Siyasar Arewa: An fara Tono Laifin Yan Majalisar Dokoki 8 da Suka Fice daga Jam'iyyar APC
- Majalisar dokokin Zamfara ta ce ’yan majalisa takwas da suka sanar da ficewa daga APC an dakatar da su tun watan Fabrairun 2024
- Rt. Hon. Bilyaminu Moriki ya ce an dakatar da su ne bisa zargin rashin da’a da karya dokokin majalisar
- Kakakin majalisar ya ce ba a danganta dakatarwar da sauya jam’iyya ba, inda ya tabbatar da cewa majalisar na gudanar da aikinta yadda ya kamata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Gusau, Zamfara – Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Rt. Hon. Bilyaminu Ismail Moriki, ya ce ’yan majalisa takwas da suka sanar da ficewa daga APC an dakatar da su tun ranar 26 ga Fabrairu, 2024.
Moriki ya ce an dakatar da ’yan majalisar ne bisa zargin aikata rashin da’a, hada baki, aikata barna, raina majalisa da kuma gudanar da zaman majalisa ba bisa ka’ida ba, wanda ya saba wa doka.

Source: Facebook
Dalilin dakatar da ’yan majalisa 8
A rahoton Leadershi, Moriki ya ce zarge-zargen da ake yi wa ’yan majalisar sun wuce batun karya dokokin majalisa kawai, inda suka hada da abubuwan da suka shafi kutsen ofis, shiga wuraren aiki da karfi da kuma lalata kadarorin gwamnati.
Ya ce an zargi ’yan majalisar da shiga ofishin magatakardar majalisar da na wani jami'i da karfi, tare da shiga zauren majalisa ba tare da izini ba.
Haka kuma, an zarge su da lalata wasu kadarorin majalisar kafin daga bisani su gudanar da wani zaman majalisa ba tare da izini ba.
Kakakin ya ce girman zarge-zargen ya sa aka shigar da korafin laifi a kan ’yan majalisar da aka dakatar a gaban wata kotu mai hurumin sauraron irin wannan shari’a.
Moriki ya yi martani kan fitarsu daga APC
Da yake magana kan sanarwar ficewar ’yan majalisar daga APC, Moriki ya bayyana matakin a matsayin yunkurin karkatar da hankalin jama’a daga batutuwan ladabtarwa da suka jawo dakatarwar tasu.
Ya ce hakan na iya haifar da kuskuren fahimta cewa majalisar na cikin rudani, inda ya ce:
“Majalisar Dokokin Jihar Zamfara tana cikin kwanciyar hankali, tana aiki kuma tana gudanar da ayyukan da kundin tsarin mulki ya dora mata.
"Ba za a iya gabatar da ficewar ’yan majalisar da aka dakatar a matsayin shaida cewa majalisar na cikin rudani ba,” in ji shi.
Yadda aka tsawaita dakatarwan
Moriki ya kara bayyana cewa a ranar 13 ga Mayu, 2026, majalisar ta amince da tsawaita dakatarwar a wani zaman majalisa saboda batutuwan ladabtarwa da ba a warware su ba da kuma take dokokin majalisar.

Source: Twitter
Ya ce wasu ’yan majalisa biyu da aka dakatar a baya sun nemi gafarar majalisar, daga bisani aka mayar da su kan kujerunsu, kamar yadda Vanguard ta ruwaito
Yan Majalisa 8 sun fice daga APC
Kun ji cewa ’yan Majalisa takwas daga jihar Zamfara sun fice daga APC, suna zargin jam’iyyar da gazawa wajen magance matsalar tsaro.
’Yan majalisar, ciki har da wani jigon da ke goyon bayan tsohon gwamna Abdul’aziz Yari sun ce sun fice saboda rashin tsaro, rashin adalci da sauran matsaloli.
Asali: Legit.ng

