Tafiyar Tinubu: Sowore Ya Sanar da Majalisa Hanyar Mika Mulki ga Shettima

Tafiyar Tinubu: Sowore Ya Sanar da Majalisa Hanyar Mika Mulki ga Shettima

  • Omoyele Sowore ya nemi Majalisar Tarayya ta yi amfani da Sashe na 145(2) domin bai wa Kashim Shettima damar gudanar da ayyukan Shugaban Ƙasa
  • Kiran ya biyo bayan cikar kwanaki 21 da Sowore ya ce Kundin Tsarin Mulki ya tanada yayin da Shugaba Bola Tinubu ke wajen Najeriya
  • Sowore ya nemi shugabannin Majalisar Tarayya su bayyana ko sun karɓi sanarwar da Sashe na 145 ya tanada kafin Shugaba Tinubu ya tafi hutu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na African Action Congress (AAC) a zaɓen 2027, Omoyele Sowore, ya nemi Majalisar Tarayya ta yi amfani da Sashe na 145(2) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999.

Sowore ya ce ya kamata Majalisar ta bai wa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, damar gudanar da ayyukan Shugaban Ƙasa a matsayin Mukaddashin Shugaban Ƙasa.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: Dalilin da ya sa Tinubu ya ki zuwa Amurka, ya tura Shettima taron UNGA

Sowore ya yi magana kan tafiyar Tinubu
Dan takarar shugaban kasa a 2027, Omoyele Sowore Hoto: Omoyele Sowore
Source: Facebook

Ya yi wannan kiran ne a shafinsa na Facebook ranar Talata, 22 ga watan Satumban 2026, bayan cikar kwanaki 21 da ya ce an tanada wa Shugaba Bola Tinubu domin hutunsa, yayin da Shugaban Ƙasar ke ci gaba da zama a wajen Najeriya.

Tinubu ya tsawaita zaman sa a ƙasashen waje

Tinubu ya bar Najeriya ranar 30 ga Agusta 2026 domin hutun makonni uku. Sai dai Fadar Shugaban Ƙasa ta sanar a ranar 21 ga Satumba cewa Shugaban Ƙasar ya tsawaita zaman nasa a ƙasashen waje da wasu ’yan kwanaki.

Sowore ya ce Sashe na 145 na Kundin Tsarin Mulki ya tanadi cewa idan Shugaban Ƙasa ya tafi hutu ko kuma wani dalili ya hana shi gudanar da ayyukan ofishinsa, dole ne ya aika da rubutacciyar sanarwa ga Shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Wakilai.

Abin da Sashe na 145(2) ya tanada

Sowore ya ce Sashe na 145(2) ya tanadi cewa idan Shugaban Ƙasa ya kasa ko ya gaza aika da wannan sanarwa cikin kwanaki 21, Majalisar Tarayya za ta iya, da rinjayen kuri’u a kowace majalisa, bai wa Mataimakin Shugaban Ƙasa ikon gudanar da ayyukan Shugaban Ƙasa a matsayin Mukaddashi.

Kara karanta wannan

Ta tabbata Tinubu ba zai je Amurka ba, ya ba Shettima umarni kan taron UNGA

Ya ce har yanzu babu wata sanarwa a bainar jama’a da ta tabbatar da cewa an aika da sanarwar da Sashe na 145(1) ya tanada domin miƙa wasu ayyukan Shugaban Ƙasa ga Shettima.

Saboda haka, ya nemi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, su bayyana ko sun karɓi sanarwar da Kundin Tsarin Mulki ya tanada.

Sowore ya ƙi amincewa da kalmar “hutu na aiki”

Sowore ya kuma yi watsi da bayanin Fadar Shugaban Ƙasa da ke bayyana zaman Tinubu a ƙasashen waje a matsayin hutu yayin da yake ci gaba da aiki.

Sowore ya ƙara da cewa bayanin Fadar Shugaban Ƙasa cewa Tinubu na ci gaba da gudanar da harkokin gwamnati daga ƙasashen waje bai warware tambayar da ya gabatar kan tsarin da Kundin Tsarin Mulki ya tanada game da rashin Shugaban Ƙasa ba.

Shettima ya bar Najeriya da Tinubu
Kashim Shettima na gaisawa tare da Shugaba Bola Tinubu Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Sowore ba zai yi ofoshin uwargidan shugaban kasa ba

A wani labarin kuma, kun ji cewa Omoyele Sowore, ya ce ba zai amince da Ofishin Uwargidan Shugaban Ƙasa ko ci gaba da tafiyar da shi ba idan ya zama shugaban Najeriya.

Ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya bai tanadi Ofishin Uwargidan Shugaban Ƙasa ba, yana mai cewa zama shugaban ƙasa ba zai shafi aurensa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng