2027: Minista Ya Dage Yana Yi wa Tinubu Aiki domin APC Ta Yi Nasara a Jihohi 5
- Ministan Ayyuka, Dave Umahi, ya ce Bola Tinubu zai lashe jihohi biyar na kudu maso gabashin Najeriya a zaben 2027
- Tsohon gwamnan ya bukaci al'ummar yankin da su guji siyasar shiyya, inda ya jaddada cewa ana damawa da su a yau
- Ya ce Shugaba Tinubu ya hafa yankin a gwamnatinsa tare da kawo ayyukan ci gaba ban da manyan mukamai da ya ba su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Ministan Ayyuka, David Umahi, ya ce Bola Tinubu zai lashe dukkan jihohi biyar na Kudu maso Gabas a zaben shekarar 2027.
Mai girma ministan ya bayyana haka ne a lokacin da aka buga gangar siyasa, APC ta ke sa ran yin shekaru 16 tana mulkin kasa.

Source: Facebook
David Umahi yana yi wa Tinubu aiki
David Umahi ya bayyana shirin da yake yi ne yayin wata hira da shirin siyasa na Sunday Politics a gidan talabijin Channels.
Ministan ya bukaci al’ummar Kudu maso Gabas da su guji siyasar bangaranci, yana mai cewa hakan ba zai taimaki yankinsu ba.
“Shugaban kasa zai samu kuri’u masu yawa a Kudu maso Gabas.
“Rai na yana gaya mani cewa za mu lashe jihohi biyar din. Ina aiki domin ganin hakan ta faru. Ina yi wa mutanenmu bayani,”
- David Umahi
A hirar, Sanata Umahi ya ce bai kamata al’ummar yankin Kudu maso gabas su rika kallon siyasa ta fuskar yankinsu kadai ba.
David Umahi ya ce:
“Bai kamata mu rika yin siyasar yanki ba. Hakan ba ya taimaka mana. A matsayimmu na yanki, ya kamata mu iya hada kai da sauran sassan kasar nan,”
Ana sane cewa a halin yanzu, jam’iyyar APC ce ke mulkin Imo, Enugu da Ebonyi, yayin da Labour Party (LP) ke mulkin Abia.
Dama kuma tun tuni jam’iyyar APGA ce ta ke mulkin jihar da ta rage wato Anambra.

Kara karanta wannan
Doguwa ya fito da abubuwa 2 da za su ceci APC daga shan kaye a jihar Kano a zaben 2027
‘Gwamnatin Buhari ba ta waiwayi Kudu maso Gabas ba’
Umahi yana zargin cewa gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba ta yi wa yankin Kudu maso Gabas adalci ba.
The Cable ta rahoto shi yana mai cewa ba a bai wa yankin nasu muhimman mukamai a gwamnatin baya yadda ya kamata ba.
“Ba mu samu wani shugaban rundunar tsaro ba. Ba mu samu manyan mukaman minista ba. Don haka, wariyar da ake yi wa yankin ta ci gaba, har ma ta kara tsananta a lokacin,”
Ya ce halin da ake ciki yanzu ya sha bamban, saboda shi kansa an nada shi Ministan Ayyuka, yayin da su ke da wasu manyan mukamai.
Ya ce:
“Amma yanzu labarin ya canza gaba daya. Ni Ministan Ayyuka ne. Ba mu taba samun Ministan Ayyuka daga yankinmu ba.
“Muna da Ministan Harkokin Waje. Muna da Ministan Kimiyya da Masana’antu. Muna matukar farin ciki da mukaman da aka ba mu.”
Ministan ya ce Tinubu na yi Ibo manyan ayyuka
Sai dai Legit Hausa ta fahimci Ogbonnaya Onu, Geoffrey Onyeama da Okechukwu Enelamah sunr ike mukaman nan a lokacin Buhari.
Ya kuma yi magana kan ayyukan more rayuwa, ya ce a lokacin da yake gwamna na shekaru takwas, ba a yi masu wasu tituna da gadoji ba.
Sai dai ya ce gwamnatin Tinubu ta fara aiwatar da wasu manyan ayyukan more rayuwa da mutanen Ibo za su mora a jihohin su biyar.

Source: Facebook
Minista ya kare cire tallafin fetur
A baya aka samu labari cewa Sanata Heineken Lokpobiri ya ce Najeriya ba ta da tiriliyoyin kudin ci gaba da biyan tallafin fetur da aka cire a 2023.
Ministan harkokin mai ya yi gargaɗi cewa ci gaba da tallafin zai maida Najeriya kamar ƙasar Venezuela domin ana cin N18bn a kowace rana.
Sanata Lokpobiri ya soki matsayar 'yan takarar shugaban kasa; Peter Obi da Atiku Abubakar da suke yin alkwarin dawo da shi idan an zabe su.
Asali: Legit.ng

