
Rashawa a gwamnatin Najeriya







Hukumar Shari’a ta Kano ta kori ma’aikata biyu kan karbar cin hanci da rashawa, yayin da ta janye dakatarwar da ta yi wa wasu ma'aikata uku saboda rashin hujja.

SERAP ta maka Tinubu a kotu kan kwangilolin bogi da suka lakume Naira biliyan 167, inda ta bukaci a gurfanar da 'yan kwangilar don dawo da dukiyar gwamnati.

'Yar gwagwarmaya, kuma 'yar siyasa a Arewacin Najeriya, Hajiya Naja'atu Muhammad ta tabbatar da cewa akwai shaidar Nuhu Ribadu ya zargi Tinubu da rashawa.

EFCC ta gurfanar da Farfesa Usman Yusuf bisa laifuffuka biyar da suka hada da wawure kudi da bayar da fifiko ba bisa ka’ida ba. Kotu ta tsare shi a kurkuku.

SERAP ta bukaci Shugaba Tinubu ya binciki batan Naira biliyan 26 daga PTDF da Ma'aikatar Man Fetur a 2021, tare da mayar da kudaden don rage gibin kasafin kudi.

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ya zuba ido a rika zaluntar mutanen da su ka zabe shi ba, inda ya lashi takobin yaki da rashawa.

Babbar kotu da ke zamanta a Abuja ta ci gaba da sauraron shari'ar almundahana da hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta shigar gabanta.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta na sane da nauyin jama'a da ya rataya a wuyanta, kuma za ta yi abin da ya dace.

Hukumar ICPC za ta gurfanar da tsoffin mukarraban El-Rufai kan zargin karkatar da Naira miliyan 64, yayin da tsohon gwamnan ya musanta zargin cin hanci.
Rashawa a gwamnatin Najeriya
Samu kari