2027: Kwankwaso Ya Fara Shirin Kifar da Tinubu, Ya Tura Sako ga 'Yan Najeriya

2027: Kwankwaso Ya Fara Shirin Kifar da Tinubu, Ya Tura Sako ga 'Yan Najeriya

  • Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce Najeriya na fuskantar kalubale masu yawa da suka hada da tsadar rayuwa da rashin tsaro
  • Kwankwaso ya bayyana cewa ya zabi hada kai da Peter Obi domin tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin tikitin Obi-Kwankwaso
  • Ya bukaci 'yan Najeriya su goyi bayan tikitin Obi-Kwankwaso da sauran 'yan takarar jam'iyyar NDC domin kawo sauyi a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira ga 'yan Najeriya su mara wa tikitinsa na hadaka da Peter Obi baya a zaben shugaban kasa na 2027.

Kwankwaso ya ce Najeriya na tsaka da fuskantar manyan kalubale da suka hada da tsadar rayuwa, rashin aikin yi, matsalar tsaro da kuma matsin tattalin arziki da ke addabar 'yan kasa.

Kara karanta wannan

Takarar Obi da Kwankwaso ta gamu da cikas, rikicin shugabanci ya raunana ta

Rabiu Musa Kwankwaso
Sanata Rabiu Kwankwaso a wajen wani taro. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

A cikin sakon da ya fitar a Facebook, Kwankwaso ya bayyana cewa hadakarsa da Peter Obi ba ta da alaka da bambancin yanki, addini ko kuma son rai.

Sakon Kwankwaso kan 2027

Kwankwaso ya ce yana so 'yan Najeriya su yi nazari sosai kan halin da kasar ke ciki da kuma irin kasar da suke son bari ga al'ummomi masu zuwa.

Ya ce hauhawar farashin abinci da sauran kayan masarufi na ci gaba da sanya matsin lamba mai yawa kan iyalai, yayin da miliyoyin matasa ke neman ayyukan yi da damammakin inganta rayuwarsu.

Har ila yau, tsohon gwamnan ya ce rashin tsaro na ci gaba da barazana ga al'ummomi a fadin kasar, inda ya ce iyalai da dama sun rasa 'yan uwansu, gidaje da hanyoyin samun abin dogaro saboda ta'addanci, 'yan bindiga da satar mutane.

Batun hadakar Kwankwaso-Obi

Kwankwaso ya ce saboda irin wadannan kalubale ne ya yanke shawarar hada kai da Peter Obi domin tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin tikitin Obi-Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi wa APC yasa a Kano, manya a jam'iyyar sun rungumi Kwankwasiyya

A cewarsa, manufar hadakar ita ce gina Najeriya inda gwamnati za ta yi aiki domin jama'a, a rika aiki tukuru, sannan matasa su samu damar gina makomarsu a cikin kasar.

Ya kuma ce gwamnatinsu za ta mayar da hankali kan inganta tsaro domin manoma su koma gonakinsu, yara su samu damar zuwa makarantu cikin kwanciyar hankali.

Kwankwaso ya ce bangaren ilimi da lafiya na bukatar zuba jari cikin gaggawa, yayin da ya jaddada bukatar inganta abubuwan more rayuwa, karfafa hukumomi da sauransu.

Rabiu Kwankwaso tare da Peter Obi
Dan takarar shugaban kasar NDC, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso. Hoto: Mr Peter Obi
Source: Facebook

Kira kan zaben 2027

Kwankwaso ya ce zaben 2027 wata babbar dama ce ga 'yan Najeriya su zabi wata sabuwar hanya wajen tafiyar da kasar.

Ya bukaci jama'a su wuce siyasar rarrabuwar kawuna, su mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi rayuwarsu, tare da neman rikon amana, kwarewa da sakamako daga shugabanni.

A karshe, Kwankwaso ya yi kira ga 'yan Najeriya su goyi bayan tikitin Obi-Kwankwaso da sauran 'yan takarar jam'iyyar NDC.

Dan Ganduje ya koma APC

A wani labarin, mun ruwaito cewa babban dan tsohon gwamnan Kano kuma tsohon shugaban jam'iyyar APC Abdullahi Ganduje, Abdulaziz Ganduje ya koma jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

'Ba jira': Kwankwaso ya fadi tanadin NDC wajen nada mukamai idan an zabe ta

Rahotanni sun ce Abdulaziz ya koma APC ne bayan yunkurinsa na neman tikitin takarar kujerar majalisar wakilai a karkashin jam'iyyar NDC bai samu nasara ba.

An karbe shi a hukumance a ofishin jam'iyyar APC da ke mazabarsa ta Ganduje a karamar hukumar Dawakin Tofa, inda ya karbi katin zama mamba na jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng