Kwankwaso Ya Yi Magana kan Kwamitin Kamfen din Tinubu, Ya Aika Sako ga Sanata Yari

Kwankwaso Ya Yi Magana kan Kwamitin Kamfen din Tinubu, Ya Aika Sako ga Sanata Yari

  • Rabiu Kwankwaso ya soki tsarin kwamitin yakin neman zaɓen APC na 2027, yana mai tambayar irin abin da jam’iyyar ke son gabatar wa ’yan Najeriya
  • Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC ya buƙaci Abdul’aziz Yari ya sake duba matsayinsa na jagorantar kamfen din Tinubu
  • Kwankwaso ya kuma nuna damuwa kan rawar da manyan jami’an gwamnati ke takawa a tsarin tara kuɗaɗen kamfen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya soki tsarin kwamitin yakin neman zaɓen APC na zaɓen 2027.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kuma buƙaci Abdul’aziz Yari ya sake duba matsayinsa na jagorantar yakin neman zaben Shugaba Tinubu a 2027.

Kwankwaso ya ba Sanata Yari shawara
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Sanata Abdulaziz Yari Hoto: Hon Saifullahi Hassan, Al'mansoor Gusau
Source: Facebook

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi, 23 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya shawarci Yari game da nema wa Tinubu kuri'a a zaben 2027

Madugun na Kwankwasiyya ya tambayi dalilin da ya sa Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma jigo a APC, ya amince ya jagoranci kamfen ɗin sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu.

Kwankwaso ya soki tsarin kamfen din Tinubu

A cewar Kwankwaso, tsarin kwamitin ya nuna cewa jam’iyyar mai mulki tana dogaro da ’yan siyasar da suka goyi bayan gwamnatin yanzu ko kuma suka taɓa kasancewa a cikinta.

Ya ce hakan na haifar da tambayar abin da APC ke shirin gabatar wa masu zaɓe a shekarar 2027.

“Kwamitin ya haɗa da da yawa daga cikin ’yan siyasar da suka goyi bayan gwamnatin yanzu, suka kare ta ko kuma suka shiga cikinta."
“Haɗuwarsu ta haifar da wata muhimmiyar tambaya: me suke son ’yan Najeriya su zaɓa a 2027, sabon farawa ne ko kuma ci gaba da tsarin da ya jefa al’ummarmu cikin tsananin wahala?” in ji shi.

Kwankwaso ya ce zaɓen shugaban ƙasa na 2027 zai bai wa ’yan Najeriya damar yanke shawarar ko za su ci gaba da riƙe da gwamnatin yanzu ko kuma su nemi wata hanya dabam.

Kara karanta wannan

Ba tare da tsoro ba, Kwankwaso ya fadi rukunin mutane 2 da za su gwabza a zaben 2027

Ya lissafa tsadar rayuwa, rashin aikin yi, rashin tsaro da matsin lamba kan ilimi, kiwon lafiya da sauran ayyukan gwamnati a matsayin wasu daga cikin ƙalubalen da ’yan Najeriya ke fuskanta.

Kwankwaso ya nemi Yari ya sake tunani

Tsohon gwamnan na Kano ya yi kira na musamman ga Yari da ya sake duba shawarar da ya yanke ta jagorantar kamfen ɗin Tinubu.

Kwankwaso ya ce kwarewar Yari a matsayin tsohon gwamnan Zamfara ya kamata ta sa ya fahimci matsalolin da ’yan Najeriya ke fuskanta, musamman a yankin Arewa maso Yamma.

“A matsayinsa na tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma fitaccen jagora daga Arewa maso Yamma, na yi amanna cewa Sanata Yari ya fahimci illolin rashin tsaro, talauci, rashin aikin yi, ƙaura da lalacewar hanyoyin samun abin rayuwa a yankin da ma ƙasar baki ɗaya,” in ji shi.

Kwankwaso ya tambayi ko Yari zai ji daɗin jagorantar kamfen ɗin neman wa gwamnatin Tinubu wa’adi na biyu, alhali kuwa yana fuskantar matsalolin da ya ce ’yan Najeriya ke fama da su.

Kwankwaso ya ba Sanata Yari shawara
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na jawabi a wajen taro Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Ya yi magana kan jami’an gwamnati

Kwankwaso ya kuma nuna damuwa kan rahotannin da suka ce an saka Shugaban Hukumar Kula da Haraji ta Najeriya, Zacch Adedeji, da Darakta-Janar na Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya, Tanimu Yakubu Kurfi, cikin tsarin tara kuɗaɗe da harkokin kuɗin kamfen.

Kara karanta wannan

Sanatan da ya fice daga APC ya samu tikitin PDP, zai fafata da gwamna a 2027

A cewarsa, shigar manyan jami’an gwamnati cikin ayyukan kamfen na jam’iyya na haifar da tambayoyi kan tsaka-tsakin hukumomin gwamnati da kuma amincewar jama’a.

Kwankwaso ya yi kira ga 'yan Najeriya

Kwankwaso ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su ƙi abin da ya bayyana a matsayin ci gaba da danniya, tare da zaɓar shugabanci mai riƙon amana da kuma mai fifita bukatun jama’a a 2027.

“Idan mutanen Osun sun iya yin hakan, sauran sassan ƙasar ma za su iya,” in ji shi.

Tinubu zai kayar da Kwankwaso a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan majalisar wakilai, Abdulmumin jibrin, ya nuna kwarin gwiwar cewa Shugaba Bola Tinubu zai kayar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a Kano a zaben 2027.

Dan majalisar ya nuna cewa Tinubu zai kayar da tsohon gwamnan ne saboda ba shi ba ne dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng