Zargin $16bn: Ku Bincike Ni idan da Hujjar Na Yi Sata In ji Atiku ga Tinubu

Zargin $16bn: Ku Bincike Ni idan da Hujjar Na Yi Sata In ji Atiku ga Tinubu

  • Atiku Abububakar ya buƙaci gwamnati ta fito da kwararan hujjoji a kansa maimakon sake dawo da tsofaffin zarge-zarge
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa bai taɓa jagorantar aiwatar da aikin wutar lantarki na $16bn a baya
  • Maimakon haka, ya buƙaci Bola Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya bayanin inda kuɗin da aka tara daga cire tallafin fetur suka shige

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

FCT, Abuja - Atiku Abubakar ya gaji da surutai, wannan karo ya kalubalanci gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bincike shi.

Alhaji Atiku Abubakar ya kalubalanci gwamnati mai-ci da magoya bayanta su kawo hujjar cewa ya aikata ba daidai ba a ofis.

Atiku Abubakar
Jagoran adawa, Atiku Abubakar da Shugaban kasa Bola Tinubu Hoto: @atiku/@officialABAT
Source: UGC

0Atiku Abubakar ya kalubalanci Bola Tinubu

An dade ana zargin tsohon mataimakin shugaban Najeriya da badakaloli, Vanguard ta ce wannan karo sai ya jefa kalubale.

Maimakon a yi ta yawo da maganganu, Atiku yana so a bincike shi game da zargin wawaso da dukiyar gwamnatin kasa.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Atiku ya bayyana 'barayin' da yake fafatawa da su a zaben 2027

‘Dan takaran shugaban kasar na ADC ya yi magana ne kan jifansa da zargin satar kudin wuta ko saida kadarorin gwamnati.

Atiku yake cewa wadannan zargi ba komai ba ne illa kauda hankalin jama’a daga tambayar ina kudin Najeriya suka shige a yau.

‘Dan adawar ya ce bayan an cire tallafin man fetur a 2023, gwamnatin Najeriya tana samun kudin da ya kamata talaka ya mora.

A wani jawabi da Phrank Shaibu ya fitar a yammacin Laraba, ‘dan siyasar ya zargi gwamnati da neman kawar da tunanin jama’a.

Ya ce ana canza akalar tattaunawa daga kuncin rayuwa da miliyoyin mutane suke fama da shi a mulkin Bola Ahmed Tinubu.

Tsohon zargin da ake ta yi wa Atiku

Atiku ya ce maimakon wannan an tafi ana maganar zargin da ake ta yi wanda har yau bai kai ga gurfanar da wanda ake tuhuma ba.

The Cable ta rahoto shi ya ce Majalisar tarayya ta binciki kwangilolin wuta a baya, amma ba a taba gayyatar da shi saboda wani zargi ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gamu da matsala har a majalisa daga nadin kwamitin yakin neman zabe

"Eh, na jagoranci kwamitin saida kadarorin gwamnati a matsayin Mataimakin shugaban kasa.
"Amma a kwangilolin wuta, ban yarda da tsarin ba, kuma ban jagoranci dabbaka shi ba. Ministan da yake da alhaki ya yi wannan..."

- Atiku Abubakar

Jawabin ya ce haka kuma Atiku bai da hannu a sha’anin gwanjon karfen Aluminium Smelter.

VP Atiku Abubakar
Shugaban Najeriya da 'dan takaran ADC a 2027, Atiku Abubakar Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Meyasa har yau ba a kama Atiku ba?

‘Dan takaran ya ce tun 2007 ya bar ofis kuma ya dade yana adawa da gwamnati, da akwai wata hujja a kan shi da an yi ram da shi.

Atiku ya ce:

"Idan akwai hujjar cewa na saci kudin al’umma, meyasa har yau babu gwamnatin da ta kai shi kotu?
"Ba a makara ba har yau. Ku bincike ni. Ku gayyace ni. Ku kawo hujjar. Ku gurfanar da ni idan za ku iya. Amma furofaganda ba hujja ba ce."

Yadda Atiku zai maido tallafin man fetur in

Bisa dukkan alamu a 2027, ba da wasa yake yi ba, domin an ji labari Atiku Abubakar ya fito da dabarar da zai bi ya maido tallafin fetur.

Kara karanta wannan

Atiku ya fito ya yi bidiyo kan dawo da tallafin mai da aka fara yada jita jita

Atiku Abubakar ya gabatar da sabon tsarin tallafi domin rage radadin da aka shiga tun Mayun 2023 lokcin da Bola Tinubu ya shiga ofis.

Manufarsa ita ce saukar da farashin litar fetur don rage hauhawar farashin kayayyaki da saukaka wa talakawan Najeriya idan aka zabe shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng