Yan Bindiga Sun Turo Sako kan Malaman Musulunci 6 da Suka Sace, Sanata Ya Tsoma Baki
- Yan bindiga sun bukaci Naira miliyan 30 a matsayin kudin fansa domin sakin malaman addinin Musulunci shida da suka sace a Zamfara
- Bayanai sun nuna cewa masu garkuwan sun saki direban malaman bayan iyalansa sun biya Naira miliyan 2
- Ana zargin malaman na cikin mawuyacin hali saboda tsufansu da tsawon lokacin da suka shafe a hannun masu garkuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - Yan bindigar da suka yi garkuwa da malaman addinin Musulunci shida a jihar Zamfara sun bukaci a biya su N30m a matsayin kudin fansa domin sakin su.
An ruwaito cewa yan bindigar sun fara tattaunwa da iyalan malaman, inda suka shaida masu a hada wadannan kudi domin fansarsu.

Source: Original
Wani mazaunin kauyen Dakko da ke karamar hukumar Bakura ta jihar, Malam Muhammad Ibrahim, ya tabbatar wa Daily Trust da lamarin ta wayar tarho.

Kara karanta wannan
Tinubu ya sanar da karyewar farashin sufuri a Najeriya, ya kafa hujja da Kaduna da wasu jihohi
An sako direban malaman Zamfara
Sai dai Ibrahim ya ce an saki direban malaman, wanda aka sace tare da limaman, bayan iyalansa sun biya Naira miliyan 2 a matsayin kudin fansa.
Ya ce:
“A gaskiya mutun takwas ‘yan bindigar suka sace tun farko, limamai biyar, direbansu da wasu mutane biyu da aka ce suna hanyarsu ta komawa gida daga gona.
“Mun ji cewa ‘yan bindigar sun bukaci N300,000 kowanne da kuma jarkokin man fetur guda biyu masu lita 25 domin sakin mutanen biyu da aka sace a hanyarsu daga gona. Game da direban kuwa, ‘yan bindigar sun karbi N2m daga iyalansa.
“An saki direban a yau (Asabar), kuma tun daga lokacin ya koma tare da iyalinsa a kauyen Kwatsama. Mun kuma ji cewa ana shirye-shiryen biyan kudin fansa na N30m domin sakin limaman da aka sace.
Sanata zai biya kudin fansa
Ibrahim ya kara da cewa wani sanatan Zamfara ya yi alkwarin biyan kudin fansar da yan bindigan suka nema domin sako malaman musulunci.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun mamaye gidan kwamishina, sun bude wuta ba tare da nuna tausayi ba
“Bisa ingantaccen bayani, wani Sanata mai ci daga jihar Zamfara ya yi alkawarin biyan kudin fansar domin sakin limaman. Muna fatan ba zai dauki lokaci mai tsawo ba," in ji shi.
Ibrahim ya yi kira ga hukumomi da su kara kaimi wajen kokarin kubutar da limaman, yana mai nuna damuwa kan cewa watakila masu garkuwa sun gallaza musu, musamman ganin shekarunsu.

Source: Twitter
“Limaman tsofaffi ne, kuma zaman da suke yi a maboyar ‘yan bindigar kadai na iya jefa lafiyarsu cikin mawuyacin hali. Don haka gwamnati ta gaggauta kokarin kubutar da su,” in ji shi.
Wani dan daya daga cikin limaman da aka sace, wanda ya bukaci a boye sunansa, ya ce iyalan malaman sun yi farin ciki da sabon ci gaban da aka samu.
Ya tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun bukaci N30m domin sakin malaman.
Yan bindiga sun tada garuruwa a Zamfara
Kun ji cewa yan bindiga sun kashe aƙalla mutane 13 a kauyuka uku da ke Masarautar Dansadau a ƙaramar hukumar Maru ta Jihar Zamfara.
Ana zargin cewa wannan harin na ramuwar gayya ne bayan ’yan sa-kai sun kashe wani jagoran ’yan bindiga da wasu daga cikin mutanensa.
Asali: Legit.ng