Atiku Ya Fito Ya Yi Bidiyo kan Dawo da Tallafin Mai da aka Fara Yada Jita Jita
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce matsayarsa ba ta sauya ba kan shirin mayar da tallafin man fetur idan ya lashe zaben 2027
- Atiku ya nesanta kansa da wasu kalaman mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, yana mai cewa bai yi magana da umarninsa ba
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce zai samar da tsarin tallafi da zai taimaka wajen rage tsadar makamashi da dawo da walwalar 'yan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya jaddada cewa zai mayar da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi shugaban Najeriya a 2027.
Atiku ya ce matsayarsa kan lamarin ba ta sauya ba, duk da wasu kalamai da ɗaya daga cikin masu taimaka masa kan harkokin yada labarai.

Kara karanta wannan
Batun dawo da tallafin mai ya tada hankalin shugaban APC na ƙasa, ya tura tambaya 1 ga Atiku

Source: Facebook
A bidiyon da ya wallafa a Facebook, Atiku ya bayyana cewa Ibe bai yi kalaman a madadinsa ko da umarninsa ba, yana mai jaddada cewa shi ne ke da ikon bayyana manufofin da zai aiwatar idan ya zama shugaban ƙasa.
Atiku ya karyata Ibe
Atiku ya jaddada cewa zai maido tallafin man fetur ne a ranar Talata lokacin da ya karɓi shugabannin jam'iyyar ADC na jihar Osun a Abuja.
Ya ce ɗaya daga cikin masu taimaka masa kan harkokin yada labarai ya bayyana wani matsayi da ya saba da nasa dangane da batun tallafin man fetur.
Atiku ya ce:
"Da farko, ɗaya daga cikin masu taimaka min kan harkokin yada labarai ya saba wa matsayina a wata sanarwa kan manufar tallafin man fetur.
"Ina son sake bayyana a fili cewa lokacin da na ce zan dawo da tallafin man fetur, to tabbas zan yi hakan. Najeriya tana da arzikin da zai iya kula da jin dadin 'yan kasarta."
Paul Ibe ya taba bayyana a wata hira cewa Atiku zai mayar da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa, amma zai cire tallafin a hankali bayan tattalin arzikin kasar ya farfaɗo.
Sai dai Atiku ya musanta cewa wannan ne cikakken matsayinsa, inda ya wallafa a shafinsa na X cewa ba zai sauya ra'ayinsa kan mayar da tallafin ba.
Atiku zai mayar da tallafi
Atiku ya ce manufarsa ba wai komawa tsarin da gwamnati ke kashe makudan kudi wajen tallafa wa man fetur da ake shigo da shi daga kasashen waje ba ce.
A cewarsa, zai samar da tallafi na musamman wanda zai mayar da hankali kan habaka tace man fetur da samar da shi a cikin Najeriya.

Source: Getty Images
Ya ce hauhawar farashin man fetur na haifar da tsadar sufuri, wanda daga bisani ke kara farashin abinci da sauran kayan masarufi, lamarin da ke jefa iyalai cikin wahala.
Atiku ya ce:
"Zan karya wannan mummunar sarkar da ta mamaye rayuwar kasar nan a kusan shekaru hudu na mulkin Tinubu."
Ga bayanin da Atiku ya yi a kasa:
Gargadi kan mayar da tallafi

Kara karanta wannan
Zance ya ƙare, Peter Obi ya bayyana matsayarsa kan batun dawo da tallafin man fetur a Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama'a, Mohammed Idris, ya yi gargadi kan kiraye-kirayen da ake yi na mayar da tallafin man fetur.
Mohammed Idris ya ce komawa tsohon tsarin tallafin na iya rage kwarin gwiwar masu zuba jari da kuma rusa wasu nasarorin da gwamnatin Bola Tinubu ta ce ta samu.
Ya ce masu neman dawo da tallafin man fetur su yi la'akari da kudin da za a iya karkatarwa daga bangarorin ilimi, lafiya, tsaro, manyan ayyukan raya kasa.
Asali: Legit.ng
