'Dalilin da Ya Sa Tinubu Zai Kayar da Kwankwaso a Kano a Zaben 2027'

'Dalilin da Ya Sa Tinubu Zai Kayar da Kwankwaso a Kano a Zaben 2027'

  • Abdulmumin Jibrin ya ce Shugaba Bola Tinubu zai kayar da Rabiu Kwankwaso a Kano a zaben shugaban kasa na 2027
  • Dan majalisar Kiru/Bebeji ya ce sanin dabarun siyasar Kwankwaso zai bai wa Tinubu da jam'iyyar APC damar yin galaba
  • Jibrin ya amince Kwankwaso na da karfin fada aji a Kano, amma ya ce kasancewarsa dan takarar mataimakin shugaban kasa zai sauya lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Abdulmumin Jibrin, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Kiru/Bebeji a jihar Kano, ya bayyana kwarin gwiwar cewa Shugaba Bola Tinubu zai kayar da Rabiu Kwankwaso a jihar Kano a zaben shugaban kasa na 2027.

Kwankwaso, wanda ya taba zama gwamnan Kano sau biyu, shi ne dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) a zaben 2027.

Kara karanta wannan

2027: Sanatan APC Salihu Mustapha ya yi watsi da jam'iyyar, ya yi murabus

An ce Tinubu zai kayar da Kwankwaso a Kano
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Shugaba Bola Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Jibrin ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 20 ga watan Agustan 2026 yayin wata hira da tashar Channels Tv a shirin Politics Today.

Dan majalisar, wanda a baya ya kasance abokin siyasar Kwankwaso amma yanzu yake cikin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, ya ce sanin tsarin siyasar Kwankwaso zai taimaka musu wajen samun galaba a zaben.

Jibrin ya yarda da karfin Kwankwaso

Da aka tambaye shi ko Shugaba Tinubu zai iya kayar da Kwankwaso a Kano, Jibrin ya ce:

“Zai kayar da shi saboda da yawa daga cikinmu mun san yanayin siyasar, dabarunsa, yadda yake gudanar da harkokinsa, da kungiyar Kwankwasiyya, da karfinsu da rauninsu. Dukkanmu muna nan kuma mun san yadda za mu iya tunkarar wannan yanayi.”

Jibrin ya amince cewa tsohon gwamnan na Kano ba mutum ne da za a raina ba, amma ya ce abin da zai iya bambanta sakamakon zaben shi ne Kwankwaso ba shi ne dan takarar shugaban kasa ba, sai dai mataimakin dan takara.

Kara karanta wannan

Za a fara yakin neman zabe, Tinubu ya aika sako ga 'yan takara da jam'iyyunsu

Meyasa Tinubu zai kayar da Kwankwaso a Kano?

A cewarsa, da Kwankwaso ne dan takarar shugaban kasa, da yanayin zaben shugaban kasa a Kano ya kasance daban.

“Mun san shi sosai, sosai. Mun san dabarunsa. Har yanzu yana da tasiri kuma yana da magoya baya a Kano. Duk wanda ya ce ba shi da magoya baya, ba ya fadin gaskiya. Don haka, za a fafata sosai."
“Zan fada muku wannan, akwai bambanci tsakanin Kwankwaso ya kasance a takardar zabe a matsayin dan takarar shugaban kasa da kuma kasancewarsa a takardar zabe a matsayin mataimakin dan takara. Akwai babban bambanci, abubuwa biyu ne mabanbanta."
“Da Kwankwaso ne dan takarar shugaban kasa, yanayin siyasar Kano zai iya kasancewa daban, amma ba shi ne dan takarar shugaban kasa ba,” in ji Jibrin.
Abdulmumin Jibrin ya yi magana kan Kwankwaso
Abdulmumin Jibrin da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Abdulmumin Jibrin
Source: Twitter

Tinubu ya ba Adeleke shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya karbi bakuncin gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke a fadar Aso Rock Villa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

"Jama'a sun waye": Jigo a APC ya hango abin da zai sanya Tinubu ya fadi a 2027

Shugaba Bola Tinubu ya bukaci Gwamna Ademola Adeleke da kada ya kunyata ko wulakanta abokan hamayyarsa a zaben gwamna da aka kammala a jihar.

Tinubu ya kuma gargadi Adeleke da kada ya tsangwami ko da mutum guda saboda nasarar da ya samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng