Ba Tare da Tsoro Ba, Kwankwaso Ya Fadi Rukunin Mutane 2 da Za su Gwabza a Zaben 2027
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce babban zaɓen 2027 ya wuce fafatawa tsakanin jam’iyyu, ya zama zaɓin makomar Najeriya
- Dan takarar mataimakin shugaban kasar ya yi kira ga ’yan Najeriya su haɗa kai wajen kare ƙuri’unsu da yaƙi da sayen ƙuri’a
- Kungiyar KNN ta yi alƙawarin tattara ƙuri’u miliyan 5 ga tikitin Peter Obi-Kwankwaso a Kudu maso Gabas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi hasashen yadda za a gwabza a zaben 2027.
Kwankwaso ya bayyana zaɓen 2027 a matsayin yaƙi tsakanin rukunin ’yan Najeriya da bangaren da ya kira “masu zalunci."

Source: Facebook
Kwankwaso ya gana da kungiyar KNN
Vanguard ta ruwaito cewa Kwankwaso ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi wata tawaga ta shugabanni da masu ruwa da tsaki daga Kudu maso Gabas na kungiyar Kwankwaso National Network (KNN).

Kara karanta wannan
Minista ya fasa kwai, an ji yadda ake shirin ƙarawa Atiku 'hawan jini' kafin zaben 2027
Tawagar ta kai masa ziyaraa gidansa da ke Abuja ƙarƙashin jagorancin shugaban KNN na shiyyar Kudu maso Gabas, Dakta Ukpai Iro Ukpai.
Ukpai, wanda ya bayyana hakan a wata hira da yan jarida a Umuahia, ya ce tawagar ta ziyarci tsohon gwamnan Kano ne domin yi masa bayani kan ayyukan KNN.
Abin da Kwankwaso ya hango a 2027
A cewar Ukpai, Kwankwaso ya shaida wa tawagar cewa rashin gamsuwa da halin da ƙasar ke ciki ya haifar da ƙaƙƙarfan muradin ’yan Najeriya na ganin an sauya salon tafiyar da mulkin ƙasar.
Ya ce bai kamata a takaita zaɓen 2027 da takarar jam’iyyu kawai ba, sai dai a ɗauke shi a matsayin muhimmiyar dama ta yanke shawarar makomar Najeriya.
Kwankwaso ya yi kira ga ’yan Najeriya da su yi tir da magudin zaɓe da sayar da ƙuri’a, yana mai cewa babu wani abu da mutum zai samu da y fi makomar ƙasar muhimmanci.
A cewar Ukpai, Kwankwaso ya buƙaci shugabannin KNN da su ƙara kaimi wajen wayar da kan jama’a a matakin ƙasa kafin zaɓen, kamar yadda Guardian ta rahoto.

Source: Facebook
KNN ta daukar wa Kwankwaso alkawari
Daga bisani, tawagar Kudu maso Gabas ta yi alƙawarin yin aiki domin samun aƙalla ƙuri’u miliyan biyar ga tikitin Obi-Kwankwaso a faɗin yankin.
Ya ce Kwankwaso ya nuna gamsuwa da yadda ayyukan KNN ke ƙaruwa, yana mai bayyana ƙungiyar a matsayin ɗaya daga cikin ƙungiyoyin goyon baya masu ƙarfi a bayan wannan tafiyar siyasa.
Dalilin hadewar Kwankwaso da Obi
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamna a Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi bayanin abin da ya sa ya yarda su yi aiki tare da dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi a 2027.
A dogon jawabin da ya fitar, Sanata Kwankwaso ya ce Najeriya ta shiga wani hali na wahala da kunci a dalilin tsadar abinci da kuma rashin aikin yi.
Ya ce kawancensa da Peter Obi na da manufar kawo ƙarshen matsalolin tattalin arziki da tsaro da ke addabar jama’a a fadin Najeriya.
Asali: Legit.ng
