Yadda Obasanjo ya sa mutum 9 suka yi sanadiyyar zaman Umaru Yaradua Shugaban kasa

Yadda Obasanjo ya sa mutum 9 suka yi sanadiyyar zaman Umaru Yaradua Shugaban kasa

  • An zo lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari zai yi fama da ciwon kan wanene zai zama magajinsa
  • ‘Yan siyasa da-dama su na rububin samun tikitin takarar shugaba kasa a jam’iyyarsa ta APC mai mulki
  • A shekarar 2006, Olusegun Obansajo ya san yadda ya bi wajen ganin Gwamna Umaru ‘Yaradua ya gaje shi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Daily Trust ta dauko tsohon tarihi a game da yadda Olusegun Obasanjo a lokacin yana shugaban kasa ya dauko wanda zai karbi mulki daga hannunsa.

A wancan lokaci, Olusegun Obasanjo ya kafa wani kwamitin mutum tara da aka daurawa nauyin wannan aiki. Hudu daga cikinsu gwamnonin jihohi ne.

Shugaba Obasanjo ne ya zama shugaban kwamitin da kan sa, sai shugaban PDP, Ahmadu Ali, Marigayi Tony Anenih, Ojo Maduekwe da Bode George.

Kara karanta wannan

Shugaban kamfanin buga kudi ya ajiye aiki, ya shiga neman takara gadan-gadan a APC

Ragowar ‘yan kwamitin su ne gwamnonin jihohin Kwara, Gombe, Delta, Ondo; Bukola Saraki, Muhammad Danjuma Goje, James Ibori da Olusegun Agagu

Wani ‘dan kwamitin ya shaidawa jaridar cewa sun yi ta zama da Obasanjo a fadar Aso Villa a boye, a karshe aka amince Umaru ‘Yaradua ya yi takara.

“A shekarar 2006 aka kafa kwamitin, kuma ‘yan kwamitin kadai suka san da maganar domin da shugaban kasa mu ke aiki kai tsaye.”

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

- Tsohon gwamna da ya yi aiki a kwamitin

Umaru Yaradua da Shugaban kasa Obasanjo
Umaru Musa ‘Yaradua da Olusegun Obansajo Hoto: Getty
Asali: Getty Images

Gwamnoni sun hadu a Aso Villa

Bayan an cin ma matsaya a kan zabin Marigayi Umaru ‘Yaradua, sai Mai girma Obasanjo ya kira duka gwamnonin PDP zuwa wani taro a fadar shugaban kasa.

“A taron ya sanar da za a gudanar da wani zabe ga masu neman takarar shugaban kasa a jam’iyya, duk wanda ya ci, shi ne zai samu tikitin PDP.”

Kara karanta wannan

Tambuwal da Gwamnoni 9 masu neman mulki su na kashe miliyoyi duk rana a hayar jirgi

“’Yan kwamitin nan su ka yi aiki a matsayin malaman zabe. Bayan an kada kuri’a, sai shugaban kasa ya ce a wani wuri za a kirga kuri’un.”
“Kafin mu isa inda za a kirga kuri’un, sai aka kira mu a waya, aka ce ka da a kirga tukuna.”

- Tsohon gwamna da ya yi aiki a kwamitin

Magana ta canza

Kwanaki kadan bayan an yi haka, sai shugaban kasan ya kira su fadar Aso Villa, ya shaida masu cewa ‘dan takararsa shi ne gwamnan jihar Katsina mai-ci.

Daga nan sai ya ce zai tafi gidan Aliko Dangote, inda ya aika jirgi domin ya dauko masa Yar’adua daga Katsina. Bayan wani lokaci kadan, sai ga gwamnan.

Kamar yadda ‘dan kwamitin ya sanar da Daily Trust, Yar’adua yana zuwa sai suka fara kiransa Mai girma shugaban kasa, nan take ya hadu da Obasanjo a ofis.

Aikin tallata 'dan takara

Kara karanta wannan

Jerin Gwamnonin jihohi 17 da za su sauka daga kan kujerar mulki nan da watanni 12

Bayan Cif Obasanjo ya sanar da Marigayi Yar’adua manufarsa, sai ya bukaci Saraki da Ibori su yi kokarin tallata takarar Gwamnan ga sauran abokan aikinsu.

Gwamnonin su na wannan aiki, shi kuma Obasanjo a gefe guda yana kokarin ganin Yar’adua ya lashe zaben tsaida gwani, a karshe dai hakan dai aka yi kuwa.

Umaru Musa ‘Yaradua ya yi nasarar zama ‘dan takara, ya kuma yi galaba a zaben shugaban kasa a 2007. A karshe shugaban kasar ya mutu a ofis a Mayun 2010.

Asali: Legit.ng

Online view pixel