‘Kiran ’Bola’ da Atiku Ke Yi wa Tinubu na Neman Saka Shakku kan Ingancin Zabensa’

‘Kiran ’Bola’ da Atiku Ke Yi wa Tinubu na Neman Saka Shakku kan Ingancin Zabensa’

  • Tsohon darektan yakin neman zaben Peter Obi, Akin Osuntokun, ya soki Atiku Abubakar kan yadda yake kiran Shugaba Tinubu
  • Osuntokun ya ce Atiku na da damar sukar Tinubu da gwamnatinsa, amma kiransa da sunansa ya saba wa mutuncin ofishin
  • Ya ce masu adawa da Tinubu suna da hanyoyin kundin tsarin mulki na neman sauya gwamnati, ciki har da zabe ko tsige shugaban kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Akin Osuntokun, tsohon kakakin shugaban kasa kuma darektan yakin neman zaben Peter Obi a 2023, ya soki Atiku Abubakar kan kiran Tinubu da “Bola”.

Osuntokun ya ce Atiku Abubakar na da damar sukar Shugaba Bola Tinubu da gwamnatinsa, amma yadda ya kira shugaban kasar ya kasance rashin girmamawa.

An caccaki Atiku kan kiran Tinubu da 'Bola'
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya da Atiku Abubakar. Hoto: Dada Olusegun, Atiku Abubakar.
Source: Twitter

Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa, yana mai cewa doguwar alakar abota tsakaninsa da Atiku ta hana shi sukar tsohon mataimakin shugaban kasar da tsanani, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An buɗe wa Tinubu ƙofar da zai iya raba Atiku da mataimakinsa kafin zaɓen 2027

Osuntokun ya ce:

“Atiku Abubakar na da damar sukar shugaban kasa, ko da kuwa sukar ta yi tsauri. Abin da na ga bai dace ba shi ne yadda ya maimaita kiran sa da ‘Bola’.
“Wannan ba karfafa hujja ba ne; nuna rashin girmamawa ne da ba shi da amfani, wannan ba abin karba ba ne. Da farko dai, cin mutunci ne ga Najeriya, wadda a madadinta yake rike da wannan mukami,.”

Ya ce Tinubu zababben shugaban Najeriya ne kuma yana rike da mukamin da Atiku ya taba neman samu, yana mai cewa masu adawa da shugaban suna da hanyoyin kundin tsarin mulki da dimokuradiyya na neman sauya shi.

Osuntokun ya ce, “Wadanda suke ganin bai cancanci wannan mukami ba suna da hanyoyin halal na neman sauya shi, ta hanyar tsigewa ko kayar da shi a akwatin zabe. Har zuwa lokacin, Tinubu na da damar moriyar gata da ke tattare da mukaminsa.”

Ya bayyana cewa matsayinsa ba kira ba ne na goyon bayan manufofi ko halayen Bola Tinubu, sai dai neman a kiyaye da’a a muhawarar jama’a tare da girmama ofishin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Dan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Faɗi dalilin da Ya Sa Tinubu ke Son Komawa Ƙarfi da Yaji

Ya ce duk wanda ke neman kuri’un ’yan Najeriya domin zama shugaban kasa ya kamata ya nuna girmamawa ga mukamin, musamman idan abokin hamayya ne ke rike da shi.

Osuntokun ya ce:

“Ku yi tunanin tsohon mataimakin shugaban kasa yana kiran shugaban da ke kan mulki ‘Segun’ ko ‘Mohammadu’ a dukkan wani jawabin kasa. Rashin kunya zai fito fili.”

Ya ce zabin kalmomin da Atiku ya yi ya haifar da tambayoyi game da irin hukunci da dabi’ar da zai zo da su fadar shugaban kasa idan aka zabe shi.

Punch ta ruwaito cewa Atiku, wanda ya kasance mataimakin shugaban kasa daga 1999 zuwa 2007, na daga cikin fitattun ’yan adawa da ke kalubalantar jam’iyyar mai mulki gabanin babban zaben 2027.

An sake zama tsakanin jagororin adawa

Mun ba ku labarin cewa kungiyar G100 na kokarin sasanta Atiku Abubakar da Peter Obi kan dan takara guda ke ci gaba.

Atiku da Obi ba su nuna goyon baya ga tsarin dan takara guda ba, amma G100 na son ci gaba da tattaunawa domin hadin kan ‘yan adawa.

G100 ta ce idan babu wanda ya samu nasara a zagaye na farko, tattaunawar za ta taimaka wa jam’iyyun adawa su marawa dan takara guda baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.