'Yan Najeriya Sun Sa Dangote Ya Yi Barkwanci kan Hannun Jarin Matatar Shi

'Yan Najeriya Sun Sa Dangote Ya Yi Barkwanci kan Hannun Jarin Matatar Shi

  • Aliko Dangote ya yi barkwanci kan yadda sababbin masu hannun jarin matatar Dangote ke neman a gudanar da taron hukumar kamfanin
  • Attajirin ya kuma bayyana cewa kamfaninsa na shirin fitar da harkokin takin zamani zuwa kasuwar hannayen jari a shekarar 2028
  • A bayanin da ya yi, ya ce shirin zai bai wa karin ’yan Najeriya damar zama masu hannun jari a harkokin kasuwancin Dangote.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana shirin fitar da harkokin takin zamani na kamfanin zuwa kasuwar hannayen jari a shekarar 2028.

Dangote ya bayyana hakan ne yayin wata hira a taron Tattalin Arzikin Qatar ranar Lahadi, inda yake magana kan tsarin mallakar kamfanoninsa da kuma shirin kara yawan masu zuba jari.

Kara karanta wannan

Hakar ma’adanai: Atiku ya tausaya wa yaro, ya dauki dawainiyar karatunsa a makaranta

Alhaji Aliko Dangote
Attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Dalilin sayar da hannun jari

Da yake magana kan yiwuwar samun karin masu hannun jari a hira da Bloomberg, Dangote ya ce a baya kamfanoninsa sun dogara ne da kansu ba tare da abokan hulda ba.

Attajirin ya ce hakan ne ya sa suke kokarin bai wa dimbin mutane damar zama abokan hulda ta hanyar mallakar hannun jari a kamfanonin.

Aliko Dangote ya yi barkwanci

Dangote ya kuma yi tsokaci kan yadda wasu ’yan Najeriya da suka saye hannun jarin matatar Dangote ke yin barkwanci a kafafen sada zumunta.

Ya ce sababbin masu hannun jarin na ta kiraye-kirayen a gudanar da taron hukumar kamfanin, abin da ya bayyana cikin raha.

Cikin barkwanci mutane da dama ke nuna cewa yanzu suma sun zama masu ruwa da tsaki na kamfanin bayan sayen hannun jari.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun nuna rashin imani, sun kashe wani malami da bayin Allah da dama

Batun hannun jarin taki

Punch ta wallafa cewa Dangote ya tabbatar da cewa ana shirin sanya harkar takin zamani ta Dangote a kasuwar hannayen jari a shekarar 2028.

A baya, Dangote ya bayyana cewa fadada wannan bangaren kasuwancin zai taimaka wajen mayar da kamfanin takin zamani cikin manyan masu samar da urea a duniya.

Shirin IPO na shekarar 2028 shi ne sabon lokacin da Dangote ya bayyana a bainar jama'a kan lokacin da ake sa ran fitar da harkar takin zamani zuwa kasuwar hannayen jari.

Matatar Dangote da ke jihar Legas
Wani sashe na matatar Dangote. Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

Wannan sanarwar na zuwa ne yayin da tayin sayar da hannun jarin matatar Dangote ke ci gaba da jawo hankalin kananan masu zuba jari a Najeriya.

Tayin ya bude damar da jama'ar Najeriya za su samu wajen mallakar wani bangare na matatar ta hanyar hannun jari.

Obi ya taya Dangote tallla

A wani labarin, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya yi martani kan fitar da hannun jarin matatar Dangote zuwa kasuwar hannayen jari.

Kara karanta wannan

Dangote ya bayyana alherin da yake jiran wadanda suka saye hannun jari a matatarsa

A wata sanarwa da ya fitar, Obi ya yabawa Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, kan abin da ya bayyana a matsayin gagarumin ci gaba a Najeriya da Afirka.

Obi ya ce matakin Dangote ya kara tabbatar da matsayinsa na cewa ya kamata Najeriya ta sauya daga tattalin arzikin amfani da kaya zuwa samar da su, tare da karfafa sauran ’yan kasuwa su zuba jari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng