Atiku Ya Dauki Zafi, Ya Sake Fallasa Abin da Yan Najeriya ba Su Sani ba kan Tallafin Man Fetur

Atiku Ya Dauki Zafi, Ya Sake Fallasa Abin da Yan Najeriya ba Su Sani ba kan Tallafin Man Fetur

  • Dan takarar shugaban kasa na ADC Atiku Sbubakar ya ce babu abin da zai hana shi dawo da tallafin mai da ya yi wa ’yan Najeriya alkawari
  • Ya zargi gwamnatin Tinubu da cewa tana kiran cire tallafin mai gyara tattalin arziki tare da bai wa masu zuba jari a man fetur rangwame
  • Ya nemi gwamnati ta bayyana wadanda suka ci gajiyar rangwamen harajin man fetur da kudaden shiga da aka yi watsi da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce babu sbin da Shugaba Bola Tinubu ko miliyoyin ’yan tawagarsa za su fada d zai za ya janye yunkurinsa na dawo da tallafin mai.

Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, ya zargi gwamnatin Tinubu da kiran cire tallafin mai da sunan gyara tattalin arziki, yayin da take ci gaba da bai wa yan kasuwar fetur rangwamen haraji da wasu fa’idodi.

Kara karanta wannan

Jigo a APC kuma dan kasuwar mai ya kwancewa Atiku zani kan dawo da tallafin fetur

Atiku.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar yayin da ya karbi bakuncin matasan ADC a Abuja Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Vanguard ta rahoto cewa madugun adawar ta Najeriya ya fadi jaka ne a cikin wata sanarwa da Babban Mataimakinsa na Musamman kan Hulda da Jama’a, Phrank Shaibu, ya fitar a Abuja ranar Lahadi.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce ikirarin Tinubu na cewa ya cire tallafin mai yaudara ce kawai, domin yana biyan tallafi amma da sunan rangwamen haraji da sauran abubuwan ƙarfafa gwiwa ga dillalan mai.

Atiku ya kafa hujjarsa ne kan bayanan asusun binciken kuɗaɗen da kamfanin mai na kasa (NNPC) ya fitar, yana mai cewa alkaluman sun saɓa da ikirarin gwamnati na cewa an kawo ƙarshen tallafin mai.

Atiku ya fasa kwai kan bayanan NNPCL

A cewar sanarwar, asusun NNPC na 2023 ya nuna an kashe kusan Naira tiriliyan 4.84 a matsayin kuɗaɗen tsaron makamashi da gibin da ya danganci hakan.

Ya ce a cikin bayanan kashe kuɗaɗe na kamfanin NNPC da aka tantance na 2024 kuma, an samu kusan Naira tiriliyan 7.13 a ƙarƙashin kuɗaɗen tsaron makamashi.

Kara karanta wannan

Atiku ya haska kokarinsu na fito da El Rufai, ya fadi abin da ya hana a kama shi

Ya ce a sauƙaƙe, gwamnati tana ci gaba da biyan wani bangare na farashin fetur yayin da gefe guda Tinubu ya sanar cewa an kawo ƙarshen tallafin mai.

“Ko gwamnati ta kira shi tallafi ko wani abu daban, mun ssn an yi amfani da kuɗaɗen gwamnati wajen cike gibin da ke tsakanin ainihin kuɗin da man ya ci da kuma farashin da ake sayar da shi,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa ba za a iya cewa an soke tallafin mai a bainar jama’a sannan a sake bayyana shi a cikin asusun gwamnati da wani suna daban ba.

Tinubu da Atiku.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da dan takarar ADC a 2027, Alhaji Atiku Abubakar Hoto: @aonanuga1956, Atiku Abubakar
Source: Twitter

Atiku ya bayyana tsarinsa

Atiku ya bayyana shirin nasa mai suna Atiku Economic Recovery Plan a matsayin wanda ya bambanta da tsohon tsarin tallafin mai da ya kira “mai cike da rashin gaskiya da cin hanci da rashawa”.

Ya ce shirins na dawo da tallafin mai zai kasance da iyaka bayyananniya, kasafin kuɗi a fili da sa ido mai zaman kansa, kamar yadda Punch ta rahoto.

Hadimin Atiku ya soki cire tallafin mai

Kun ji cewa mai magana da yawun ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, Kenneth Okonkwo, ya soki cire tallafin man fetur.

Okonkwo ya ce cire tallafin bai kawo sauƙin rayuwa ga 'yan Najeriya ba, yana mai cewa tsadar man fetur, hauhawar farashin kayayyaki da faduwar darajar Naira sun ƙara tsananta wahalhalun jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262