An Cafke Mutane 5 kan Zargin Lalata Fastocin Tinubu, Abba Kabir a Kano

An Cafke Mutane 5 kan Zargin Lalata Fastocin Tinubu, Abba Kabir a Kano

  • Rundunar ’yan sandan Kano ta kama mutane biyar da ake zargi da lalata alluna da fastocin Shugaba Tinubu da sauran ’yan siyasa
  • Kwamishinan ’yan sandan Kano Ibrahim Adamu Bakori ya ce an kammala bincike, kuma an gurfanar da su a gaban kotu
  • Kamen ya biyo bayan fitowar Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, inda ake zargin wasu daga cikin tawagarsa da lalata fastoci yayin rikicin masarautar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Yan sanda a Kano ta kama mutane biyar da ake zargi da lalata alluna da fastocin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Rundunar ta ce mutanen da aka kama kuma sun lalata allunan Gwamna Abba Kabir Yusuf da sauran ’yan siyasa a jihar.

An cafke matasa kan yada allunan Tinubu, Abba Kabir
Shugaba Bola Tinubu da Abba Kabir Yusuf. Hoto: Bayo Onanuga, Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Kwamishinan ’yan sandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana hakan yayin amsa tambayoyin ’yan jarida kan matakan tsaro da aiwatar da dokar hana hawan dawakai a bainar jama’a, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Matasa sun barke da zanga zanga a Faransa, ana ta kone kone

An cafke matasa a Kano saboda Tinubu

Yan sanda suka ce matasan da ake zargin ne bayan gudanar da bincike kan yaga fastocin shugabannin wanda ya jawo matsala biyo bayan hawan dawakai da jerin gwanon jama’a a jihar.

Bakori ya tabbatar da cewa an gudanar da bincike kan lamarin, har ila yau an gurfanar da matasan da ake yi zargin a gaban kotu, ya kara da cewa rundunar za ta ci gaba da aiki domin tabbatar da bin doka.

Kwamishinan ya ce za a dauki mataki kan duk wanda aka samu da laifin da zai iya barazana ga zaman lafiyar jama’a ko kawo tashin hankali.

Kamen ya biyo bayan fitowar Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, a ranar Lahadi, inda aka samu rahotannin cewa wasu daga cikin mutanen da ke tare da shi sun lalata fastoci.

Yan sanda sun kama matasada ake zargi da lalata allunan Tinubu, Abba a Kano
Kakakin rundunar yan sanda a Kano, Abdullahi Kiyawa. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa.
Source: Facebook

Yadda matasa suka lalata fastocin Tinubu, Abba

Majiyoyi sun ce an lalata fastoci da allunan talla na Shugaba Tinubu, Gwamna Abba Kabir Yusuf da sauran ’yan siyasa, lamarin da ya kara dagula yanayin rikicin masarautar Kano.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun yi barazanar cafke Sarki Sanusi II da Aminu Ado Bayero a Kano

Ya ce:

“Muna gargadin cewa daga yanzu, idan aka kama wanda ya karya wannan doka za a gurfanar da shi a gaban kotu. Ba za a daga wa kowa kafa ba."

Lamarin cafke mutanen da aka yi ya kasance daya daga cikin matakan farko da aka bayyana a bainar jama’a na aiwatar da doka, dangane da rahotannin lalata kayayyakin yakin neman zaɓe na siyasa.

Wannan gargadin ya kuma sake jaddada muhimmancin samun izinin tsaro tun kafin gudanar da hawan doki a bainar jama’a, yayin da hukumomi ke kokarin hana sake barkewar rikici, cewar Punch.

Tinubu Must Go: Yan sanda sun cafke matasa

A wani labarin an ji cewa ’yan sandan Borno ta kama mutane biyar inda ta ce an gurfanar da a gaban kotu bayan zargin sun saka rigar “Tinubu Must Go”.

Mutanen sun musanta aikata laifuffukan da ake zarginsu da su, yayin da kotu ta ɗage sauraron batun belinsu zuwa ranar 6 ga Oktoba 2026.

Amnesty International ta soki tuhumar, tana mai cewa bayyana ra’ayin siyasa cikin lumana ta hanyar sanya tufafi na cikin ’yancin ɗan Adam.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.