Muhimmin Abin da Ya Sa Rabiu Kwankwaso Ya Zabi Yin Aiki da Peter Obi a NDC
- Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa ya ajiye buƙatarsa ta kashin kai a gefe a takarar da suke yi a 2027
- Ya ce kawancensa da Peter Obi na da manufar kawo ƙarshen matsalolin tattalin arziki da tsaro da ke addabar jama’a
- Ana sa rai haɗuwar magoya bayan Kwankwasiyya da ‘yan Obidients za ta haifar da babban ƙarfin hamayya a ƙasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Tsohon gwamna a Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi bayanin abin da ya sa ya yarda su yi aiki tare da Peter Obi a 2027.
Rabiu Musa Kwankwaso shi ne abokin gamin Peter Obi a zaben shugaban kasa mai zuwa a karkashin jam’iyyar adawa ta NDC.

Source: Facebook
Matsalolin da Rabiu Kwankwaso ya hango
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kawo wannan bayani a jawabin fara kamfe da ya fitar a X a ranar Alhamis, 20 ga Agusta 2026.

Kara karanta wannan
Abin da Atiku zai yi don magance rashin tsaro cikin kwana 100 idan ya zama shugaban kasa
A dogon jawabin da ya fitar, Kwankwaso ya ce Najeriya ta shiga wani hali na intaha a dalilin tsadar abinci da kuma rashin aikin yi.
Baya ga haka ‘dan siyasar ya ce ana fama da rashin tsaro da kuma tsadar yin kasuwanci.
Kwankwaso wanda ya taba zama ministan tsaro ya yi maganar yadda matsalar tsaro ta hana a samu abinci, sannan ta shafi makarantu.
Rabiu Kwankwaso ya yi jawabin soma kamfe
Ganin an fara yakin neman zaben shugaban kasa, ya yi kira ga duk ‘yan Najeriya su duba halin da ake ciki da makomar ‘yan gaba.
Ban da matsalar tattalin arziki da tsaro, ya ce gwamnati tana bukatar ta waiayi sha’anin ilmi, kiwon lafiya da abubuwan more rayuwa
Da yake bayanin hada-kai da ya yi da Peter Obi, Madugun yake cewa ba kabilanci, yanki, addini ko ra’ayin kashin kai ya duba ba in ji Punch.
Dalilin hada-kai da Peter Obi
Yake cewa ba burin shiga fadar shugaban kasa yayi la’akari da shi ba, illa kishin Najeriya.
"Wannan ya sa na zabi in yi aiki da Mai girma Peter Obi, a tikitin Obi-Kwankwaso.
"Hadin-kan mu ba saboda yanki, addini, ko burin kashin kai ba ne. Magana ce ta Najeriya."
- Kwankwaso
Tafiyar Obi-Kwankwaso ta maida hankali game da jagorancin da za a sa al’umma a gaba kuma a inganta kafin tattalin arzikin kowa.
'Dan takaran ya ce:
“Mun yi amanna a samu kasar da gwamnati take yi wa mutane aiki, inda ake samun sakayyar aiki tukuru, inda matasa za su samu makomar kwarai daga gidajensu, sannan inda kowane ‘dan kasa yake da damar samun nasara.
Kiran Kwankwaso na karshe ga al'umma
A yanzu hukumar INEC ta bude kofa, an kada gangar siyasa ga masu neman takarra kujerun tarayya.
Kwankwaso ya yi kira ga matasa, mata, ma’aikata, manoma, ‘yan kasuwa da sauran kwararru su fito a shiga kamfe cikin zaman lafiya.
Ya kuma bukaci ‘yan siyasa da magoya baya su guji abin da zai kawo rabuwar kan jama’a tare da neman goyon baya kowa ya zabi NDC.
Tarayyar Kwankwaso da Obi a NDC
Ana da labarin yadda Rabiu Musa Kwankwaso ya fice daga ADC, ya shiga jam'iyyar NDC suka hade tare da Peter Obi da ‘yan Obidients.
Madugun na Kwankwasiyya ya tsaya takara a kan karon kansa a inuwar NNPP lokacin da Obi yake jam’iyyar LP a 2023 idan ba a sha'afa ba.
Wannan karo da ya amince ya tsaya takara a inuwa guda da tsohon gwamnan na Anambra ya jawo maganganu a yankin Arewa.
Asali: Legit.ng

