An Tona 'Sirrin' Obi a Anambra don Ya Hakura da Takarar 2027
- Gwamnatin jihar Anambra ta buqaci tsohon gwamnan jihar, Peter Obi, da ya cika alqawarinsa na janye takarar shugaban qasa idan aka samu shaidar barin bashi
- Offishin yada labarai na jihar ya fitar da wata wasika ta shekarar 2006 da ke nuna bukatar biyan albashin ma'aikatan hukumar ruwa da ba a biya ba
- Magoya bayan Obi sun yi martani da cewa wasikar ta kasance ne makonni kalilan bayan ya kama aiki, wanda ke nufin bashin gwamnatin da ya gada ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Anambra – Gwamnatin jihar Anambra ta ƙalubalanci Peter Obi, da ya fice daga takarar shugaban ƙasa na shekarar 2027 sakamakon abin da ta kira karya alƙawuran da ya ɗauka kan al'amuran bashi da biyan albashin ma'aikata.
A cikin wata sanarwa da ofishin yaɗa labarai na gwamnatin jihar ya fitar an tambaya cewa: "A yaushe ne Peter Obi zai janye daga yakin neman zaben shugaban kasa?"

Source: Facebook
Vanguard ta rahoto cewa gwamnatin jihar ta tunatar da al'umma irin alƙawuran da Obi ya ɗauka a baya na cewa zai yi murabus ko janye takararsa idan har aka tabbatar da ya bar jihar Anambra cikin bashi ko kuma aka samu saɓani wajen biyan albashi.
Shaidar da gwamnati ta fitar
Gwamnatin jihar ta haɗa sanarwar tata da wata wasiƙa mai kwanan wata 25 ga watan Afirilu, 2006, wadda ake zargin shugaban ma'aikatan Obi na lokacin, Chuks Iloegbunam, ya sanya wa hannu yana mai roƙon Obi da ya biya albashin ma'aikatan hukumar ruwa ta jihar Anambra.
Wasiƙar ta bayyana cewa albashin ma'aikatan hukumar na kowane wata ya kai kimanin naira miliyan 15 kuma rabon da a biya su tun watan Fabrairu na waccan shekarar.
Sanarwar ta ƙara da cewa:
"Ya yi alƙawarin janye takararsa idan har aka tabbatar da ya bar jihar Anambra cikin bashi. A matsayinsa na gwamna, ya yi alƙawarin murabus idan ba a biya ma'aikata albashi a kan lokaci ba. Ya karya duka biyun. Ya bar ofis a shekarar 2014 da tarin bashi mai yawa."

Kara karanta wannan
Gwamna ya ɗauki zafi da 'yan bindiga suka shiga gari, suka kashe basarake a Najeriya
Wani bincike da aka yi
Punch ta ruwaito cewa da ake bincike an gano Obi ya shafe mako biyar kacal a kan mulki lokacin da aka rubuta wasiƙar a ranar 25 ga Afirilu, 2006, bayan rantsar da shi a ranar 17 ga Maris, 2006, wanda hakan ke nuni da cewa bashin albashin ya faru ne kafin hawansa mulki.
Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar, Dr Law Mefor, ya ce Obi ya bar bashin gida da na waje har naira biliyan 127.4 zuwa watan Yuni na shekarar 2026.

Source: Getty Images
Sai dai mai taimakawa Obi kan harkokin yada labarai, Idris Zekeri Jnr, ya qaryata waɗannan zarge-zarge, inda ya jaddada cewa Obi ya bar mulki ba tare da bin bashin albashi ko 'yan kwangila ba.
Dabarar Wike ga Obi da Atiku
A wani labarin, mun ruwaito cewa Nyesom Wike ya bayyana dabarun da su gwamnonin ƙungiyar G-5 suka yi amfani da su wajen dakile nasarar Atiku Abubakar a 2023.
Wike ya bayyana cewa ƙungiyar ta amince da ba wa Peter Obi damar samun nasara a jihohin Edo da Cross River domin hana Atiku samun nasara a yankin.
Sai dai kuma ya ce sun toshe damar Obi na yin nasara a jihar Rivers saboda sakamakon siyasar da hakan zai haifar a jihar da ma Najeriya ma.
Asali: Legit.ng

