin albarkatun ƙasa, za ta iya samar da sauƙi ga ’yan ƙasa tare da ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi alkawarin magance matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro na rayuka da dukiyoyi idan aka zaɓe shi a 2027.

Ina fafatawa da barayi - Atiku

A wani labarin, kun ji cewa Atiku Abubakar da ke takarar shugaban kasa a inuwar ADC ya zargi masu mulki da satar zabe da kuma lalata tattalin arzikin Najeriya.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Shirin Atiku na dawo da tallafin mai na iya tsorata wasu yan ƙasashen waje

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya sake tabbatar da cewa zai dawo da tallafin man fetur idan aka zabe shi a 2027 domin saukakawa talakawan kasar nan.

Alhaji Atiku Abubakar ya ce cire tallafin man fetur ya jefa karin ‘yan Najeriya cikin talauci, yayin da Tinubu ya soki manufarsa tare da cewa zai mai da kasar nan baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng