Jarumar Fim Ta Kunyata APC bayan Saka Sunanta a Kwamitin Yakin Neman Zabe

Jarumar Fim Ta Kunyata APC bayan Saka Sunanta a Kwamitin Yakin Neman Zabe

  • Toyin Abraham ta fito ta yi magana bayaj an saka sunanta a cikin kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar APC na jihar Legas
  • Jarumar ta ce ta yanke shawarar nisantar harkokin siyasa, tare da roƙon jama’a su yi watsi da rahotannin da suka saka sunanta cikin kwamitin
  • Jerin kwamitin ya ƙunshi fitattun ’yan wasan kwaikwayo da mawakan Najeriya, ciki har da Jide Kosoko da Eniola Badmus

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Fitacciyar jarumar fina-finan Najeriya, Toyin Abraham, ta musanta cewa tana cikin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen All Progressives Congress (APC) na Jihar Legas, musamman ɓangaren nishaɗi da bunƙasa harkokin fikira.

Jaruma Toyin Abraham ta roƙi jama’a da su yi watsi da rahotannin da ke cewa an saka sunanta cikin kwamitin.

Kara karanta wannan

Tirkashi: ADC ta bankado makarkashiyar da ake kullawa a Arewa gabanin zaben 2027

Toyin Abraham ta musanta shiga kwamitin APC
Jarumar fina-finai Toyin Abraham Hoto: Toyin Abraham
Source: Instagram

Ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a Instagram Story ranar Alhamis, 17 ga watan Satumban 2026.

“Ba ni cikin wani kwamitin yaƙin neman zaɓe”

Toyin Abraham ta ce ba ta cikin wani kwamitin yaƙin neman zaɓe, tana mai tunatar da jama’a cewa ta riga ta bayyana matsayinta kan shiga harkokin siyasa.

“Ba na cikin wani kwamitin yaƙin neman zaɓe. Na faɗi hakan kwanan nan. Ina nisantar siyasa. Don Allah ku yi watsi da saka sunana a cikin wani kwamitin yaƙin neman zaɓe,” in ji ta.

Fitattun Nollywood da aka saka a kwamitin

Sai dai jerin sunayen da aka fitar na fannin nishadantarwa da tattalin arzikin fikira ya ƙunshi wasu fitattun ’yan wasan kwaikwayo da mawaka.

Daga cikinsu akwai jarumi Jide Kosoko, da jarumai mata Eniola Badmus, Toyin Abraham da Bimbo Akintola, da kuma mawakan Fuji Wasiu Alabi Pasuma, Abass Akande Obesere da Adewale Ayuba.

Kara karanta wannan

Ana rigimar Wike da gwamnonin APC kan Tinubu, Shettima ya fasa kwai kan zaben 2023

An bayyana kwamitin ne ranar Alhamis ta hannun Kadri Obafemi Hamzat Media Centre, gabanin ƙaddamar da shi a hukumance da aka shirya yi ranar Juma’a, 18 ga Satumba, 2026.

Za a gudanar da bikin a sakatariyar APC da ke kan titin ACME, Ikeja, a Legas, jaridar Vanguard ta kawo rahoton.

Wadanda aka ba mukaman jagoranci?

An sanya Toke Benson-Awoyinka a matsayin Daraktar ɓangaren Nishaɗi da Bunƙasa Harkokin Fikira.

Jide Kosoko zai kasance Mataimakin Darakta, yayin da Eniola Badmus za ta kasance Mataimakiyar Darakta.

An kuma naɗa Akeem Alimi, wanda aka fi sani da Ajala Jalingo, a matsayin Sakatare, yayin da Dare Olateju zai kasance Mataimakin Sakatare.

Sauran fitattun ’yan wasan kwaikwayo

Jerin ya ƙunshi tsofaffin jaruman fina-finai da suka haɗa da Adebayo Salami, wanda aka fi sani da Oga Bello, da Saheed Balogun, Bukky Wright, Fathia Balogun, Yinka Quadri da Tayo Sobola.

Sauran sunayen da aka lissafa sun haɗa da Abiola Adebayo, Remi Oshodi, Foluke Daramola, Kikelomo Balogun, Bopo Oyekan Ismaila, Rasaq Yusuf, Aderinola Philips, Olamide Maja da Abbey Lanre.

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Na hannun daman Tinubu ya gargadi Wike kan yawan surutu

Mawaka da sauran masu nishaɗantarwa

Haka kuma, cikin jerin akwai mawaka da masu nishaɗi kamar Sulaimon Alao Adekunle, wanda aka fi sani da Malaika; Akorede Babatunde Okunola (Osupa) da Temitope Adekunle (Small Doctor).

Sauran sunayen sun haɗa da Sule Adiro Ataweye, Yemisi Falaye, Leke Babatunde Akinrowo, Kayode Fahm da Aruna Ishola.

Duk da kasancewar sunanta a cikin jerin da aka fitar, Toyin Abraham ta bayyana a fili cewa ba ta cikin wani kwamitin yaƙin neman zaɓe kuma tana son ci gaba da nisantar harkokin siyasa.

Toyin Abraham ta kunyata APC
Taswirar jihar Legas, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Daliin Dickson na kin shiga APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa jagoran jam'iyyar NDC mai adawa na kasa, Sanata Seriake Dickson, ya fito ya bayyana dalilinsa na kin shiga jam'iyyar APC mai mulki.

Sanata Seriake Dickson ya ce ya ƙi shiga APC ne saboda bai yarda Najeriya ta koma ƙasar da jam’iyya ɗaya ke mulki ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng