Za a Tura Tawaga ga Dattawan Igbo domin Rokon Obi Ya Janye wa Tinubu a 2027

Za a Tura Tawaga ga Dattawan Igbo domin Rokon Obi Ya Janye wa Tinubu a 2027

  • Kungiyar Renewed Hope for Greater Nigeria ta ce ta shirya wata ganawa a Kudu maso Gabas domin nema wa Bola Tinubu sauki a 2027
  • Shugaban kungiyar a yankin ya ce za su nemi Emeka Anyaoku da Ebitu Ukiwe su jagoranci tawaga zuwa wajen Obi
  • Yaya ce janyewar Obi ba zai kawo ƙarshen burinsa na shugabancin Najeriya ba, sai dai dagewa zuwa lokacin da ya dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Owerri, Imo - Reshen Kudu maso Gabas na kungiyar Renewed Hope for Greater Nigeria (RHGN) ya yanke shawarar samar wa Bola Tinubu sauki a yankin.

Kungiyar ta ce za ta tuntuɓi fitattun dattawan Igbo domin su lallashin Peter Obi, ya janye daga takarar shugaban ƙasa ta 2027 tare da goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

'Akwai gagarumar matsala': Malamin addini ya bukaci Tinubu ya hakura da takara

Za a nema wa Tinubu alfarma wurin Obi
Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi da Shugaba Bola Tinubu. Hoto; Mr Peter Obi, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Shugaban kungiyar a Kudu maso Gabas, Mazi Franklin Ngoforo, ne ya bayyana hakan a Owerri ranar Asabar, cewar Vanguard.

Za a roki Obi ya goyi bayan Tinubu

Ya ce kungiyar za ta tuntuɓi shugabancin Ohanaeze Ndigbo ƙarƙashin Sanata John Azuta Mbata, tare da dattawan ƙasa, ciki har da Cif Emeka Anyaoku da Commodore Ebitu Ukiwe, domin su jagoranci tawaga zuwa wajen Obi.

A cewar Ngoforo, matakin ba shi da nufin rage darajar Obi ko kalubalantar matsayinsa na siyasa, sai dai lallashe shi ya fifita muradun dogon lokaci na al’ummar Igbo fiye da neman tikitin shugaban ƙasa a wannan lokaci.

Ngoforo ya ce manufar ita ce Obi ya sake duba zaɓen 2027, ya fahimci cewa wata yarjejeniyar siyasa mai faɗi za ta iya bai wa Kudu maso Gabas damar samun shugabancin ƙasa cikin mafi kusancin lokaci.

Ya ce muhimmin abin da ya kamata a duba shi ne irin ribar da Kudu maso Gabas za ta samu ta hanyar gina kyakkyawar alaƙar siyasa da Kudu maso Yamma.

Kara karanta wannan

Shugabannin kwamitin yakin zabe da aka yi kafin Abdulaziz Yari daga 1999 zuwa 2027

Ngoforo ya lura cewa idan aka sake zaɓar Tinubu, kundin tsarin mulki ya iyakance shi da wa’adi guda ɗaya kacal, cewar Punch.

Masoyan Tinubu na son Obi ya janye takara
Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi. Hoto: Mr Peter Obi.
Source: Facebook

Abin da ake bukata daga Kudu maso Gabas

Don haka, ya ce Kudu maso Gabas za ta iya tallafa wa Kudu maso Yamma yanzu, yayin da take gina yarjejeniyar siyasa da za ta taimaka mata samun shugabancin ƙasa idan mulki ya koma Kudu a gaba.

Maimakon kallon zaɓen 2027 a matsayin fafatawar da za a ci ko a sha kaye kawai, ya ce al’ummar Igbo ya kamata su ɗauke shi a matsayin damar tara kyakkyawar alakar siyasa da kuma samar da alƙawuran taimakon juna da sauran yankuna.

Ngoforo ya roƙi Peter Obi ya yi la’akari da cewa janyewa daga takarar 2027 ba lallai ya zama ƙarshen burinsa na zama shugaban ƙasa ba, sai dai jinkirta wannan buri zuwa lokacin da ya dace.

DSS za ta ba Obi da yan takara tsaro

An ji cewa Hukumar DSS ta ƙara tsaurara matakan tsaro ga Atiku Abubakar, Peter Obi, Ritimi Amaechi da Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Ko Tinubu na da abubuwan da zai shawo kan 'yan Najeriya su zaɓi APC a 2027? An samu bayani

Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin kare dukkan ’yan takarar shugaban ƙasa 18 da mataimakansu.

INEC ta wallafa sunayen ’yan takarar gwamna da majalisun jihohi na 2027, yayin da wasu fitattun ’yan siyasa suka ɓace daga jerin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.