Gwamnatin Tinubu Ta Yi Karin Haske kan Batun Sayar da Makarantun Sakandare

Gwamnatin Tinubu Ta Yi Karin Haske kan Batun Sayar da Makarantun Sakandare

  • Gwamnati ta damka makarantar Kings College a Legas ga ƙungiyar tsofaffin daliban da suke ta ƙoƙarin gyaran ta
  • Ministan Ilimi ya ce Gwamnatin tarayya ba ta da niyyar mika ikon makarantun ga 'yan kasuwa ko kuma ta saida su
  • Tunji Alausa ya bayyana cewa za a buƙaci fiye da ₦2tr domin gyara dukkan makarantun Unity 115 da ke faɗin ƙasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce ba ta da shirin saida kwalejojin sakandare ko ta sallama masu ga ‘yan kasuwa su tafiyar da su.

Ministan ilmi ya fadi haka ganin ana neman tada rigima sakamakon damka makarantar Kings College a hannun tsofaffin dalibai.

Makaranta
Wasu 'daliban makaranta a Ijebu Ode a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Makarantar Kings College ta koma hannun KCOBA

Mista Tunji Alausa ya yi magana saboda rudanin da aka shiga game da fitacciyar makarantar King College a Legas a cewar The Cable.

Kara karanta wannan

Olu Jacobs: Abubuwan sani game da fitaccen jarumin fim da Allah ya yi wa rasuwa

Gwamnati ta damka Kings College zuwa ga kungiyar KCOBA ta tsofaffin daliban makarantar sakandaren, hakan ya jawo zanga-zanga.

Iyaye da malaman makarantar ba su ji dadin wannan lamari, suna adawa da mika Kings College a hannun kungiyar tsofaffin dalibanta.

Ma'aikata sun tafi yajin-aiki a makarantu

Ranar Litinin da aka koma karatu ana jira a fara karanta da yara, sai aka ji kungiyar ASCSN ta shiga yajin aiki a duka makarantun kasar.

Wannan yajin-aiki ya shafi duka makarantun sakandaren da ke hannun gwamnatin tarayya da ke bukatar N2tr kafin a iya gyara su.

Tunji Alausa ya kira taron gaggawa da ma’aikata daga ciki har da shugabannin TUC.

Bayan zaman da aka yi da Mai girma Ministan ilmin, kungiyar TUC ta roki ASCSN ta janye yajin-aiki kuma a bari koma karatu washegari.

Zanga-zanga a Kings College ta jawo 'yan sanda

Amma duk da haka, iyaye da ma’aikatan Kings College sun tare hanya a Legas, suka hana ‘yan KCOBA su shiga masu cikin makaranta.

Kara karanta wannan

Syria: Mutane sun barke da zanga zanga kan tsadar man fetur da gas

A sanadiyyar haka sai da ‘yan sanda suka shigo ciki har Vanguard ta rahoto cewa jami’an tsaro sun jawo an rufe makarantar sakandaren.

Alausa ya ce ba za a yi irin abin da aka yi a Legas a sauran makarantun sakandare na kasar ba, tsarin zai shafi Kings College ne kawai.

Ya ce:

"Gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar ilmi ba ta da wata niyyar saida wata makarantar Unity."

Ministan ya ce an kira kowane bangare a tattauna tare da bayanin hikimar ba KCOBA dawainiyar kula da babbar makarantar da ke Legas.

Ya ce an yi haka ne saboda su kula da makarantar domin ta tabarbare kuma kungiyar ta kashe N2bn wajen gyaran ta a ‘yan shekarun nan.

Domin gyara sauran makarantun Unity da ake da su, Alausa ya ce sun samu $20m daga bankin duniya da nufin fara aiki a kan guda 20.

Makaranta
Daliban makarantar sakandare a Najeriya da Bola Tinubu a Eagle Square a Abuja Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Lokacin da gwamnati ta rufe wasu makarantu

Ana da labarin gwamnatoci sun dauki matakin rufe makarantu a 2015 saboda karuwar matsalar tsaro da sace dalibai a jihohin da dama.

Kara karanta wannan

Houthi sun kwace yankin Bab al Mandab yayin da Saudi ke naman agajin Trump

Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin rufe makarantun sakandare na Unity guda 41 a fadin kasar don kare rayukan dalibai da ke karatu.

Jihohi irin su Katsina, Kwara, Filato, da Taraba su ma sun rufe makarantunsu ko kuma maida makarantun kwana zuwa na jeka-ka-dawo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng