Shugabannin Kwamitin Yakin Zabe da aka yi kafin Abdulaziz Yari daga 1999 zuwa 2027

Shugabannin Kwamitin Yakin Zabe da aka yi kafin Abdulaziz Yari daga 1999 zuwa 2027

FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta nada Abdulaziz Yari ya zama shugaban yakin neman zaben Bola Tinubu/Kashim Shettima

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kafin Sanata Abdulaziz Yari, an samu wasu ‘yan siyasa da suka rike matsayin Darekta Janar na yakin zaben shugaban kasa a kasar nan.

A rahoton nan, mun tattaro shugabannin kamfe da suka kai jam’yyun PDP da APC ga nasara a takarar shugaban kasa tun daga 1999.

Amaechi
Shugabannin kwamitin yakin zabukan 2015 zuwa 2027 tare da Bola Tinubu Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tarihin darektoci janar na kame daga 1999

Shugabannin kamfe da suka ci zabe bayan dawo wa mulkin farar hula sun kunshi Iyorchia Ayu, Adamu Ciroma da irinsu Bode George.

Baya ga ‘yan PDP, an samu Rotimi Amaechi da Sanata Simon Lalong a jam’iyyar APC.

PDP ta rika cinye kimanin 60% na kuri’u a zabukan 1999 zuwa na 2015, sai dai adadin ya ragu lokacin takarar Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Ribadu, Dikko Radda da mutum 10 da Tinubu ya manta da su a kwamitin yakin zabe

Da Bola Tinubu ya nemi mulki a shekarar 2023 kuwa, 36.6% na kuri’un da aka kada ya samu.

Iyorchia Ayu, Fidelis Tapgun, Rotimi Amaechi, Simon Lalong duk sun zama ministoci bayan an kafa gwamntocin tarayya da aka lashe zabe.

Shugabannin kwamitin yakin zaben shugaban kasa

1. Iyorchia Ayu

Sanata Iyorchia Ayu shi ne ya jagoranci yakin neman zaben Olusegun Obasanjo lokacin da ya nemi mulkin Najeriya a 1999 a karkashin PDP.

A wata hira da Vanguard, ‘dan siyasar ya ce Atiku ya hada shi da Obasanjo. Sai dai bai iya rike wannan matsayi da aka zo zaben 2003 ba.

2. Fidelis Tapgun

Da Obasanjo yake so ya zarce, sai ya dauko tsohon gwamna Fidelis Tapgun ya zama Darekta Janar na kamfe, da ya ci zabe ya nada shi minista.

A lokacin Adamu Ciroma ya taka rawar gani wajen yakin neman babban zabe. Tsohon gwamnan na CBN ya yi Ministan kudi a zamanin na PDP.

3. Bode George

Bode George ne shugaban yakin neman zaben Ummaru Musa Yar’adua da Goodluck Jonathan a zaben 2007, kuma PDP ta samu nasara a takarar.

Kara karanta wannan

Ko Tinubu na da abubuwan da zai shawo kan 'yan Najeriya su zaɓi APC a 2027? An samu bayani

Tsohon gwamnan na mulkin soja ya taka rawar gani, sai dai har gobe ana sukar zaben na 2007 da cewa an shirya gagarumar magudi a Najeriya.

4. Ahmadu Ali

Ahmadu Ali wanda ya taba zama minista da sanata ya jagoranci tallata Goodluck Jonathan a 2011 har PDP ta doke CPC, ACN da ANPP.

Ali ya yi wannan aiki tare da Dalhatu Sarki Tafida, Jonathan ya samu 58.9% na kuri’u duk da nasarar da Muhammadu Buhari y samu a Arewa.

Amaechi
Marigayi Muhammadu Buhari tare da shugaban kwamitin zabensa, Rotimi Amaechi da Hadi Sirika Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

5. Rotimi Amaechi

Rotimi Amaechi ne Darekta Janar a zaben 2015 da ya kawo karshen mulkin PDP, shi ya jagoranci kamfen Muhammadu Buhari a jam’iyyar APC.

Ko da za a shiga zaben 2023, shi ya sake zama shugaban yakin zabe. A gwamnatin APC ya yi kusan shekaru takwas yana Babban Ministan sufuri.

6. Simon Lalong

Shi Bola Tinubu ya dauko Simon Lalong - kirista daga Filato ya zama shugaban yakin neman zabensa lokacin da ya duako danuwansa musulmi.

APC ta ci zaben 2023 amma kamar yadda Rotimi Amaechi bai iya ba jam'iyyarsa nasara a Ribas ba, shi ma tsohon gwamnan ya ji kunya a jihar Filato.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gamu da matsala har a majalisa daga nadin kwamitin yakin neman zabe

Babu wasu manya a kwamitin kamfen APC

Wannan labari ya yi duba ne kan jerin manyan 'yan siyasa na APC kamar Nuhu Ribadu, Dikko Radda, da Abba Kabir Yusuf da ba su cikin kamfe.

Rahoton ya zakulo jami'ai da 'yan siyasa daban-daban da aka bar su a waje duk da irin gudunmuwar da suka bayar ko kuma matsayinsu na siyasa a kasa.

Gwamnoni masu-ci, tsofaffi da shugabannin majalisa da na yanzu da jagorori a APC suna cikin wadanda babu su a kwamitin kamfen Tinubu/Shettima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng