Yakin Zaben 2031 da Abubuwan da Suka Haddasa Rigimar Wike da Gwamnonin APC
- Nyesom Wike yana amfani da gamayyar haɗakar jam’iyyunsa don tallata Bola Tinubu da kuma kare tasirinsa a siyasa
- Su kuma gwamnonin APC na ganin hakan na iya zama zagon ƙasa ga 'yan takararsu da aka tsaida a jihohi a 2027
- Takaddamar ta samo asali ne tun daga rikicin siyasar jihar Rivers tsakanin Wike da magajinsa, Gwamna Simi Fubara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Sabanin siyasan da ke tsakanin Ministan Abuja, Nyesom Wike da gwamnonin APC ya yi kamari a halin da ake ciki.
Nyesom Wike wanda ‘dan jam’iyyar PDP ne a hukumance yana taya Bola Tinubu yaki, amma bai tare da gwamnonin APC.

Source: Facebook
A makon nan, jaridar Leadership ta yi nazarin rigimar da ake yi, kuma ta jero wasu abubuwan da ta ke ganin a kansu ake fada.
Silar rikicin Nyesom Wike da gwamnonin APC
Ga sabuban tata-burzarsu nan kamar haka:
1. Tsohuwar rigimar Fubara-Wike
Wasu gwamnonin APC, ana zargin musamman Hope Uzodinma sun yi kokarin taya takwaransu, Simi Fubara fadansa da Nyesom Wike.
A karshe Ministan Abuja ya yi galaba kuma gwamna Simi Fubara ya rasa damar zarcewa a mulki duk da ya bar PDP zuwa cikin jam'iyyar APC.
Har yanzu Wike bai manta da wannan ba, kuma ba zai so a hana shi kawo wanda zai zama sabon gwamna a jiharsa wato Rivers a 2027 ba.
2. Iko da jam’iyya da kawo magaji
Ana ganin cewa kokarin ganin an karbe iko da jam’iyya yana cikin abubuwan da suka haddasa wannan rigima da ake yi da gwamnonin APC.
Gwamnonin da wa’adinsu ya zo karshe za su dage sai kawo wadanda za su zama gwamnoni a 2027 a karkashin jam’iyyarsu mai mulki.
Mista Wike a wani bangaren yana amfani da ikon shi domin ganin ‘yan takaransa sun kai labari a wasu jihohi, abin da ‘yan APC ba za su so ba.
3. Neman tazarce
Ban da gwamnonin da za su yi sallama da fadar mulki a shekara mai zuwa, akwai wadanda babu abin da suke hange irin ganin sun zarce.
Wadannan gwamnoni suna so a yi APC sak a 2027, shi kuwa Ministan na Abuja yana cigaba da salon siyasarsa ta doya da manja a Najeriya.
Duk da yana goyon bayan shugaban kasa Bola Tinubu, mutanen Wike suna yaki da wasu gwamnonin APC, suna zarginsu da rashin aiki.
4. Yakin neman zaben Tinubu
Tafiyarsu Nyesom Wike ta ‘The Rainbow Coalition’ tana tallata Bola Tinubu a sama, da kuma wasu ‘yan takaran adawa a matakin jihohi.
A lokacin da APC take da kwamitin yakin neman zabe na ‘ya ‘yanta, tsohon gwamnan yana na shi kokarin na dabam a gefe a zaben 2027.
Gwamnonin jam’iyya mai mulki sun fito baro-baro sun barranta daga wannan gamayya duk da tana goyon bayan tikitin Tinubu/Shettima.
5. Dogon lissafin 2031
Fadan ‘yan siyasan ba na 2027 ba ne kawai, rahoton ya ce da alama an fara lissafin 2031, shekarar da za a sake yin babban zabe a kasar.
Shi Wike yana so ya cigaba da zama na-kusa da Shugaban kasa har lokacin da zai yi gama wa’adi na biyu alhali kuma bai rabu da PDP ba.
Ana wannan lissafi ne idan har APC ta lashe zaben badi, ta cigaba da mulki a sama. Wike zai iya katse alakarsa da gwamnati mai-ci a 2031.

Source: Facebook
Wike: PDP ta kula gwamnonin APC
Rahoton nan ya ce Kakakin bangaren PDP karkashin Nyesom Wike ya fadi abin da ya sa gwamnonin APC suka tsorata da Mai girma Ministan Abuja.
Tsagin PDP da ke goyon bayan Nyesom Wike ya gargaɗi gwamnonin APC cewa raina tasirin Nyesom Wike zai iya haifar masu da babbar matsala a 2027.
Kakakin tsagin jam'iyyar ya bayyana cewa tsoron gazawarsu a mulki ke sa gwamnonin APC rashin kwanciyar hankali, yayin da ya wanke Wike daga zargi.
Asali: Legit.ng


