"Ku Nemi Mafaka," NiHSA Ta Jero Jihohi 15 da Za a Yi Mummunar Ambaliyar Ruwa a Najeriya

"Ku Nemi Mafaka," NiHSA Ta Jero Jihohi 15 da Za a Yi Mummunar Ambaliyar Ruwa a Najeriya

  • Hukumar NiHSA ta yi gargadin cewa ambaliyar ruwa mai tsanani za ta auku a jihohin Imo, Cross River, Lagos da wasu 12 daga 19 zuwa 25 ga Satumba
  • Hukumar ta ce makarantu, asibitoci, kasuwanni, gonaki da wuraren ibada na cikin wuraren da ke fuskantar barazanar ambaliyar
  • NiHSA ta bukaci gwamnatocin jihohin da abin ya shafa su gaggauta kwashe jama’a zuwa wurare masu tsaro da aminci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Hukumar Kula da Ruwa da Ambaliyar Najeriya (NiHSA) ta yi hasashen jihohin Imo, Cross River, Lagos da wasu 12 za su fuskanci ambaliyar ruwa mai tsanani cikin kwanaki bakwai.

Shugaban Hukumar NiHSA, Arch Umar Mohammed, ne ya bayyana hakan ranar Juma’a a cikin wani gargadi kan ambaliyar ruwa, inda ya ce ana sa ran ambaliyar za ta faru tsakanin 19 zuwa 25 ga Satumba, 2026.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Shugaba Tinubu ya ɗauki zafi kan kutuwar matasa 37 a wajen hukumar NSCDC

Ambaliya.
Yadda ruwa ke mamaye gidaje da garuruwa sakamakon ibtila'in ambaliya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A rahoton Vanguard, Mohammed ya ce makarantu, cibiyoyin kiwon lafiya, kasuwanni, gonaki da wuraren ibada, da sauran muhimman wurare, na cikin wadanda ambaliyar za ta iya shafa.

NiHSA ta bukaci jihohi su dauki mataki

Ya kuma yi kira ga gwamnatocin jihohin da abin ya shafa da su gaggauta mayar da mutanensu zuwa wurare masu tsaro da aminci kafin fara ambaliyar.

Ya ce:

“Ana hasashen babbar barazanar ambaliyar koguna cikin kwanaki bakwai masu zuwa a Imo, Cross River da wasu jihohi 13. Ana sa ran tashin ruwan koguna zai haddasa ambaliya.
“Mutanen yankin da ambaliya ke mamayewa su shirya yin kaura zuwa wurare masu tudu da aminci.”

Wasu yankunan da ruwa zai yi ambaliya

A jihar Imo, kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Aboh-Mba, Ahizu-Mb, Ehime-Mb, Ezinihit, Ideato No, Ihitte/U da Ikeduru.

Hukumar ta ce garuruwa 958, makarantu 1,022, cibiyoyin kiwon lafiya 553, kasuwanni 161 da wuraren ibada 198 na fuskantar barazanar ambaliya.

Kara karanta wannan

"Ka da ku": Shawarar Sanusi II ga masu son sayen hannun jarin matatar Dangote

A Cross River, kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Abi, Akamkpa, Akpabuyo, Biase, Calabar, Calabar South, Ikom da Obubra.

NiHSA ta ce garuruwa 2,471, makarantu 703, cibiyoyin kiwon lafiya 344, kasuwanni 145, wuraren ibada 453 da hekta 854 na gonaki na fuskantar barazanar ambaliya.

Ambaliya.
Yadda ruwa aya tashi da gidaje da ababen hawan mutane a wasu sassan da aka yi ambaliya a Najeriya Hoto: Getty
Source: Facebook

A jihar Benue, Buruku, Gboko, Guma, Katsina-Ala, Logo da Ukum na daga cikin kananan hukumomin da ake hasashen za su fuskanci ambaliyar ruwa

Barazanar ta shafi kauyuka 303, makarantu 100, cibiyoyin kiwon lafiya 48, kasuwanni 32, wuraren ibada 151 da hekta 55 na gonaki.

Bayan haka, hukumar ta bayyana Edo, Bayelsa, Enugu, Kogi, Delta, Abia, Taraba da Rivers, da wasu jihohi, a matsayin jihohin da ake sa ran za su fuskanci mummunan tasirin ambaliyar da aka yi hasashe.

An ja kunnen mutane kan ambaliya

Kun ji cewa Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya ta fitar da gargadi cewa jihohi tara da yankuna 14 a Arewa na iya fuskantar ambaliyar ruwa.

Takardar da ma'aikatar ta fitar ta bukaci jama’a musamman mazauna da ke kusa da Kogin Niger daga Jebba zuwa Lokoja da su gaggauta barin yankunan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262