Jam’iyyar PDP Ta Ja Kunnen Gwamnonin APC, Ta Fadi Dalilin Yakar Nyesom Wike

Jam’iyyar PDP Ta Ja Kunnen Gwamnonin APC, Ta Fadi Dalilin Yakar Nyesom Wike

  • Bangaren PDP da ke mara wa Nyesom Wike baya ya gargaɗi gwamnonin APC cewa raina tasirin ministan zai haifar masu da matsala
  • PDP ta bayyana cewa tsoron gazawarta a mulki ne ya sa gwamnonin APC suka damu da Ministan na Abuja da barazanar ‘yan takaransa
  • Kakakin tsagin jam'iyyar ya ce goyon bayan Tinubu ba yana nufin Wike ya mika ragamar PDP ga APC ba a sauran zabukan 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

FCT, Abuja - Bangaren jam’iyyar PDP da ke tare da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya maida raddi ga gwamnonin APC a Najeriya.

Tsagin jam’iyyar adawar ya ce gwamnonin da ke mulki a jihohin APC suna tsoron jama’a domin ba su tabuka masu komai a ofis ba.

Nyesom Wike
Ministan Abuja, Nyesom Wike wajen taro a Rivers Hoto: Lere Olayinka
Source: Facebook

Kakakin tsagin PDP ya kare Nyesom Wike

Bangaren na PDP ya yi wannan magana ne ganin sabanin da aka samu tsakanin ministan da gwamnonin a cewar jaridar Tribune.

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Na hannun daman Tinubu ya gargadi Wike kan yawan surutu

Sakataren yada labaran tsagin PDP, Hon. Jungudo Haruna Mohammed ya fitar da jawabi yana aika gargadi ga gwamnonin APC.

Jungudo Haruna Mohammed ya ce Nyesom Wike ba wasa ba ne, ba za a yi watsi da shi ba.

Kakakin jam’iyyar yake cewa duk wanda ya raina tasirin tsohon gwamnan na jihar Ribas, zai iya cutar kan shi idan aka shiga zabe.

PDP: 'Ba Wike ba ne matsalar gwamnonin APC'

A jawabin na shi, ya fada wa gwamnonin jam’iyya mai mulki cewa ba Wike ba ne matsalarsu, su ji da rashin kokarinsu kan karaga.

Yake cewa gwamnonin ba su da kwarin guiwar tunkarar masu kada kuri'a a takarar 2027.

"Ba za a yi wa PDP barazana ba ta hakura da takara. Za mu tsaida ‘yan takara masu nagarta, mu jawo ‘yan Najeriya kuma mu kawo wa al’umma zabi na gaskiya a 2027.
"Fargaba ta jawo suke adawa da Wike. Suna tsoron cewa rashin kokarinsu a mulki zai bayyana a filin zabe."

Kara karanta wannan

2027: Sabon rikici ya barke tsakanin Wike da gwamnonin APC

- Jungudo Haruna Mohammed

Ya PDP take ganin doya da manjar Wike?

Daily Trust ta rahoto Jungudo Mohammed ya ce Wike yana da damar goyon bayan Bola Tinubu musamman ganin ya ba shi mukami.

Jam’iyyar ba ta ga wata tafka da warwara a wajen mara wa Tinubu baya alhali Wike yana nan a PDP ba tare da ya sauya-sheka zuwa APC ba.

Tsagin ya ce babu wanda ya isa ya hana Mista Wike da PDP tsaida ‘yan takaran da za su yaki APC a zabukan da ba na shugaban kasa ba.

Idan da gwamnonin na APC sun yi aikin a-zo-a-gani, Jungudo ya ce da ba za su ji tsoron Ministan Abuja ya goyi bayan ‘yan takaransu ba.

A karshe ya bukaci kungiyar gwamnonin jihohin ta maida hankali wajen aiki, ta rabu da ministan.

Nyesom Wike
Nyesom Wike a Ikwere, Rivers ana taron siyasa Hoto: Lere Olayinka
Source: Facebook

An ja layi tsakanin PGF da Nyesom Wike

An ji cewa rikicin da ya fara tsakanin Nyesom Wike da Hope Uzodimma da AbdulRahman AbdulRazaq ya shafi sauran gwamnoni na APC.

Kara karanta wannan

An sake rusa lissafin Tinubu, tsohon shugaban Majalisar dokoki ya fice daga jam'iyyar APC

Kungiyar gwamnonin APC ta yi zama a makon nan, a nan suka dauki matsaya cewa babu ruwansu da wata alaka da Wike da mutanensa.

Gwamnonin suna tsoron cewa biye wa Ministan Abuja yana nufin za a doke 'yan takaran APC a jihohinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng