INEC Ta Sanar da Dan Takarar da Ya Lashe Zaben Cike Gurbi a Kano

INEC Ta Sanar da Dan Takarar da Ya Lashe Zaben Cike Gurbi a Kano

  • Jam’iyyar APC ta lashe zaɓen cike gurbin Dawakin Kudu/Warawa a Kano, inda ɗan takararta Hussaini Yusuf Datti ya samu ƙuri’u 22,890
  • PDP mai adawa ta samu ƙuri’u 180, PRP ta samu 270, yayin da APP da Labour Party suka samu 53 da 39 bi da bi
  • An gudanar da zaɓen ne domin cike gurbin kujerar da Shuaibu Rabiu Nagoggo, wanda aka fi sani da Abba Gano, ya bari bayan ya koma Majalisar Wakilai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta lashe zaɓen cike gurbin kujerar Dawakin Kudu/Warawa a Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Ɗan takarar jam’iyyar, Hussaini Yusuf Datti, ya samu jimillar ƙuri’u 22,890, inda ya yi nasara a kan sauran ’yan takarar da suka fafata a zaɓen.

APC ta samu nasara a Kano
Taswirar jihar Kano, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

APC ta samu nasara a zaben

Kara karanta wannan

Rigima ta kunno kai a NDC kan kwamitin yakin neman zaben Kwankwaso da Obi

Legit Hausa ta fahimci cewa jami'in tattara sakamakon zaben, Farfesa Ibrahim Tajo Suraj ne ya sanar da sakamakon a ranar Asabar, 19 ga watan Satumban 2026.

Sakamakon zaɓen ya nuna cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta samu ƙuri’u 180, yayin da Peoples Redemption Party (PRP) ta samu 270, jaridar Vanguard ta kawo rahoton.

Jam'iyyar Action Peoples Party (APP) ta samu ƙuri’u 53, yayin da Labour Party (LP) ta samu 39.

Zaɓen ya kasance na musamman ne domin cike kujerar mazabar Dawakin Kudu/Warawa da ta samu gibi a Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Dalilin da ya sa aka gudanar da zaɓen

Kujerar ta samu gibi ne bayan Shuaibu Rabiu Nagoggo, wanda aka fi sani da Abba Gano, ya bar Majalisar Dokokin Jihar Kano bayan ya lashe zaɓen da ya kai shi Majalisar Wakilai ta Tarayya.

Nagoggo ya samu kujerar Majalisar Wakilai ne a zaɓen cike gurbin da aka gudanar bayan rasuwar Alhaji Muhammad Hassan, wanda ke wakiltar mazabar tarayya ta Dawakin Kudu/Warawa.

Rasuwar Muhammad Hassan ta jawo zaɓen cike gurbi

Muhammad Hassan ya rasu a Abuja ranar 10 ga Afrilu, 2026, yana da shekaru 66, bayan wani lokaci yana fama da rashin lafiya.

Kara karanta wannan

APC ta yi zarge zarge masu nauyi kan Atiku, ta bukaci ya janye daga takara

Rasuwarsa ta jawo gudanar da zaɓen cike gurbin kujerar mazabar Dawakin Kudu/Warawa a Majalisar Wakilai.

A wannan zaɓen ne Nagoggo ya samu nasara, abin da ya sa ya koma Majalisar Wakilai ta Tarayya, tare da barin kujerarsa ta Majalisar Dokokin Jihar Kano a buɗe.

Daga nan ne aka gudanar da sabon zaɓen cike gurbin kujerar, inda ɗan takarar APC, Hussaini Yusuf Datti, ya samu nasara da ƙuri’u 22,890.

Yusuf Datti ya lashe zabe a Kano
Yusuf Hussain Datti da ya lashe zabe a Kano Hoto: Hon Yusuf Hussain Datti
Source: Facebook

PDP ta sauya dan takarar gwamna a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar mai adawa a Jihar Kano ta tabbatar da Muhammad Sani Abacha a matsayin ɗan takararta na gwamnan jihar a zaɓen 2027.

Sanarwar sauyin ta biyo bayan janyewar Muhammad Bello Dalha, wanda a baya ya samu tikitin jam’iyyar PDP bayan ya lashe zaɓen fitar da gwani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng