‘Akwai Gagarumar Matsala’: Malamin Addini Ya Bukaci Tinubu Ya Hakura da Takara
- Wani malamin addini a Najeriya ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya janye aniyarsa ta sake neman takarar shugaban ƙasa a 2027
- Malamin ya ce tsadar kayan masarufi da wahalhalun rayuwa na addabar talakawa, ya ce shugabanci bai magance matsalolin ba
- Faston ya kuma gargadi masu son mayar da Najeriya ƙasar addini guda, yana cewa hakan ya saba da tsarin Allah
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Wanda ya kafa Clear Revelation Ministry, Fasto Oluwarotimi Adeyeye, ya ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan zaben 2027.
Faston ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya janye aniyarsa ta sake neman takarar shugaban ƙasa a 2027.

Source: Twitter
Adeyeye ya yi wannan kiran ne a yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya gudanar a karshen mako, inda ya bayyana damuwarsa kan halin da ƙasar ke ciki, cewar Tribune.
Musabbabin da ake son ya hakura da takara
Ya ce matsalolin tattalin arziki da tsaro na ci gaba da yin illa ga ’yan Najeriya, musamman mutanen da ke zaune a matakin ƙasa.
Malamin ya ce shugabancin siyasa a Najeriya ya kasa magance wasu manyan matsalolin da ke addabar ’yan ƙasa, musamman talakawa.
Ya ce:
“Ƙasar ba ta cikin wani yanayi mai kyau. Ba dadi ga mutane. Mutanen da ke saman matakala ne kawai suke yin abin da suke so. Idan suna son sayen jirage biyu ko ma guda goma sha biyu, suna da kuɗin, amma mutanen da ke ƙasa suna wahala.”

Source: Twitter
Abubuwan da suka jawo karuwar barace-barace
Adeyeye ya ce wahalhalun da ake fuskanta a ƙasar sun kuma taimaka wajen ƙara yawan masu bara, yana mai cewa lamarin na bukatar daukar matakin gaggawa daga shugabannin siyasa, cewar Daily Post.
Ya roki Tinubu da kada ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027, yana cewa matsayinsa ya samo asali ne daga yadda yake kallon halin da ƙasar ke ciki, ba wai saboda ƙabilanci ba.
Ya ce:
“Ina roƙon Tinubu kawai kada ya tsaya takara a 2027. Ba batun kasancewar ni da Bayarbe ba ne. Zan iya gaya muku cewa Tinubu ya taimaka wa mutane da dama wajen cimma burinsu na rayuwa, amma mai yiwuwa ba zai cimma burinsa na sake lashe zaɓe a 2027 ba.
“Abin da ke gabanmu ya fi kowane mutum girma. Da ni ne shi, ba zan tsaya takara ba. Wannan ita ce shawarar da zan ba shi.”
Sai dai malamin ya amince da wasu nasarorin da Bola Tinubu ya samu, yana mai bayyana shi a matsayin shugaba da ya taimaka wa mutane da dama wajen cimma burinsu na rayuwa.
Adeyeye ya kuma nuna damuwa cewa ci gaba da wahalhalun tattalin arziki na iya shafar damar Tinubu ta siyasa a 2027 idan lamarin bai inganta ba.
Tinubu zai tafi hutun makonni ketare
A wani labarin, an ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya bar babban birnin tarayya Abuja zuwa Turai domin fara hutun makonni uku na shekara.
Birnin London da ke kasar Birtaniya ne zangon farko na hutun shugaban kasar wanda ke neman wa'adi na biyu a zaben 2027.
Ana sa ran Tinubu zai dawo Najeriya bayan hutun domin shiga yakin neman zaben shugaban kasa na Janairu 2027.
Asali: Legit.ng


