Iyorchia Ayu: Muhimman abubuwa 3 game da sabon shugaban PDP da zai firgita APC kafin 2023

Iyorchia Ayu: Muhimman abubuwa 3 game da sabon shugaban PDP da zai firgita APC kafin 2023

Akwai dalilan da yasa bayyanar Iyorchia Ayu a matsayin sabon shugaban babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) bayan gagarumin zaben da ta yi zai basu wasu damammaki kafin zuwan zaben 2023.

Ya dace jam'iyya mai mulki ta APC ta fara tunanin yadda za ta sake tsari domin kawo sabbin dabarun da za su daidaita tare da dacewa wurin yakar Ayu.

Iyorchia Ayu: Muhimman abubuwa 3 game da sabon shugaban PDP da zai firgita APC kafin 2023
Iyorchia Ayu: Muhimman abubuwa 3 game da sabon shugaban PDP da zai firgita APC kafin 2023. Hoto daga vanguardngr.com
Asali: UGC

A wannan rubutun, Legit.ng ta bayyana wasu daga cikin irin abubuwan da kwarewar da Ayu ke da ita wanda zai iya tsorata APC.

1. Gudumawar da Ayu ya bai wa damokaradiyyar Najeriya

Sabon shugaban jam'iyyar adawan ya yi suna a matsayin daya daga cikin wadanda suka samar da damokaradiyyar Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Bayan lashe zabe, sabon shugaban matasan PDP ya magantu kan manufarsa akan APC

An san cewa Ayu ya sadaukar da abubuwa da yawa domin ganin cewa M.K.O Abiola ya zama shugaban kasar Najeriya a 1993.

Balle kuma 'yan Najeriya sun matukar tausayawa Abiola ganin cewa shi ne ya ci zabe mafi inganci da aka taba yi a Najeriya, sun rike dukkan makusantansa da kyau. Ayu na daya daga ciki.

Wannan kuwa babban abu ne da zai iya bada gudumawa wurin samun goyon bayan 'yan Najeriya a 2023.

2. 'Yan arewacin Najeriya na son shi

Ganin cewa ya na daga arewa ta tsakiya, a yanzu yankin shi ne ke fatan samar da shugaban kasa na gaba.

Bayyanar Ayu a matsayin shugaban babbar jam'iyyar adawa ya zo daidai da yadda yankin ya ke ta fatan samar da shugaban kasa na gaba.

Hakazalika, da yawa daga cikin tararrabin da ake yi a arewa ya na da alaka da rikicin shugabancin jam'iyya mai mulki wanda kuwa akwai yuwuwar Ayu ya tabuka abun arziki fiye da Mai Mala Buni.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun manta Allah: Buhari ya bayyana mafita ga matsalolin Najeriya

3. Ana zargin wadanda suka bar jam'iyyar za su koma

A halin yanzu, Ayu ya bayyana cewa ya fara samun kira daga wasu manyan 'yan PDP wadanda suka bar jam'iyyar domin suna son komawa.

A yayin magana a wata tattaunawa kan tsarin shi na hana wasu barin jam'iyyar, ya ce:

"Idan muka fara habaka damokaradiyyar cikin gida, wadanda ke barin jam'iyyar za su tsaya. Ba za su daina ba duka amma za a samu karanci kuma na yarda cewa wadanda suka tafi za su dawo.
"Da yawa daga cikinsu sun fara kira na kan cewa sun tafka babban kuskure saboda sun koma wani abu da ba jam'iyya ba. Ta yaya jam'iyya za ya dinga samun shugabancin gwamna?"

Asali: Legit.ng

Online view pixel