Tinubu na tsaka Mai Wuya, Sama da 67% na Yan Najeriya na So a Dawo da Tallafin Fetur

Tinubu na tsaka Mai Wuya, Sama da 67% na Yan Najeriya na So a Dawo da Tallafin Fetur

  • Atiku Abubakar ya ce wani binciken SBM Intelligence ya nuna kashi 67.4% na ’yan Najeriya na son a dawo da tallafin man fetur
  • Dan takarar na ADC ya ce tsadar man fetur na ƙara tsadar sufuri da sauran abubuwan more rayuwa ga iyalai da ’yan kasuwa
  • Atiku ya ce idan aka zaɓe shi, zai samar da sabon tsarin tallafin samar da man fetur da aka tace a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce wani rahoton bincike na SBM Intelligence ya nuna cews 67.4% na ’yan Najeriya na son a dawo da tallafin man fetur.

Atiku ya ce sakamakon binciken ya nuna yadda iyalai, ma’aikata da ’yan kasuwa ke fuskantar matsin tattalin arziki yayin da tsadar man fetur ke ci gaba da ƙara tsadar rayuwa.

Kara karanta wannan

2027: Tsohon sakataren gwamnatin Najeriya ya sauya sheka, ya bi tafiyar su Kwankwaso a NDC

Atiku.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Mataimakinsa na Musamman kan Sadarwar Jama’a, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Talata.

Atiku ya ce man fetur shi ne matsala ta biyu da aka fi ambata a matsayin babbar matsalar ƙasa, sannan manufar cure tsllafi ita ce mafi muni da mutane suka fi nuna damuwa a kanta.

“Wannan bincike ba batun manufofin tattalin arziki kawai ba ne, ya zama batun dimokuraɗiyya. Idan mafi yawan ’yan Najeriya suka bayyana cewa manufar gwamnati na lalata rayuwarsu, to ya kamata shugabanci ya saurare su,” in ji Atiku.

Ya ce matsalar man fetur ta fi tsanani a yankunan karkara, inda 32.4% na waɗanda aka yi wa binciken suka bayyana shi a matsayin babbar matsalarsu, idan aka kwatanta da 11.7% a birane.

Haka kuma, man fetur ya kasance matsala mafi girma a yankin Kudu maso Yamma da kashi 30.5 da kuma Kudu maso Kudu da kashi 29.1%, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Atiku ya jero mutane 3 da ya kamata su amsa tambayoyi kan mutuwar matasa 37 a hannun NSCDC

Atiku ya dora laifin kan cire tallafi

Atiku ya danganta tsananin wahalhalun da ake ciki da cire tallafin man fetur, yana mai cewa matakin ya ƙara tsadar sufuri da abinci tare da rage ƙarfin saye na iyalai da ’yan kasuwa.

“Shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur ne da taken yaƙin neman zaɓe, ba tare da tsari ba. Bai da ingantaccen shiri kan tace man fetur a cikin gida, sufuri, kare albashi ko miliyoyin ƙananan ’yan kasuwa da suka dogara da makamashi mai araha,” in ji shi.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce mafita ba za ta kasance komawa tsohon tsarin tallafin fetur ba, sai dai samar da tsarin samar da man fetur da aka tace a Najeriya kuma aka sayar wa ’yan Najeriya.

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadr Aso Rock da ke Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Atiku ya ce idan aka zaɓe shi, daga ranar 29 ga Mayu, 2027, zai ƙaddamar da tsarin tallafin samar da man fetur da aka tace a Najeriya kuma aka sayar wa ’yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Atiku ya 'tona wayau' da Tinubu yake shirin yi game da tallafin fetur

Atiku ya caccaki Tinubu kan tsadar fetur

Kun ji cewa Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan yadda farashin man fetur ya kai N1,470 kan kowace lita a Najeriya.

Atiku ya ce farashin danyen mai a yanzu ya kai $102.52 kan kowace ganga, amma 'yan Najeriya na biyan kudin mai fiye da lokacin da danyen mai ya kai $147 a 2008.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262